Thursday, January 16, 2020

MURUCIN KAN DUTSE.... Tsakure



MURUCIN KAN DUTSE...
(Tsakure daga littafin Murucin Kan Dutse, inda Sanusi ke karanta wani sashe na littafin da mahaifinsa ke rubutawa)

Ahmadu ya yi imanin dan adam ba zai ketare abin da Allah ya rubuto masa ba. Watakila da ya so, da ya gudu lokacin da Akintola ya zo masa da tayin haka. Sannan ‘yan kawanki kadan kafin zuwan Akintola, ai yana Ummara a kasar Saudiyya. Yana can aka kira aka sanar da shi babu lafiya, akwai rade-raden wasu na shirya juyin mulki a kasar, wannan labari bai hana shi kamo hanyar gida ba. A lokacin da ya dawo gida, wani bature D.J Muffet ya zo gida ya same shi, inda a cikin tattaunwarsu yake fada masa ba ya jin zai kai sallah, ma’ana sallah karama. Sannan a daren ranar juma’a ya kira Sarkin Kano Ado Bayero a waya yake sanar da shi labarin juyin mulkin da ake shiryawa, wanda shi ne maganarsu ta karshe.


Wata makarkashiyar da ta fito fili wanda sai daga baya aka fahimce ta ita ce yadda tun asali aka janye sojojin da suke gadin gidan Firimiyan, sannan aka musanyasu da ‘yan sanda bisa wani dalili da har yau ba a gamsu da shi ba. A wannan rana da Sardauna ya ga Nzeogwu na kai koma, a wannan daren ya jagoranci sojoji suka isa gidan gwamnati inda Sardauna yake tare da iyalinsa. Anan suka bude wuta a bakin babbar kofar shiga gidan, duk da cewa kwarewar ‘yan sanda dake a bakin babbar kofar ba ta kai ta su ba a matsayin sojoji, hakan kuma bai sa sun tsorata ba. Nan take suka mayar da martani. Nan aka dinga musayar wuta har aka kashe wasu ‘yan sanda.
Chukuma Nzeogwu wanda ba shi da tabbas ta ko zai iya samun shiga cikin gidan cikin sauki ta wannan kofa saboda rike masa wuta da suka yi, sai ya yi kokarin sauya tsari, inda ya zagaya ta bayan gida ya yanka wayar da aka zagaye gidan. Ta nan suka samu shiga gidan Sardauna, amma kuma sai suke neme shi suka rasa. A dakin Sardauna da ya shiga, Nzeogwu ya yi kokarin zazzagar da harsasansa gami da harbin kankaren dake saman dakin, yadda kasan ya tari bataliyar sojoji dubu. Nan take ya samu rauni sosai sanadiyar kankaren dakin da ya zubo masa. Ba su samu Sardauna a nan ba sai a bangaren da iyalinsa suke a inda suka tarwatsa duk iyalinsa, amma uwargidansa Hafsa ta ce ba inda za ta je ta bar mijinta. An ce ta cika da mamaki ganin cewa Nzeogwu ne ya ja tawagar sojojin, musamman kasancewarsa dan gida wanda Sardauna ya yi wa riga da wando. Nan take ta fara zaginsa da tofin Allah wadai da halinsa da kare ba zai yi ba. Wanda suke tare da Nzeogwu sun sanar da cewa ya bude wuta ga Sardaunar, amma bindigar ba ta tashi ba a kansa ba. A lokacin ya juya kan Hafsat ya harbe ta a kubi, ganin haka ne shi Ahmadun ya cire hular da take kansa. A wannan lokaci Nzeogwu yasa bindiga ya harbe shi a kansa. Ina amana da amincin zaman tare, mene ne dalilin rashin mutunci ya wuce kan shi Sardaunan ya fada har kan matarsa wadda ba ‘yar siyasa ko ma’aikaciyar gwamnati ba. Ko makiya Sardaunan za su ce abin da ta yi na kare mijinta bai kamata ba?
