Sunday, January 5, 2020

ALKALAMI: GAJERUN LABARU 10 DA SUKA LASHE GASA






ALKALAMI...
Gajerun Labarun Gasar
Bikin  Fadila H. Aliyu Kurfi





Tattarawa
Kabiru Yusuf Fagge
Shamsudden Fatimiyya
Zaidu Barmo



Alkalai
Abdurrahman Aliyu
Ibrahim Muhammad Indabawa
Shamsuddeen Fatimiyya


WACE CE FADILA H. ALIYU KURFI
C
ikin girmamawa nake gabatar da fitacciyar marubuciya, 'yar gwagwarmaya, 'yar jarida, mai sharhin al'amuran yau da kullum (public commentator), fitacciyar mai tsokaci a kafar sadarwar zamani (social media critic), kwararriya a fagen ado da kwalliya (beauty therapist); FADILA H. ALIYU KURFI (BABY FADILA)

KARATU DA KURUCIYA A TAKAICE
An haifi Fadila H. Aliyu Kurfi a ranar 12 ga watan Disamba 1992, a birnin Katsina. Mahaifanta Alhaji Aliyu Kurfi da Hajiya Halima Aliyu Kurfi dukkansu 'yan asalin Kurfi a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina. Baby Fadila kamar yadda aka fi sanin ta, ita ce ta biyu a wurin mahaifiyar su, bayan Zaharaddein Aliyu da kuma kannenta hudu Bishir Aliyu, Abdurrahman Aliyu, Maryam Aliyu da Amjad Aliyu sai kuma diyarta guda daya Ibtihar Bashir Kurfi.
Fadila Kurfi ta samu damar yin karatun addinin Islama, da na zamani tun daga makarantar Islamiyya, firamare, har zuwa sakandire. Haka kuma ta halarci Babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Katsina (F.C.E. Katsina) inda ta samu takardar shaidar malamta mai daraja ta daya (N.C.E.) a fannin Ingilishi/Hausa (English/Hausa). Haka kuma Fadila Kurfi ta yi karatun Diploma a fannin Girke-girke, da kuma wani satifiket din a fannin Ado da Kwalliya.

GWAGWARMAYA DA RUBUCE-RUBUCE:
Fadila H. Aliyu Kurfi ta fara sha'awar rubuce-rubuce tun tana karama, ta yi rubuce-rubuce a fannoni da dama, mafi shahara a cikinsu na labarun jarumta da yake-yake. An buga littafinta na farko mai suna BUWAYAR SADAUKAI ya fita kasuwa a shekarar 2014, sai kuma RUNDUNAR SADAUKAI a shekarar 2016.
A bangaren fafutika ma ba a barta a baya ba, domin Fadila Kurfi tana cikin kungiyoyi da dama, da ita aka kafa kungiyar marubuta ta jihar Katsina, ta taba zama shugabar riko ta kungiyar, da kuma mataimakiyar shugaba ta jihar Katsina. Fadila mamba ce a kungiyar Mata Marubuta 'yan gwagwarmayar nema wa mata mafita "Mace Mutum", haka kuma mamba ce a kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Katsina (ANA Katsina). Haka kuma Fadila Kurfi ta kasance daya daga cikin zakakuran marubutan da suka kafa kungiyar nan ta marubuta masu rubutu da harsunan gida (NILWA). Daya daga cikin abin da tarihi ba zai taba manta wa da shi ba a rayuwar Fadila Kurfi, shi ne taron Ranar Marubuta Hausa na Duniya, wanda kyakkyawan tunaninta, da hazakar ta suka haifar a birnin Kano a 2016, da Katsina 2018, wanda ita ce ta assasa shi.

NASARORI
Kasancewar Fadila marubuciya mai fikira da hazaka ya ba ta damar shiga gasar rubutu a fagage daban-daban, a lokuta daban-daban, ba domin son samun kyautuka ko neman suna ba, sai dai domin sha'awarta da rubutu da kuma bayar da gudunmawa ga kasa da al'umma baki daya.
Baby Fadila tana daya daga cikin zakakuran marubuta da suka samu nasara a fitacciyar gasar gajerun labarai ta PLBC da Makarantar Malam Bambadiya, karkashin jagorancin Shehin Adabin Hausa na wannan zamanin, Farfesa Ibrahim Malumfashi. Da gasar Na'awwa Literary Award, haka kuma ta taba lashe gasar rubutun zube ta Sabuwar Duniya da littafinta mai suna RUNDUNAR SADAUKAI. Haka kuma gudunmawar rubuce-rubucen Fadila Kurfi a kafar sadarwar zamani (social media) sun taimaka wajen sauya al'amura da dama a cikin al'umma.

Duk wanda ya san Fadila H. Aliyu Kurfi, idan aka tambaye shi abubuwa hudu kacal da yake iya tunawa game da ita, a lokacin da aka ambaci sunanta, na tabbata zai ce; 'Yargayu ce, mai dagewa da mai da hankali ga abin da ta yi imanin zai kai ta ga nasara ba tare da karaya ko tsoron kasawa ba, mace ce mai kishi da son addini da komai ake yi ba ta wasa da sallah, sai kuma yawan murmushi.

