Wannan littafi mai suna TAJWEEDIN
RIWAYATI QALUN fassara ne na littafin (SHARHI RISALATI QALUN) wanda Shehin
Malami Aliyu Muhamad Ad-Dhiba’i mutumin Misra ya rubuta, shi ma kuma sharhi ne
ya yi a kan baitocin da Shehin Malami Muhammad Sa’udi ya tsara a bisa
hukunce-hukuncen tajweed da Imamu Abu Musa Isah, wanda aka yi wa laqabi da
Qalun, wanda shi Shehu ALiyud Dhiba’i ya yi sharhin sa da Larabci, shi kuma
Malam Muhammadus-Su’udiy ya tsamo hukunce-hukunce ne daga littafin Shaxibiy.
Kamar yadda daga kowa ya sani ne,
riwayar Warshe da Hafsu sun rigaya sun bazu ko ina a birni da qauye a qasar
nan, savanin riwayati Qalun wanda ba kowa bane ma ya san da ita ba, don haka
nag a ya dace a bisa xan abin da Allah yah ore min in fassara littafin (SHARHI
RISALATI QALUN) da harshen Hausa tare da yin bayani dalla-dalla da fitar da
hukunce-hukuncen da aka qudundune a ciki a fili don burin samun ci gaba da
qaruwa a cikin tajweedin Al-Qur’ani tare da bunqasa karatun Al-Qur’ani a qasar
nan.
Babu shakka babba da yaro, namiji da
mace za su fa’idantu da wannan littafi. Ina fatan Allah ya sa albarka a
cikinsa, Allah ya ba shi karvuwa kuma ya albarikaci qasar nan da makarantun
Al-Qur’ani da riwayati Qalun da sanadinsa wannan littafi nawa kamar yadda ya
azurta qasar nan da makaranta AL-Qur’ani da riwayati Hafsu da Warshu.
Na gode,
‘YAR’UWARKU
NAFISATU YUSUF
ABDULLAHI BICHI
MRS. DAYYIB
SHEIKH DAN-ALMAJIRI
RIJIYAR LEMO,
LAYIN XAIBA
KANO STATE
No comments:
Post a Comment