A kokarinsa na cimma burinsa dana kabilarsa, Nzeogwu tare da tawagarsa suka wuce gidan ogansa a soja Birgediya Samuel Ademulegun, shi ma suka kashe shi tare da iyalinsa. Kisa na rashin mutumci da imani, domin bai ankara ba sai ganin daya daga cikin yaransa a soja Timothy Onwuatuegwu a dakin barcinsu. Timothy da Nzeogwu gidan Ademulegun ba bakon zuwansu ba ne, domin idan suna sha’awar cin sakwara da farfesun kafar sa can suke zuwa su sa matarsa Latifat a gaba. Ademulegun ya yi mamakin ganinsu duk da dinbin tsaron dake gidan. Cikin karaji ya ce. “Timothy, ta ya ya ka shigo nan, kuma wane iskanci kake kokarin yi?”
Abin da ya mayar masa shi ne an bashi umarni ya kamo shi. A tsawon shekaru da Ademulegun ya kwashe a wannan kujera, irin wannan umarni sai dai shi ya bayar. Abin tambayar a nan wane ne ya bada wannan umarnin? Hakan yana nufin cewa wanda ya bada umarnin yana waje, domin sun fita da shi waje ne, watakila inda jagoran yakin yake. Nan suka sa shi gaba zuwa waje. Ba anan rashin imanin nasu ya kare ba, kafin su fita da shi waje sai Timothy yasa bindiga ya dauke Latifat wanda ke dauke da ciki. Ina amana a cikin wadannan sojoji, ko dama haka tsarin sojoji yake na rashin amana da Imani? Ai koda wadannan sojoji basa zuwa cin abinci gurin Latifat a matsayinta na mace bai kamata su kashe ta. Ko suna ganin don ita ma’aikaciyar jinya ce a asibitin sojoji? Amma ita Hafsa Bello da suka kashe mai ya hada ta da aikin gwamnati? Kowa ya san cewa akwai abota da amana tsakanin Ademulegun da Ahmadu Bello, don haka ake ganin dole su kawar da shi idan suna son komai ya tafiyar musu daidai.
Latifat na cikin karajin mutuwa yayin da ‘yarta ‘yar shekara shida da ba ta jin dadi ta zo dakin iyayenta taya su kwana ko ta samu kulawarsu, ta rikice domin a kan idonta abin ya faru, hakan yasa ta dinga rafsa kuka. Qarar bindigu da suke rugugi da kai komo na sojoji ya hana sauran ‘ya’yan tare da ‘yan aiki fitowa daga dakuanan da suke kwance. Latifat na cikin kakarin mutuwa ne sojojin suka dawo da mijinta dakin suka yasar da shi a mace. Cikin jini da jan jiki Latifat ta matso kan mijinta tana kuka, yayin da jini ke tsiyaya a jikinta har ita ma ta rai ya yi halinsa.
Shi ma mataimakin Birgediya Samuel Ademulegun, wato Kanal Ralph Shodeinde a daren suka nufi gidansa. Koda aka kwankwasa masa bai yarda ya fito ba, sai ya leko ta taga. Anan suka sanar da shi abin da suka aikata na kashe Sardauna sannna suka bukaci su ji ko yana tare da su. Nan take ya nuna rashin amincewarsa da wannan danyen aiki, ko matsawa bai yi daga bakin tagar ba aka ce suka jefa masa gurneti, wanda ya tashi da shi ya kuma yi sanadiyar mutuwarsa. Matarsa da take da danyen jego ta samu raunuka. A wannan lokaci ta fita don zuwa gidan Ademulegun ta kai kuka abin da wasu sojoji suka aikata. Ba ta san ba shima ya gamu da ajalinsa a hannun wadannan ‘yan ta’adda ba.
©Zaharaddeen Ibrahim Kallah

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...