Za a iya samun Fadila H. Aliyu ko kuma karanta rubuce-rubucenta ta wadannan adiresoshin a yanar gizo;
Facebook: Fadila H Aliyu Kurfi
Twitter: fadila_kurfi
Instagram: fadila_kurfi
Email:fadilahkurfi@gmail.com

Ga Yazid Nasudan


KANIN MIJI…
08093585811

"G
angar jikina  ne  kawai  tare da kai, amma zuciyata na mallakawa waninka” Na fada ba tare da na damu da na dube shi ba. Saboda na riga na saka kuba na kulle zuciyata, komai ta fanjama-fanjam.
Daga cikin matakan da na san za su biyo baya, shi ne in ji rugugu, duka ta ko'ina, amma hakan bai faru ba. Ina ta son na ga dalilin da ya hana shi dukana. Ya kura min ido yana duba na, kwalla ta cika masa idanuwa. Bakon al’amari, ban taba ganin hawayensa ba sai yau. Na sha fadi ko na aikata abin da bai kai wannan ba, ya dau mummunan mataki a kaina.
“Hadiza.” Ya ambaci sunana a karo na farko tun bayan shekaru goma sha uku, na ji kamar ba da ni yake ba. "Na aikata munanan ayyuka, na saka ki cikin kunci, na hana miki hakkinki na aure, na zalunce ki ina sane, ban zo gabanki don na nemi yafiyar ki ba. Sai don na yi kokarin saukaka miki wasu abubuwan”
Ya fada hawaye na sauka a kan fuskarsa. "Hakika ban dace dake ba, ke fara ce, ni baki ne, babu dalilin da za mu ci gaba da kasancewa a karkashin inuwa guda daya, zan sawwake miki tare da baki abin da za ki rike kanki, kafin Allah ya yi miki musanye mafi alkairi, don na san ni ba alheri ba ne a gareki.”
Ya saka hannunsa a aljihu ya dauko wasu takardu guda biyu, ya miko min, ban karba ba, amma idanuwana na kansa. "Wannan chekue ne na miliyan biyu, da kuma takardar saki daya. Gara na sawwake miki a kan ki cigaba da zama a karkashina ina gurbata miki rayuwa.”
Gabana ya yi mummunan faduwa, ji nake kamar a mafarki.  Ta ya ya ma haka zata faru, mutumin da ya tsane ni, yake fifita 'yan iskan karuwan a kaina. Ya sha kawo matan banza gidan nan bangarensa, ba na ganinsu, amma ina jin hayaniyarsu, tun abin yana tafasa min kokon raina, har na sallama na saduda, saboda ba ni da in da zan je, da ya wuce nan in da nake din. Akwai kaninsa Salmanu wanda yake masifar kishi na, yana tausaya min, a duk sanda Sahabi ya ji sha'awar cin mutunci na, suna debo ta da Salmanu, don akwai lokacin da ya balla shi bal a hannunsa na dama, saboda kawai Salmanu ya shiga gabana ya ce ba zai doke ni ba, shi kuma ya hassala, ya hau shi da duka, ya fi shi karfi, wannan ya sa bai bata lokaci wajen gamawa da shi ba, ya dawo kaina, tare da kai min duka da kafa, wanda ya yi daidai da lokacin da Salmanu ya kawo min dauki.
Tun daga lokacin ni da Salmanu muka zama Hassan da Usaina, komai nawa da shi nake yi, babu wani abu da zai yi da ban sani ba.
Wannan kusancin namu ya yi yawa wanda ya haddasa shaidan ya yi galaba a kanmu, muke neman juna, har ciki ya shiga, yanzu haka ina dauke da cikinsa wata hudu.
“Hadiza in har na nemi da ki yafe min hakika ban yi miki adalci ba, amma ke akan karan kanki ki ji tausayina, ki yafe min, wallahi ban taba jin labarin wani azzalumin mutum irina ba. Ban taba ganin wata mutuniyar kirki da take bautawa aure kamar ki ba.”
Na fashe da kuka."Ka yafe min Sahabi, na ci amanarka, na dauka, na rasa ka, ban yi tsammanin zaka sake dawowa ta kaina ba, na bai wa waninka kaina, yanzu haka ina dauke da cikinsa…”
Ban kai ga rufe bakina ba, na ji kutufo, kafin na ankara, na sake jin wata mahangurbar. "Allah ya tsine miki albarka Dije, ni za ki yi wa wulakanci, ashe ke ma karuwa ce, na dauka wata mutuniyar kirki ce, ashe duk…” Yana sambatun zagi na, yayin da ni kuma nake kokarin kwatar kaina. “Don Allah ka yi hakuri ka…”
Wajen ya yi tsit!  Sahabi ya yanke jiki, ya fadi, jini na zuba daga kansa ta baya.
A tsaye rike da tabarya a hannunsa yana huci, Salmanu ne."Bai dai ji miki rauni ba ko?” Ba damuwa ko alamar nadama ko daya a muryarsa.
Cikin firgici da tsoro na yi Magana. "Salmanu me ya sa za ka doke shi…?”
"Duk ran da ya kara taba ki, na yanke hukuncin da zan masa.” Ya katse ni.
“In kuma ya mutu fa?” Na tambaye shi  ina kallon Sahabi da yake kwance.
“Wa ya gaya miki na yi masa dukan da zai tashi ne?”
Da gaske Salmanu ya kashe yayansa Sahabi saboda ni.


