Monday, January 13, 2020

Gajeren Labari: BUHARI YA ZAGA




BUHARI YA ZAGA
Kabiru Yusuf Fagge

Tun da na samu sahalewar hukuma a kan bincike ya sa, duk lokacin da na samu dama nakan leka ofishin 'yansanda na kusa da mu, na zauna a bayan kanta ina ganin abubuwan da ke faruwa na tsakanin jami'an tsaro ('yansanda) da masu kawo kara ko masu laifi.
Ba tonon asiri ba, gaskiya ana tafka magun-magun da kacabe-kacabe, kiri-kiri ga shi an rubuta baro-baro BELI KYAUTA NE da Turanci da Yoruba da Ibo har da uwa-uba Hausa, amma duk wanda zai zo karbar dan'uwansa tsakanin mai gaskiya da mara gaskiya sai ya biya kudi.
Da abin ya ishe ni, sai na matsa kusa da ofisan da ke kula da ni, kuma ka sahalewa ya rinka amsa min duk tambayoyin da na yi, na ce masa.
"Yallabai ga shi an rubuta beli kyauta ne amma na ga duk wanda ya zo sai ya biya." Na kammala fadi ina nuna masa inda rubutun yake.
Ofisa Bello ya ce, "Wannan kudin da ka ga suna bayarwa ba beli ba ne, alheri ne, saboda irin kulawa da sasanta 'yan'uwansu da aka yi...."
"To amma yallabai..."
Na yi kokarin katse shi, amma shi ma sai ya katse ni da cewa, "Wai kai Kabiru cewa aka yi komai ka gani sai ka tambaya?" Ya dan rage murya, yana kallon wasu manyansa da ke gefe, "Ya kamata ka sani, a Nijeriya ba komai ake yin bayaninsa dalla-dalla ba, kuma ba komai ake yin tambaya a kansa ba...Shin ko ka san har yanzu ba a gama yin cikakken bayanin me kundin tsarin mulkin Nijeriya ke dauke da shi ba, duk da tarin tambayoyin da ake yi a kansa?" Ya tambaye ni, bai jira na amsa ba, ya ci gaba, "To ka takaita yin tambayoyi kar ka tambayo abin da ba a tambaya. Ina fatan ka fahimta."
Na girgiza kai, "Gaskiya ban fahimce ka ba."
Ya harare ni, "To wannan ita ce amsar ka, don kuwa ba za ka taba fahimta din ba, kamar yadda duk 'yan Nijeriya ba sa fahimta duk da irin tarin abubuwan tambayoyin da suke da su, kuma suke yi."
Muka yi shiru na dan lokaci, musamman don kar na matsa masa, ya sallame ni a wannan ranar kamar yadda muka saba.
A gefen mu, Ofisa Ashakunu ne tsaye, sai harara ta yake yi cikin bacin rai, duk da tun da nake zuwa wannan dibishin din ba ma wani dasawa da shi amma ban taba ganin shi cikin bacin rai irin na yau ba. Na kalli Ofisa Bello na ce, "Yallabai, zan iya yin wata tambayar?"
"Yi mana, zan hana ka ne ka je ka rubuta, ka ce 'yansanda ba abokan kowa ba ne." Ya ce da ni.
Na yi dariya, sannan na nuna masa Ofisa Ashakunu na ce, "Yau na ga mutumin cikin damuwa, wani abu ne ya faru da shi ne?"
Ofisa Bello ya yi dariya ya ce, "Abubuwa da yawa ne suka faru." Ya sake kyakyacewa da dariya kamar ba shi ba ne ya cukule min dazu a kan tambaya ba, ya ci gaba da cewa.
"Ashakunu ya ci burin wannan sabon karin albashin da wannan gwamnatin ta ce za ta yi, don yana son zai yi aure a wannan lokaci, aka yi ta jan biyan sabon albashin, lokacin da za a yi karin ya zo kuma, sai ya zo da wani irin sabon salo na ka-gani-a-kwaryarka, in da shi ya ga karin Naira dubu daya da naira saba'in. Sannan, dama ga shi tun tuni yana cikin damuwar rufe boda da aka yi, domin an hana maigidansu shigo da kaya, wanda kusan kullum suke samun kudi daga gare shi, don haka yanzu shi a duk duniya ba wanda ya ke jin haushi kamar maigirma shugaban kasa, don ya ce shi ya lalata masa shiri." Ya ci gaba da dariya.
Ni kam bin shi na yi da kallo ina nazarin irin girman damuwar da yake ciki.
A daidai wannan lokacin wani dansanda mai suna Sajan Ado ya shigo rike da wani dogon sauri mai siffar rakumin dawa saboda tsayi da dogon wuya. A bayansa kuwa mutane ne kusan su shida suka dafo masa baya, a cikinsu daya na rike da wuyansa wajen da ke nannade da farin kyalle wanda ya jike da jini, haka nan duk rigarsa jike take da jini - Gabadaya muka mayar da hankulanmu gare su, musamman ni da nake son labari.
Kai tsaye a gaban Ofisa Ashakunu suka tsaya, ya daka musu tsaya, "Kai me ya faru?"
Sajan Ado ya nuna dogon saurayi ya ce, "Ga su nan musu suke yi, shi ne wannan ya dauki almakashi ya caka wa wannan."
Ashakunu ya dubi saurayin wanda aka cakawa almakashi, da alama jini na daukarsa yana bukatar taimakon gaggawa, sannan ya dubi dogon saurayin nan ya ce, "Kai wanne irin musu kuke za ka kashe shi haka?"
Cikin gadara dogon saurayi nan ya gyara tsayuwa, don a tunaninsa idan ya fadi abin da ya faru 'yansandan nan za su goya masa baya, ya ce, "Yallabai wani mummunan laifi ya aikata, shi ya sa na hukunta shi."
Muka kara nutsuwa, don jin irin laifin da ya yi, ya yi masa wannan hukunci da yake fada.
Ashakunu ya ce, "Kai muke sauraro..."
Dogon saurayi ya ce, "Yallabai muna cikin musu kawai sai ya yi zagi, shi ya sa na kaddamar masa..."
"Wa ya zaga?" Ashakunu ya bukata.
"Buhari ya zaga..." Dogon saurayi ya yi kokarin fada, amma bai kammala maganarsa ba, sai jin mari ya yi hadi da barin makauniya daga kamfacecen hannun Ashakunu. Kafin wani lokaci ya hadawa dogo jini da majina har da cire masa hakori guda, ya dora da fadin.
"Ka ji dan iska, wahalalle, wanne kundin doka ne ya ba ka ikon ka hukunta mutum ba tare da zuwa wajen hukuma an tantance laifin da ya yi ba, tare da sanin dalilin da ya sa ya aikata laifin da kuma halin da yake ciki a lokacin da ya yi laifi irin wannan? Ka san wane hali aka jefa shi ya sa shi aikata laifin? Ko kuma ka san wanne Buhari yake nufi?"
Yana magana yana kirbar dogo, ni dai na lura Ashakunu fanshe haushinsa yake yi a kan dogo, ya gama yi masa laga-laga, ya watsa shi a sel, sannan ya ba da dama a je, a kai saurayin da aka cakawa almakashi asibiti, don taimakon gaggawa.
Suka rankaya, ni ma na tashi, na rufa musu baya, don ganin yadda aikin 'yansandan yake a asibiti.

Mu kwana nan.

Kabiru Yusuf Fagge

1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...