Tuesday, January 7, 2020

RUBUTUNKA TUNANINKA: MARUBUCI MAI TSARA JADAWALIN RUBUTU



RUBUTUNKA TUNANINKA
Mataki na 2:    MARUBUCI YA SAN SHI MAI TSARA JADAWALIN RUBUTU NE KAFIN YA FARA, KO MAI DURFAFAR YIN RUBUTU BA TARE DA TSARAWA BA?

Idan kai marubuci ne mai tsara jadawalin yadda rubutu zai kama ne, za ka tsara dukkan rubutun kafin ka fara rubutawa. Za ka san taurarin labarinka sannan ka san me zai faru a labarin daga farko har zuwa karshe.
Amma idan kai marubuci ne mai yin rubutu ba tare da ka tsara shi ba, daga samun tunanin rubutu za ka fara, kana tafe wasu abubuwa suna fadowa rubutun kana rubuta su, to.
-Wasu masana a rubutu kan ce, ka sanya taurarin da ake so a mawuyacin hali na sa marubuci ya sami tunanin labarin abubuwan da ka iya faruwa a labari.
Idan muka lura da wannan magana ta sama, kowacce hanya takan iya samar da labari mai dadi, ya danganta da yadda marubuci zai iya jan zaren labarinsa cikin gamsuwa.
Marubuta masu yawo, wadanda kan yi rubutu ba tare da tsara yadda rubutun kan kasance ba, ba sa fara yin rubutun ba tare da sanin inda suka dosa ba.

Mataki na 3: KIRKIRAR BABBAN TAURARON DA BA ZA A MANTA DA SHI BA
Kafin marubuci ya fara rubutu, yana da kyau ya fahimci taurarin labarinsa. Sau tari ina yin magana akan muhimmancin tauraro ko taurari a labari, to ya kamata marubuci ya sani, taurari su ne kashin bayan labari, su ne na farko a mafi muhimmanci a labari.
Babban tauraro a labarinka shi ne mafi muhimmanci (tauraro ko jarumi ko gwarzo), sannan shi ne ragamar taurarin labarinka.
Wannan babban tauraro ya zama, ya sha bamban da sauran, ya zama na musamman, kuma wanda ya fi a karshe.
Sannan ya zama yana da duk wata dacewa da zai kai labarinka kololuwa.
Ya zama yana da wani kuskure (ko nakasu) da ya dace da labarin wanda da mai karatu zai rinka ganin kamar ba zai cimma burinsa ba, amma a karshe sai ya cimma.
A bangare guda a taurarin kana da tauraro wanda shi ne mugu (mai kawo tarnaki ga tauraron labari) wanda yake da ban tsoro.
Amma kar ka sanya mugun tauraron ya zama mugu kawai don yana mugu, ka kirkirar masa wani ko wasu dalilai da suka mayar da shi mugun.

Ina kara jaddadawa, kamar yadda na fada a baya, ya kasance tauraronka yana da wani gazawa, amma ta dan wani lokaci.
Sannan kana bukatar taurarin da za su dace da labarin.
Kuma kowanne tauraro ka iya tambayar kanka:-
-Me suke so?
-Me ko kuma wane ne yake hana su samun abin da suke son?
-Me za su yi?
-Mene ne rawar da za su taka a labarin?
-Ka yi amfani da suna na musamman ko na daban ga taurarin labarinka - sunan da zai dace da su, wanda ba zai rikita mai karatunka ba.
-Ka takaita gabatar (introduction) da taurari, ko kuma a shafuka na kurkusa. Sannan kar ka yawaita gabatar da taurari, bayan gabatarwar da ka yi musu a baya.
-Domin saurin tunawa, ko rashin mantawa, ka yi kokari taurarinka su zama karbabbu a wajen masu karatu. Ka ba su 'yan-adamtaka ta daban. Idan taurarinka ba su zama haka ba, to tuni labarinka zai bata a rubibi.
A rayuwa ta zahiri, tauraronka yana fuskantar bayyanannun matsaloli, a lokaci guda yana da wasu matsaloli na boye da ba a sani ba.
-Ka san hoton duk karfi, gazawa, rashin tsaro na taurarinka kafin ka fara rubutu, ta haka rubutunka zai zamo mai sauki.

KA'IDOJIN RUBUTU
*rabe-rabenku* ba *rabe-raben ku* ba
*rike wa Ali* ba *rikewa Ali* ba
*rikewa suke* ba *rike wa suke* ba
*rigar Manu* ba *rigam Manu* ba
*rigarsa* ba *rigassa* ba
*riguna* ba *rigunoni* ba
*rubuta wa Malam* ba *rubutawa Malam* ba
*rubutawa yake* ba *rubuta wa yake* ba
*rubutunka* ba *rubutun ka* ba
*ruda-kuyangi* ba *ruda kuyangi* ba
*rufa-ido* ba *rufa ido* ba
*rugum* ba *rugun* ba
*rumfuna* ba *runfunoni* ba

*sa ka* ba *saka* ba
*sa ku* ba *saku* ba
*sa mu* ba *samu* ba
*sa ni* ba *sani* ba
*sa shi* ba *sashi* ba
*sa su* ba *sasu* ba
*sa ta* ba *sata* ba
*sabi-zarce* ba *sabi zarce* ba
*saboda* ba *sabo da* ba
*sai da* ba *saida* ba
*sai fa* ba *saifa* ba
*sai ko* ba *saiko* ba
*sanduna* ba *sandunoni* ba
*sarkinmu* ba *sarkimmu* ba
*share wa gida* ba *sharewa gida* ba
*shassharbe* ba *shashsharbe* ba
*shi da* ba *shida* ba
*shi dai* ba *shidai* ba
*shi fa* ba *shifa* ba
*shi ko* ba *shiko* ba
*shi ma* ba *shima* ba
*shi ne* ba *shine* ba
*sifa* ba *siffa* ba
*so ki* ba *soki* ba
*so mu* ba *somu* ba
*so ta* ba *sota* ba
*so ni* ba *soni* ba
*son sa* ba *sonsa* ba
*son ta* ba *sonta* ba
*su ga* ba *suga* ba
*su ko* ba *suko* ba
*su ma* ba *suma* ba
*su ne* ba *sune* ba
*sukan* ba *su kan* ba
*suke* ba *su ke* ba
*sukutum* ba *sukutun* ba
*sun sa* ba *sunsa* ba
*sun ki* ba *sunki* ba
*sun so* ba *sunso* ba
*sun yi* ba *sunyi* ba
*sun ce* ba *sunce* ba
*sun ga* ba *sunga* ba

Kabiru Yusuf Fagge

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...