MAZA GUMBAR DUTSE
Abba Abdullahi Gumel

"M
aza ne, sa'a dai maza, maza gumbar dutse an buga da ku an bar ku, 'yan adawa sun yi sun kare, gamji kake, dan Abdu yau fa akwai fita, domin akwai kwalkwal, don kuwa shegen malamin nan yau sai jikinsa ya fada masa,wannan gemun da ya tsaida yau din zan aske masa shi da kwalba."
"Haba wannan wacce magana ce kake fada Faruk? Duk iskanci na a makarantar nan bai kai na zagi ko na ci mutumcin malamina na boko ba, balle na Islamiyya, malamin Islamiyya fa kake cewa zaka yiwa kwalkwal? Haba Faruk, ban san me ya sa ake daukar malaman Islamiyya kaskantattu ba, Faruk ban san yaushe zaka nutsu ka yi hankali ba? A duk duniya babu wani gata da iyaye za su yiwa diyansu da wuce su basu ilimi ba, sannan su zaba musu abokai nagari. Faruk a lokacin baya ko shekarun baya iyaye su ne masu zaba wa diyansu abokai, amma a yanzu sai dai yaro ya zaba wa kansa aboki nagari, sannan ya siya wa kansa mutumci ko akasin haka. Mutane nawa ne ka sani wadanda suka kai girmanmu iyayensu suka zaba musu abokai? A lokacin yanzu wannan batun ya zama tarihi...."
"Ya yi alaramma." Faruk ya daka min tsawa cikin raini ya ce "Dan gidan Katuhu jikan Sani zaka fara yi wa mutane wa'azi? Ka ga ni fa dan gata ne a gun Babana akwai Naira, ya dauren min gindi na yi duk abinda nake so, ko me na aikata ko ba ni da gaskiya ni ne mai gaskiya, na zama takalmin karfe kowa na taka ya taku, malamai nawa na zaga a makarantar nan amma ba dama a kore ni saboda Babana, da ya zo, ya dage akan karya ne, sannan ya bada hakuri komai ya wuce ka gane? Ni yanzu ba na shakka, ba na shayi."
Ilimi gishirin rayuwar duniya, jahilci mugun ciwo, Faruk bai samu ilimi ba saboda lalataccen Babansa da kuma raina malamansa, wanda raina malamai yanzu ya zama ruwan dare musumman ma malaman Islamiyya.A karshe bayan rasuwar Babansa, Faruk ya zama kasurgumin barawo saboda ba mai ba shi, ba mai daure masa gindi wanda a yanzu haka yake a garkame a gidan yari.


ILIMIN 'YA MACE
Zaidu Barmo

N
a taso a karamin gida, karamin gida a Hausa ta ba yana nufin karamin gida masu karamar magana ko rashin cika alkawari ba, a'a ina nufin talakawa wadanda kuma duniya bata ji kukansu a kan babu ba, masu daukar kaddara yadda ta zo da kuma godiya ga Allah, saboda iyayena sun riga sun yarda da kalmar nan ta cewa, komai ya yi farko zai yi karshe, sannan wani ba zai taba cin rabon wani ba.
Sunana Aishatu mu 'yan asalin Birnin Gwari ne ta Jihar Kaduna, na ji an ce har wadanda suka haifi mahaifana ma 'yan can ne, amma yanzu zama ya dawo damu Jihar Kano. Gidanmu mace ta dade tana karatu daga karamar sakandire shi kenan, duk kuwa nacinta da kwakwarta sai dai ta yi hakuri, shi ma don mahaifina yana ganin cewa, kar a kai yarinya gidan miji bata san komai ba, a kalla dai kin sami na karanta takardar wasika, da kudurin cewa, ai bukatar ma-je-Hajji-Sallah.
Ni mai son karatu ce, ba don komai ba sai don in taimakawwa 'yan'uwana mata, mace bata da wani aibu ko laifi don ta tsaya ta yi karatu mai zurfi, idan tarbiyya ake bukata daga mace ake nemanta tun farko, saboda ita ce uwa mai raino, har ma nake tunanin cewa ta ya ya wadda bata samu tarbiyya daga ilimi ba zata koyar da wasu?  Wannan ya sa na fara fafutuikar ganin cewa ni na zarce sauran 'yan'uwana mata da suka rayu a gabana cikin gidanmu.
Allah ya tarfawa garina nono, da naci gami da addu'a da komai wannan burin nawa ya cika, na samu damar shiga budaddiyar jami'ar nan ta Nijeriya wato 'National Open Unibersity' wadda aka kirkira a shekarar dubu daya da tari tara da tamanin da uku '1983' zamanin mulkin Shehu Shagari.
Dama mahaifina yawo ne ke baya so, kuma karatun makarantar a gida ne da kwamfuta,  illa iyaka in za a yi jarrabawa mu tafi cibiyar jami'ar dake nan Kano, ko kuma in muna son yin wani bincike. Da burina ya cika, na gama karatun jami'a sai na samu aiki da hukumar Tattara Haraji, sai na zama mace daban da al'umma suke girmamawa, har ya zamo idan na je waje ana cewa, ga mai digiri nan, daga ni sai ya zamanto masu kallon wadanda suka yi digiri ba su samun aiki, suka gane cewa ashe ba haka zancen yake ba. Suka gane cewa, kura ce da fatar akuya, kuma kowa da irin sa'ar da yake zuwa da ita a duniya tun da aka halicce shi. Don sun fahimci cewa idan mace ta nutsa a karatu tana taimakon al'ummarta kuma tana zama abin koyi ga 'yan'uwanta mata har ma da maza, don ni ilimi ya ba ni damar kafa gidauniya ta taimakon mabukata, na yi abubuwa da yawa da nake so.
Bayan na yi aure kuma ban dogara da abin da mijina ke samu ba, muna taruwa mu rufa wa junanmu asiri, ba tare da wani ya ji sirrinmu a waje ba.



