NA CAJE SHI, YA CAJE NI!
Kabiru Yusuf Fagge
Karfe tara da wasu 'yan mintuna ne na
dare a lokacin, muna zaune ni da abokina Hassan muna hira, mutane suna ta
wucewa ta gabanmu da motoci, a cikin motocin, wata motar 'yansanda ta zo, ta
gifta mu, tana tafiya a hankali, har sun yi nisa kadan daga inda muke, sai
kuma, muka ga sun dawo da ribas a hankali, har suka zo daf da mu, sannan suka
tsaya, 'yansanda biyu daga cikin hudun da ke bayan motar, suka diro, suka iso
inda muke.
Ko gezau ba mu yi ba, don mun san mu ba
masu laifi ba ne.
"Me kuke yi a nan?" Daya daga
cikinsu, mai rike da zungureriyar bindinga ya tambaye mu.
Sai da muka dubi juna ni da Hassan kana muka
sake kallon su, kamar hadin baki, muka amsa a tare.
"Ba komai, hira kawai muke
yi."
Su ma suka kalli junansu, wanda ya yi maganar
da farko, shi ya kara cewa, "Shira da tsakar daren nan? Gaskiya ba mu
yarda da ku ba."
Na duba wayata, na ga karfe tara da
minti tara, ina shirin yin magana ya riga ni da cewa.
"Sajan sas hyem (search
them), caje min su, da alama wani bakin ciniki suke a daren nan, ka san
yanzu an samu karuwar diloli da kuma 'yan kwaya gami da dabarun siyar da kwayoyin,
sai ka ga samari sun yi shigar mutanen kirki amma hyegu (shegu) ahye (ashe) dilolin
miyagun kwayoyi ne. Caje min su, from uf to dawun (from up to down...)"
A gurguje a irin nazarina na marubuci na
fahimci yallaban yana da matsalar furta SHA, da alama irin su ne masu cewa 'HYAYI'
a maimakon 'SHAYI' ko 'HYA' madadin 'SHA', 'HYUWA' a maimakon 'SURE' ta
Turanci.
Kafin na gama nazarina, Sajan din wanda
na ga sunansa a gaban aljihunsa Audu Maina ya gama caje Hassan ciki da bai, duk
ya fito da kudinsa da wayarsa da katin shaidarsa ya zuba a hula, sannan ya juyo
gare ni. Yana shirin fara caje ni, na yi sauri na tsayar da shi, "Yallabai
saurara!"
Abin ya ba su mamaki, ya saurara din
kuwa, yana kallona. Ni ko na ci gaba da fadin, "Kafin ka caje ni, bari in
fara caje ka, don haka na ji hukumar 'yansanda ta sanar, ta ce kafin kowanne dansanda
ya caje ka. Ka fara caje shi, saboda tsaro."
Suka kara yin mamaki suna kallon juna,
kawai sai na ga Sajan Audu din ya daga hannu sama, yana fadin.
"Caje ni yaro, ka zo da zance, yi
sauri."
Ban yi wata-wata ba, na fara caje shi,
tun daga aljifan gaban riga, har na bayan wando da na gaban wando sai da na
caje.
Wasu dukunkunannun kudade na tarar a
aljifan bayan wandon, 'yan naira ashirin-ashirin da hamsin da goma-goma da
alamun na cin hanci ne, duk na yo waje da su.
Lokacin da na fito da kudin na lura sun
yi wa juna kallo-kallo shi da mai bindiga, da alamun dayan bai ma san ya boye
wadannan kudaden ba. Ni dai na kammala caje shi na mayar masa da cukurkudaddun
kudadensa aljihu, na ce.
"Na gama." A lokaci guda ina
daga hannu sama, ina fadin, "Bismilla, caje ni."
Sajan Audu Manu ya girgiza kai ya ce,
"No! yaro sauke hannunka, ba a nan zan caje ka ba, sai mun je ofis."
Ya rarumi kuguna yana ci gaba da cewa, "Mu je, ka hau mota." Ya fara
ja na.
Daya dansandan ya dubi Hassan ya ce,
"Kai kuma dauki tarkacenka, ka wuce gida, mun gama da kai."
