Wednesday, January 8, 2020

TARIHIN MARUBUTAN HAUSA


TARIHIN MARUBUTAN HAUSA
Muna farincikin sanar da marubuta cewar mun fara tattara tarihan marubuta don samar da littafi guda da ba a taba yin irinsa ba.


Tsarin littafin:

(1) Tarihin ya hadar da na tsoffin marubuta tun daga Abubakar Imam har zuwa sabbin marubutanmu na yanzu (musamman online writers)

(2) Ma'ana marubutan da suka taba buga littafi ko littattafai da wa
ɗanda suke rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a yanar gizo ko jaridu da mujallu ko gidajen rediyo, ko rubutaccen wasan kwaikwayo

-YADDA TARIHIN ZAI KASANCE:
(a) Suna

(b) Ta
ƙaitaccen tarihi a rubutu (ko rubuce-rubuce)

(c) Jerin littattafan da marubuci/marubuciya ya buga ko ya wallafa (a yanar gizo ko jaridu)

(3) Za a turo tarihin a DOCUMENT ta adireshin da muka bayar a
ƙasa

(4) Idan aka turo sau
ɗaya kawai ya isa

(5) Wasu tarihan za mu tattara su da takarda ko rikodin

(6) In sha Allahu za mu kammala tattarawa nan da wata 6,
ƙarshen watan Yuni ke nan.

(7) Ba ma maraba da marubutan batsa ko sukar wani addini ko a
ƙida.

(8) Za a turo da hoto

Mun gode. Domin
ƙarin bayani za a iya tuntubar (07030319787 ko 08065270511) kafin turo tarihin.

-GA ADIRESAN DA ZA A TURO tarihin:
Imel: ankakabir@gmail.com ko ibmuhd2000@gmail.com
WhatsApp: 07030319787 ko 08065270511


Misalin Tarihin a Ta
ƙaice

UMMA ADAMU
An haifi Umma Adamu ranar 15th ga Oktoba 1981 a Gwarzo, duk da cewa ita 'yar asalin Hadejia ce. Ta yi karatun Firamare a Kanti Primary School Kazaure daga 1987-2003. Ta kuma yi karatun

Sakandare a Malam Madori da Sakandaren Kimiyya ta Taura inda ta gama a 1999. Ta ci gaba da karatu daga 2000 a School of Health Technology Jahun da Informatics Institute Kazaure da kuma Jigawa State College of Education har zuwa 2006. A halin yanzu (2009) tana karatu ne a Kano State University of Science and Technology Wudil. Cikin litattafan da ta buga sun hada da:
1. Raino,
2. Rigakafi
3. Sirrinusu ko Sirrimu
4. Wahayi
5. Zaman Jira
6. Ya Zalince ni
7. Sabanin Ra'ayi
8. Abu a Duhu.
Tana sha'awar koyarwa da kallon fina-finai da tafiye-tafiye da koyarwa da kuma rubuta kirkirarrun labaru.
(mun ciro wannan tarihi daga http://marubutanhausa.blogspot.com/)



No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...