DA BAN HADIYA BA
Muhammad Mubarak Dr.
08138131990, (realmubarak245@gmail.com)

D
uk yanda na so na tarairayi hankali da tunani na wajen ganin na daidaita nutsuwar zuciyata hakan neman gagara ya yi sakamakon kisfewa da batan-dabon da kwanciyar hankali ke neman yi wa duniyata,  musamman wannan yanayin na muku-mukun sanyi da ake tsugawa. Wata iska mai karfi ta yi wa rufin kwanon dakin dirar mikiya cikin talatainin daren da ban san karfe nawa ba, ban sake dulmiya gami da neman daskarewa ba sai a lokacin da na ji saukar wata kwarankwatsa wadda ta sanya dakin girgiza kamar zai rufta, kafin na ankara fankar dake manne da dakin ta fara  lilo kafin daga bisani ta tarwatse filla-filla tamkar diddigar itace.
Na yunkura ina salati gami da sallamewa, sai a lokacin na lura a dakin su Hanif nake lokacin da na zo kwantar da Mus'ab ashe barci ya yi awon gaba da ni,  amma abin da na kasa gasgatawa shi ne shin wannan tsawar da walkiya da idanuwa na keta min nuni a farke ne ko a zihiri?  Na mike da sauri domin neman wata mafitar, amma me? Wata uwar walkiya da aka sheka gami da tukuicin tsawar data nemi fitar da ni hayyacina ya sa, na koma na kife ina mai da numfarfashi gami da kame-kamen addu'ar da za ta kawo min mafita.Ni kaina da za a ritsa ni a lokacin ba zan iya ayyana me nake karantawa ba, don sai da na yi nisa a karatun sannan na ankara da addu'ar dana kamo, wato addu'ar shiga bandaki, ban sani ba gigicewa ce ko me?  Da kyar na iya kamo Ayatul Kursiyyu bayan na ankara da nisan da na yi a karanta addu'ar buda baki.
"Rashida! Rashida!! Rashida!!!" Kamar daga sama na ji muryar mijina Mahiru yana kwalamin kira, da hanzari na tarkata tsummokaran tunani na na mike jiki na rawa tamkar tsohuwar 'yar borin da ta ji sautin garaya, baki na rawa na kalli Mahiru dake tsaye bakin kofa na ce "Mahiru lafiya?"
"Ina fa lafiya, dama cin bashin wannan matar ai masifa ne?"
Na kwalalo ido cike da mamaki na ce "Wace ce?"
"Atine mai mai mana." Ya yi furucin gami da sakin gajeren tsaki, ganin mamaki na neman kulle min ciki ya sa na ari mazantaka na yo waje da sauri, inda na iske Atine mai mai rike da cocila sai karairaya take tamkar mai rawar sarmadan, na kalle ta cike da mamaki na ce
"Atine lafiya  a wannan talatainin daren?"
Ta watsa min kallon sama da kasa samfurin da wa kika zo Kano ta ce "Kamawa ta yi da ba ki ci ba, da ba ki gan ni ba, maza-maza je ki hado min kan kudade na, tafiya ce ta same ni cikin daren nan, kuma ko kwandala ba zan tafi na bar wa wani da ba." Wani daskararren bakinciki da takaici suka taru suka tokare min makoshi, ni gani ba gwanar dura ashariya ba balle na antaya mata ko da mudu daya da rabi ne, domin karya lagon tsiwar ta.
Ganin takaici na Nneman karya garkuwar jiki da tunani na ya sa na juyo, na kalli Mahiru na ce "Ai ga irinta nan sai da na ce maka kar a karbi bashin madarar nan ka ce sai an karba dole ne sai an sha shayin da madara? Ko in muka sha ba madara mutuwa zamu yi? To yanzu ga ta nan ai sai ka nemo hakkinta a bata don DA BA MU HADIYA BA da ba ta zo mana ba."
Ina rufe baki muka ji tsayuwar mota a kofar gida, kafin daga bisani muka ji wasu na salati wasu kuma na rusa kuka, na kalli Mahiru, ya kalle ni kafin daga bisani ya yi waje da sauri, ni ma na take masa baya ina wasi-wasi. Kofar gidan Atine mai mai motar ta tsaya, ina kai kaina hango Lami kishiyar Atine da Fatsima Babbar 'yarta suna ta sharbar kuka, Lami na hango ni ta karaso da gudu tana tafa hannaye ta ce.
"Aina'u, Atine kwana ya kare, yanzu muka dawo daga asibiti." Take na nemi daskarewa jin furucin Lami, ban sake neman nutsuwata ba sai da na ga ana fito da gawar Atine daga mota na yi saurin fitowa daga gida, ina barin jikin shin dama fatalwar Atine ce ta je ta ritsa mu karbar bashin da muka ci na Atine".
Tammat.



MUGUN KAWANCE
Rahma Ahmad Muhammad
(Gimbiya Rahma).