Ina ji, ina gani suka sa ni a mota muka
tafi, Hassan tsaye yana kallona.
A cajis ofis, suka ajiye ni a bayan
kanta, sai da suka gama abubuwan da ke gabansu, tare da kus-kus na tsawon
lokaci, Audu yana fadar maganganun da ba na ji, insfektan yana rubutawa, sannan
suka juyo gare ni, su hudu.
Insfektan sunansa Habu Ringim, yana da
jajayen idanu, fuskarsa babu alamun wasa a tare da ita, shi ya kura min idanu,
ya fara magana.
"Kai ne ka yi wannan aika-aikar, ka
zura hannu a aljihun hukuma?"
Na dube shi cikin mamaki, "Kamar ya
ya?"
"Kamar yadda na fada maka!" Ya
furta cikin tsawa.
Na girgiza kai, "Ko kadan, ni dai
na san na caje shi kawai."
"Ka sa hannu a aljifansa ko?"
Ya tambaye ni.
"Kwarai kuwa, na caje shi mana."
Na gyada masa kai.
"Madalla, abin da nake son ji a ke nan,
ka amsa laifinka na farko." Na bi shi da kallo kawai, ya fara rubutu a takardar
da ke hannunsa, sannan ya sake kallona, "Da farko, ka yi wa Sajan Audu
sane, ka sa hannu a aljihunsa, ka sace masa kudin albashinsa har Naira dubu
sittin da uku, da kuma karamar bindigarsa ta aiki hadi da katin shaidarsa."
Ji na yi kamar yana karanta min tatsuniya,
hakan ya sa na bi shi da kallo kawai cike da tsantsar mamaki.
"Ka kura min idanu, ko kai maye ne
in hada maka da cajin maita?"
Girgiza kai kawai na yi. Ya ci gaba da
cewa, "Yanzu muna so ka gaya mana sauran abokan aikin naka, kai ne ogan ko
a karkashin wani kake?"
"Yallabai kana maganar abin da ba
haka yake ba fa, ban san abin da kake nufi ba." Na furta da kyar.
Ya daka min tsawa, tare da yin kamar zai
mare ni, na shiga taitayi na, sannan ya ce "Za ka sani ne, idan ka fara fuskantar
tuhuma tare da mika ka wajen alkali."
Ya juya, ya yi banza da ni. Na rasa me
zan yi, lallai da alama na shigo inda ban san hanyar fita ba, lokacin da na
fara tunani, a lokacin ya juyo gare ni, yana mai sassauta murya.
"Yaro wannan laifin naka gagarumin
laifi ne, wanda zai iya kai ka da hukuncin kisa, domin za ka shiga sahun 'yan
fashi ne da suka far wa jami'an tsaro suka samu nasarar kwace musu bindiga da
kudadensu, don haka bari in yi maka wata alfarma."
Kallonsa kawai nake, na kasa yin magana.
"Ko ba ka son alfarmar tawa?"
"Ina sauraronka." Na ce da
shi.
"Yawwa, zan ba ka dama ka kira
wanda ko wadanda za su yi belinka, su biya kudin albashinsa da bindiga, kar a
je kotu ba za ka taba fita ba."
Babu yadda za a yi mamaki ya rabu da ni,
na yi ajiyar zuciya na dauko wayata, sannan na kalle shi na ce, "Ina son
ka ba ni lambar wayar IG, shugaban 'yansanda na kasa."
"Me za ka yi masa?"
"Zan bayyana masa halin da ake
ciki, in gaya masa ya ba mu dama, damar tana neman zama matsala."
Ya kyalkyale da dariya.
"Fara sawa, zan gaya maka
lambar." Ya karanto min lambar, na saka a wayata, na fara kira, tana shiga
ba a dauka ba.
A takaice na yi kira kusan sau dari biyu
amma ba a dauka ba, sannan kuma na tura sako ya fi sau shurin masaki, shi ma ba
amsa, sai a lokacin zazzafan gumi ya keto min, na fara tambayar kaina, ya zan
yi ke nan? Zan biya kudin da aka kaga min, ko zan hakura in tafi a matsayin dan
fashi?
KU TAIMAKA MIN DA AMSA...
Lallai ka shiga cakwakiya.
ReplyDeleteHahah
Delete