"H
aba Kawata, ya ya za a yi ki zauna namiji yana gasa miki aya a hannu? To wallahi ki nutsu, ki yi wa kanki fada; domin mazan yanzu sai an ci su da wuta”. Rabi'a ce tsaye a bakin kofar falon; tana magana cikin fushi da daga murya ga kawarta Zainab, yayin da ita ke jingine a jikin firji daga cikin falon. Cikin sanyi jiki, Zainab ta fara magana mai dauke da tausayi, “Kin san yanayin rayuwar sai a hankali, yanzu ba ta anko ko dinki ake yi ba, ana kokarin neman abin da za a ci ne, ni kuma Baban Walid kam alhamdulil Lah, duk da nauyin da ya masa yawa, yana kokari a kanmu…..”.
“Dakata da Allah! Ana nuna miki Annabi kina rufe idanu, yanzu wa yake tausayin namiji? Namijin za ki tsaya kina marairaicewa har kina tausayinsa, to ke idan ba ki kunsa masa ba, shi zai kunsa miki muguwar kishiya! Wallahi dama ce kawai bai samu ba, amma da ya samu dama, zai kawo wadda za ta mayar da ke bai wa. Da kyawunki, da kuruciyarki a mayar da ke boyi."
Ba a dauki lokaci ba kuwa, zugar Rabi’a ta cike zuciyar Zainab; inda ta sauya daga halin kwarai zuwa mummuna ga mijinta; wanda a baya take kiransa da FARIN CIKIN RAYUWARTA!
A yammacin ranar Alhamis, bayan Nasir ya dawo daga wurin aiki cikin gajiya da yunwa, Zainab ko kallonsa bata yi ba, tana zaune a kan kujera ta dora kafa daya kan daya; tana kadawa. Bayan tsawon lokaci, Nasir, cikin mamaki ya fara tambayar Matar tasa me yake damunta. Idan har ta san da ita yake ma, to dutse zai iya yin karfin hali ya amsa magana. Cikin nuna isa, ta tashi ta nufi dakinta ba tare da ta kalle shi ba.
Bayan tsawon lokaci cikin wannan yanayi na cin zarafi da bakaken maganganu daga bakin Zainab, wanda ya sa dole Nasir ya kai karanta gidansu. Mahaifanta suka zo har gidan suka yi mata tatas.   
Bayan tafiyarsu Nasir ya dawo gidan inda ya tarar da ita tana kuka. Cikin tausayawa ya nufi inda take ya durkusa yana tambayarta abin da yake damunta. Mangaje shi ta yi, sannan ta ci gaba da magana cikin karaji.
Cikin tattausar murya, Nasir ya ce, "Zainab, anya kuwa kina cikin hankalinki? Ni dai na san tsawon lokaci ban bata miki ba, ban san me ya faru ba…..”
Katse shi ta yi da tsaki, sannan ta ce, “Ka je ka tambayi karuwar da kake kai wa kudin ka! Ka ga, idan kai dan halak ne, ka sake ni! Na gaji da zaman talaucin da nake yi a gidanka!”

Ire-iren wadannan kalamai ne suka rinka safa da marwa a zuciyar Nasir, amma har kawo yanzu, ya rasa musabbabi, karshe ma sai zargin neman matan banza ne ya keto tsakaninsa da matarsa. Cikin tausayi dai, ya dago kai ya dub eta ya ce, “Zainab! Yanzu zargin da kike yi min ken an? Yanzu daman…..” “Ka ga Malam, ba ka ji abin da n ace ba? Ka sake ni ko na zama ajalinka”.

Bayan tsawon lokaci da mutuwar auren Zainab, inda ta koma gidan Kawunta, Kawu Idi, sakamakon Babanta ya ce ba za ta zauna masa a gida ba. A wannan gida ta gamu da wahalhalun rayuwa wadanda ba ta taba riskar su ba a rayuwarta.

 “Kalar kayan ankon bikin Rabi’a na kawo miki”. Haule ce kawa Rabi’a da Zainab take gaya wa Zainab yayin da suke rakabe a soro.
“Biki kuma?” Cikin mamaki Zainab ta yi tambaya.
“Ke ba ki da labara?” Cewar Haule.
“Inda na sani ai ba zan tambaye ki ba, to wa za ta aura?”
“Wai ke duk ba ki san abin da ake ciki ba? To Nasir za ta aura? Wannan ne abin da ya sanya aka dauki Zainab sai gadon asibiti, saboda abin da ta ji an labarta mata.

  Bayan biki da wata biyu bikin ne, rayuwar kunci da da-na-sani suka kara mamaye zzuciyar Zainab, wannan ya sanya ta yi takakkiyar har gidan domin bai wa mijinta hakuri da kuma cin zarafin Rabi’a. Ba ta yi nasarar komai ba, domin Rabi’a ta yi mata tatas, tare da nuna mata ba ta da wayo, cikin wannan hali, Nasir ya dawo, inda shi ma ya yi wa Zainab koran kare a gidansa.
A nan Zainab ta gane lalle tsakaninta da Rabi’a; MUGUN KAWANCE ne, ita ma ta yi aniyar ramuwa.



AN DAINA KIWON DABBA...
Name: Amina Dauda Abubakar
Phone No.: +2349038146336
Address: T/Matawalle, Katsina

A
 kan hanyata ta zuwa gida, na hadu da kawata Hauwa'u Ahmad. Cikin fara'a da sakin fuska muka gaisa. Ta dube ni, "Fatima Isma'il, daga ina haka?"
"Na je kasuwa ne, na yo wa Umma cefane."
Murmushi ta kuma yi, "Ai na dauka ko kin je shopping ne ke da Mukhtar (tana nufin saurayina)."
"Ni kuma? Lallai ne kawata wannan ai sai ku manya masu duniya."  Na bata amsa. Ta gwalo ido "Wa,  ni? In kin gan ni lahira kai ni akai." Ta ban amsa.
Na dube ta cikin murmushi, na ce, "To ni ma ba da ni ba, sawa jaka lalle a kafar baya. Kamar ba ki san halin samarin na yanzu ba, ke dai a yi ta sha'ani 'yar'uwa duk haka suke."
"Haka ne, duk wadda ta yi dakon turmi, tabarya ba za ta gagare ta dauke ba".
"Haka ne, kowa ya kona rumbunsa; ya ji inda toka ke kudi." In ji ni.
Ta ce, "Ke Fatima! Me ye hujjarki na fadin hakan?"
"Kin san dalilin ke ma, domin duk macen da ta riski kanta a wannan zamanin; ta san halin samarin wannan zamanin ban ce duka ba. Mafi yawansu suna mana kyauta ba don Allah ba, sai don samun wani bangare na jikinmu. Yarda da bukatarsu shi ne samuwar kyaututtukansu. Ki dubi Kyauta! Wacce a da, abin tausayi ce a cikin mu kawayenta, amma a yanzu ki duba ki ga wayar hannunta ma ko 'ya'yan manya sai haka sai hakan. Ki kalle ta ki kalli gidansu abincin da za su ci ma nema suke a taimaka musu."
Hauwa'u ta amshe, "Ke dai bari! A yanzu fa ko unguwa zata je akwai wanda  ke kai ta a mota, ba ta ko tunanin gaba domin da sun gama tsotse kwallon mangwaron, sai su yar; su huta da kuda."
"Haka take kawata."
Mun zo daidai kwanar gidanmu,  na ce, "Allah ya kyauta! Allah ya ganar da duk wanda ke cikin irin wannan halin. Mu kuma Allah ya sa mufi karfin zukatanmu don yanzu duniyar nan AN DAINA KIWON DABBA MUTUM AKE KIWO."
Ta ce, "Amin."
 Kowaccenmu ta shige gida.





BIYU BABU
Idriss Said
Z
aune yake, ya tasa Alhaji gaba da na mujiya, ya kuma baza na zomo, cike da zakuwar ji daga bakin Alhaji dalilin  kiran da ya yi masa.
Bayan gyaran murya Alhaji ya ce.
“Malam Habibu na kira ka ne a kan maganar tsohuwar dalibarka Fati.”
“Na'am, Alhaji, Allah ya sa dai lafiya.” Habibu ya tambaya cike da kulawa.
“Lafiya kalau.”
“To masha Allah.”
“Habibu gaskiya na yaba da yanayinka, idan har kana da ra'ayin kara aure, to ga Fati nan, ka turo magabatanka, zan aura maka ita, kuma sadaka, na dauke  maka komai, daga sadaki har lefe.”
Habibu tamkar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna.  Godiya sosai ya yi wa Alhaji.
“Kuma in sha Allah daga nan ma gida zan wuce domin kai maganar ga Kawu.” Cewar Habibu
Cikin mako guda aka daddale magana aka kuma tsaida ranar daurin aure.
Habibu sai farin ciki yake ta fadi gasassa. Duk kuwa da yadda yarinyar ta yo takakkiya, ta same shi  ta zayyane masa abin da ke cikin zuciyarta. Tana da wanda take so, amma bai kula da zancenta ba, domin yana ganin zai tsinci dami a kala.
Duk da nuna turjiya daga ita amaryar, amma daga karshe dai an daura aure an kai amarya dakinta.
Shekara guda cur da daura wannan aure amma zama ya ki dadi, har ta kai ga Habibu ya fara nadama da wannan aure da ya yi. Har zuwa lokacin da ya gama yadda zaman shi da Fati ba mai yiwuwa ba ne. Domin da kansa ya kama ta a dakin tsohon saurayinta Bala Niga, ganin ba zai iya jurar hakan ba ya sake ta.

Bayan wata biyar da rabuwarsu Habibu ya samu wata bazawara suka daidaita, aka  daura musu aure. Daidai lokacin da ita ma Fatin ta samu sahibin zuciyarta har an sanya masu rana.
Ana tsaka da shirye-shiryen tarewar amarya sabon surukin na Habibu ya aiko aka kira shi.
“Malam Habibu akwai wani labarin ya riske mu dangane da tsohuwar matarka, wai sun je asibiti an yi masu gwaji a shirye-shiryen auren da suke yi. Sai dai wai ita an samu tana dauke da cutar  kanjamau.”
Habibu tamkar wanda aka yi wa albishir da ranar mutuwarsa. Surukin nasa ya ci gaba da cewa;
“To yanzu abin da nake gani ya kamata mu yi shi ne, za mu je asibiti kuma a yi muku gwaji kafin Hadiza ta tare, sakamakon gwajin shi zai bayyana makomar aure ku.”

Daren ranar Habibu yadda ya ga rana haka ya ga dare. Babban abin da ke kara kaga masa hankali shi ne, tuna waccen ziyara da ya taba kama Fati ta kai wa tsohon saurayinta Bala Niga, alhahi tana matsayin matarsa. Addu’arsa daya a yanzu Allah ya sa a iya ziyarar suka tsaya. Domina iya saninsa bai taba kusantar wani abin da zai iya sada shi da wannan cuta ba.
Amma sai dai kaddara ta riga fata, a asibiti an tabbatar da Malam Habibu yana dauke da cutar HIB. Nan take  aka tilasta masa ya saki amayaryar tasa.
“Laraba za ta je asibiti a gwada ta, in har ba ta da wannan cuta to lallai za ka sake ta.”
Zancen wan uwar gidan Habibu ke nan. Wanda takanas ya zo har gida ya shaida masa, bayan ya jajanta gare shi. Zancen da kuma  ya kara daga wa Malam Habibu hankali ke nan, domin ya san in babu kara babu abin da zai ci gawayi, saboda rabon da ya kusance ta har ya manta, saboda jinyar da ta yi fama da ita tsawon lokaci.   Karshe.          


UNGULU KAZAR KOWA
Nasiru Kainuwa Hadejia

"K
e marar mutunci, ki tashi, ki share mana gidan nan, in kin share kuma ga nika can ki dauka ki kai.”
Jamila duk da fama da ciwon kan da take haka ta yi karfin hali ta tashi, ta dauki tsintsiya ta share gidan tas! Ta dauki nika ta fita da shi, Fannata kuma ta na kwance. Jamila tun bayan rasuwar mahaifiyarta sai ta koma tamkar 'yar bora, duk wani aiki kama daga shara, wanke-wanke, diban ruwa, kaiwa nika, girki duk ita ce ke yi. Fannata kuma ba abin da za ta yi saboda ita ce mai uwa a gida.
Haka rayuwar Jamila ta ci gaba ta tafiya cikin tsangwama, zagi da cin mutunci ba irin wanda ba a mata. Idan abu aka rasa sai a ce Jamila ce ta dauke, a dole aka kakaba mata tambarin sata duk da cewa ba aikin ta ba ce.
"Ni ungulu ce kazar kowa." Abin da ta fara cewa da ni kenan. Ba tare da na nuna wata damuwa a fuska ta ba na ce "Haba wannan duk ba wata matsala ba ce, da gaske son ki nake, ba da wasa ba. Amma fa a cikin zuciyata na kadu sosai kawai dai na san Allah ya jarrabe ni da son ta ne kawai ba yadda na iya. Kusan kowace rana da yamma na kan ganin wucewar ta ta kofar shago na, yau ce ranar da na yi karfin hali na tsayar da ita. A zuciyata na sake nanata abin da ta fada “Ni ungule ce kazar kowa” Wato tana nufin ita karuwa ce kenan? A can cikin raina sai na ji kamar an ce da ni "e karuwa ce kai dai ba ka na sonta ba, mene ne abin damuwa? Kawai ka isar mata da sakon soyayyarka watakila ka zama silar da za ta ajiye karuwancin."
Na dan yi murmushi na karfin hali na ce ‘yanmata mene ne sunanki?"
Ta ce “Jamila”
Na dan sunkuyar da kai na kasa, dan jim kadan na dago na kalle ta na ce “A gaskiya ba wani kwane-kwane da zan miki ina sonki in har ma kin amince da ni zan aure ki matukar za ki ajiye karuwanci.” Sai na ga ta min wani irin kallo wanda na kasa fahimtar na mene ne. Mun shafe kusan awanni biyu muna hira, abin da na fuskanta tsangwama ce da kuma yunkurin yi mata auren dole suka sa ta bar gidan su ta fada harkar karuwanci.
Da kyar na shawo kan iyaye na suka amince na auri Jamila. Yanzu haka mun shekara wajen hudu muna tare, ‘ya’yanmu biyu mace da namiji, Samir da Samiha.
Jamila ta na da ra’ayin karatu, ban hana ta ba domin yanzu saura wata uku ta kammala karatu a makarantar koyon aikin jinya dake cikin birni.
Fannata har wannan lokaci ba ta sami mijin aure ba. Delu mahaifiyar ta abin ya na matukar bata mata rai a kullum.




KUNNE YA GIRMI KAKA
Sadisu Shuaibu
Nguru Yobe State
08060495197

 A
n yi wani dattijo da ya tumbatsa wajen  fasahar zance, ya shahara a fannin hikimar magana, ya kai-ya-yawo a bangaren barkwanci da salo irin na sarrafa harshe, ya kuma kware wajen sanin ma'anonin kalmomin Hausa da inda suka samo asali da tushe.
Ya kasance maigadi ne a wata makarantar sakandiren jeka-ka-dawo mai hade da maza da mata, yana da dan teburinsa da ya ke sayar da kayan tande-tande da lashe-lashe, haka ya sa duk sanda
aka buga tara yara za su yi dafifin zuwa wajensa don su saya, kuma su sha dariyar irin barkwancinsa na zuga abinda ya ke sayarwa da kushe na makwabtansa.
Da zarar yaro ya ce Baba a bani kwakwa, sai ka ji ya ce "Kwakwa mai farin ciki jan baya". Idan kuma wani ya ce "Baba a ba ni alewa." Sai ya tsiri kirari yana cewa "Alewa shan mai koshi mayunwaci sai rogo, alewa da maganin karfe amma in ka sha kwana ya karye". Idan kuma ya ji wani ko wata sun je gurin mai kunu makociyarsa yana iya a ban kunu nan zaka ji shagube yana fadin "kunu nuna ciki a kwana da yunwa." Idan kuwa ya ji wani ya je sayen danwake sai ya yiwa danwake mumunan kirari yana fadin "na kacaa kacalcal na inna mai ruwa ya na gyambo mai yinka bata Sallah Asuba".
Idan ciniki ya lafa sai dalibai su shiga fagen tambaya, anan ne wani ya ce Baba ina da tambaya Baba ya ce yi, yaro ya ce "Wai ni Baba daga ina aka samu sunan Taguwa?"
Sai Baba ya ce "Haba yaro kwai ma ya yi wayo Balanta dan tsako, ai wannan tambayar da jinta kakanka ne ya turoka kuma zaka samu amsarta. A zamanin da sanda babu zani ko riga gwado ake yafawa, an yi wani mutun mai suna Guwa sai gwadon sa ya bule ta tsakiya maimakon ya dinke sai zura kansa ta inda ya bule ya kamo gefe da gefe ya kulle, shigowarsa gari ke da wuya mutane suka gani kuma abin ya ba su sha'awa sai suke cewa ni ma zan yi irin ta guwa ni ma zan yi irin ta guwa daga nan sai ta zama taguwa ake kiran duk wanda ya yi irin wannan.
Rufe bakin Baba ke da wuya sai wata yarinya ta yi tsaraf ta ce "Baba kallabi fa?"
Sai Baba ya ce "'Yar Baba damina kada rago, shi kallabi ya samo asali ne daga sunan wata 'yar sarki da ake kira Labi a zamanin da ba zani ba dankwali sai gwado, sai nata ya yi yawa aka yanke mata sai ta daura sauran a kanta kuma ya mata kyau, sai 'yanmatan gari suka gani sai suke cewa kun ga kan Labi! Ni ma zan yi irin na Labi, shi ke nan daga nan aka mai da shi kanlabi."
To dake bisa al'ada Baba yana bawa yara labari, sai ya ce "Yau muna da labarin shadi/sharo." Baba ya ci gaba da cewa "Wani Bafulatanin gari ne  mai suna Ura, bai taba yin shadi ba ya kwabe don ya ga wasu a kwabe, ya yi kirari a gaban 'yanmata, sai wani ya tare shi da  ya buda kirji aka tafka masa bulala, sai ya zauna, sai wani abokinsa ya lallabo ya ce Ura ba a zama in ana shadi, sai ya ce daga sama na ji ana cewa "kwanta Ura".


SHU'UMAR KAWA
Sadiya Salisu Aliyu
+2349057174177

  N
i ban ga inda na ragi maigidana da komai ba, amma haka rana tsaka yake shaida min lallai zai kra aure, a lokacin da ya shaida min ban nuna wata damuwa ba, hasali ma na yi masa fatan alheri da kawo min tagari. Amma wata rana da aminiyata Hajara ta zo gidana kamar yadda ta ke kawo min ziyara, sai na kwashe zancen aure tas na fada mata, haka ta kama min fada wai ni ba ni da hankali, ban san ciwon kaina ba, kishiya! Ai bala'i ce. To wallahi sai ta rabani da mijina, har tana ce min.
 "Ai ni idan kika ga kishiya a gidana to mutuwa na yi".
 Ta fada tana sake karkatar da daurin dankwalinta da ta kai shi gaban goshi.
"To ni Hajara ya kike son in yi? Kin ga dai auren nan tun da ya kudirin aniyar yin shi sai fa ya yi".
Na fada mata cikin karayar zuciya.
"Hmm ke dai kika sani, dabara kuma ta ragewa mai shiga rijiya" ta fada min tana tabe baki
"Ai ka da a zo garin gaggawa ne in sha ruwa da ciyawa, kin san komai a bi shi sannu-sannu".
 Na fada mata, ba ta ko kulani ba, sai ma wani tsaki da ta ja, sannan ta ce.
 "To wa ma ya sani ko har ke ma sun samu kan naki, don na ga alamar ba a banza ba"
"To wai ke Hajara abun duniya mene ne? Wai kaza ta janyo Muzuru kwanan gida, komai fa dan hakuri ne" na fada mata cikin raha, ita kuwa ai kamar na zugata ne wai ina bayar da mata.
"To shi kenan, sai ki nade hannayenki ki zauna, sai yadda ta yiwu, wai nakuda a dakin mayya".
 Hajara ta fada min tana ciccije lebe.
Bayan Hajara ta tafi maganganunta suka fara tasiri a cikin zuciyata, shedan ya fara yi min karatun wata tsirfa da zan yi wa maigidana da zaran ya dawo. Ai kuwa karfe bakwai na yamma bayan sallar magariba ya dawo, na fara gaya masa maganganu son raina game da auren da yake shirin yi, har shaguben ce masa duk abun da aka kashewa miya; ba za ta yi zaki ba in ba gishiri na yi. Shi kuwa a yadda ya nuna min ko kadan irin maganganun da nake fada mi shi ba abun da yake ji wai an tsikari kakkausa.
Sai wata rana da muka yi waya da Hajara ta kara hure min kunne akan sabon salon da zan kuma fito mishi da shi. Gabadaya na kaurace masa, muka raba shimfida, har wajen wani boka sai da Hajara ta kaini, amma babu abun da ya canja sai da au ren ya tabbata. Daga karshe kuma amarya na lakada mata dukan tsiya, wanda hakan ya sa maigidana ya sakeni. Yanzu dai na dawo gida ina idda sakamakon bin shawarar kawa.


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...