Monday, July 27, 2020

HIKAYOYIN KAIFAFA ZUKATA na Malam Aminu Kano




GABATARWA

A kowanne zamani, a ko'ina a duniya za a ga koyaushe mutane suna da hanyoyin koyar da 'ya'yansu hankali, tsinkaya da basira, jurewa, hakuri, azanci da dabara da dai sauran halayen da za su taimake su lokacin da suka fara ma'amalar zaman duniya.

Daya daga cikin hanyoyin nan yakan kasance iya amfani da harshe wajen magana. Daga nan sai labarai na gaske da na almara, zaurance, karin magana, azancin tatsuniya, habaici, wa'azu, waka, cita-cita da sauransu.

Harshen Hausa ko kadan bai gaza wajen wadannan ba; haka kuma wajen labaran ban dariya, azanci, tausayi, wayo da dabara.

Ganin abubban nan sun fara bacewa a kasar nan, da kuma ganin rashinsu zai tauye mana wata daraja nan gaba balle ga ba da ilimi kyauta ga 'ya'yanmu ya zo, na duaki nauyin rubuta wadannan dan littafi da fatan taimakawa a wannan siffa. Kuma ina kara fata da addu'a cewa zai zama kafin alkalami ne ga sauran marubuta.

Mai karatu zai ga na debo abubba daga sassa; har da labarai na gaskiya bayan na almara saboda manufa dai ita ce kaifafa zukatun yara don kafin su girma su sami wukar gindi maganin aron ta wani. Allah ya yi mana muwafaka.

Daga karshe ina so in mika godiyata ga 'yan Komitin Inganta Hausa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano musamman ma Marafan Sakkwato Alhaji Ahmadu da Dr. Dandatti Abdulkadir, Dr. Kabir Galadanci, da Alhaji Abdulmalik Mani da Alhaji Usman Mairiga, da Alhaji Abdullahi Khalil, da M. Ibrahim Yaro Yahaya wadanda suka karfafa mini gwiwa a taron da muka yi a Sakkwato cikin watan Oktoba 1976 kan wallafar wannan littafi don tarbiyyar yaranmu da inganta hikimomin Hausa.

 

Aminu Kano.

Kano, 21st January, 1977

DAUKAR FANSA na Nasir Ibrahim Umar



A yadda ta ce, wai dole ne ta dauki fansar iyayenta, ko da kuwa yin hakan na iya zama sanadin salwantar rayuwarta.
Sai dai kuma, ta furta hakan ne tun sa'ar da take zaune a kasar Labanon kafin ta sauka a kasar haihuwarta. wanda nan ne tushen faruwar al'amarin.
Watanni uku da zuwanta, sai abubuwa suke sauya a wajenta, domin kuwa tana nema ta kashe, ana nema a kashe ta.

Sunday, July 26, 2020

SANIN MAKAMAR FASSARA na Salisu Ahmad Yakasai




"SANIN MAKAMAR FASSARA"

Sabon littafi ne da yake dauke da bayanai da darussa dangane da Fassara A Hausa. Littafi ne da Farfesa a harshen Hausa, kuma gwani a fannin Fassara ya wallafa. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai qwararre ne sosai a fannin fassara kuma ya baje-kolin qwarewarsa ta tsawon shekaru a fannin fassara a cikin wannan littafin nasa. Ina masu son "Sanin Makamar Fassara" a Hausa, za a iya tuntubar Alfarah for Hausa Translation, reshen "Alfarah Educational Enterprise" a kan wannan lambar: 09081606066, a kan farashin naira 2,200.

Allah Ya yi jagora, amin!

Daga shafin Muhammad Sulaiman Abdullahi

Monday, July 20, 2020

NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM -Daga Rahma Abdulmajid





NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM

 

Rahma Abdulmajid

 

Bismillahirrahmanirraheem. Assalaatu Ala RasulilKareem.

 Kalmomin "Story By", "Screenplay By" "Written By" kalmomi ne da mai biye da jawabin godiya na kammala fim kan hadu da su, kuma su rikita shi, saboda tunanin kowa a karon farko akan fim shi ne; mai labari fa shi ne marubucin labari da tsara shi. Amma kuma ga shi a nan an karkasa aikin wa mutane da yawa, shin me hakan ke nufi? Haka ma da yawa marubuta ko masu dauke da labari a zuciya kan ji cewa ai da zaran ina da labari to fa ni marubuci ne har kuwa rubutun fim!

Muddin ba a samar da hanyar fallasa wannan tunani da wartsakar da shi ba, to zai yi wuya mutane su san abin da ke kunshe a wannan littafi da muke kaddamarwa na rubutun fim a yau, domin da zaran mutum yana da labari ji yake ya zama marubuci, in ko ya zama marubuci ai baya bukatar irin wannan littafin don koyon dabarun zama marubuci.

Don haka me ake nufi da Labari? Me ake nufi da rubutun fim? Sannan wace alaka ce tsakaninsu?

 

LABARI shi ne wani bayani da za a bai wa mai saurare ya saurara ko ya karanta, amma ba shi da damar ganin sa sai dai zuciyarsa ta sauwara masa labarin da jarumansa.

 

LABARIN FIM kuwa shi ne tsararren hoton labarin da aka hutasshe da zuciyar mai sauraro da kallo daga sauwara wa kansa ta hanyar nuna masa shi akan idonsa da taimakon allon kallo.

 

Koda yake za a iya ji ana amfani da kalmar labari da nufin rubutun fim, sai dai kalmar "Labari" ko "Story" a fannin rubutun film ta sha bambam da kalmar labari da mutane suka fi sani.

 

A cewar Patrick Cattrysse: Kalmar Labari a fannin fim tana nufin wasu sadarori hudu ko biyar da ke bayar da labarin jarumin da kalubalensa cike da amfani da hanyoyin da za su ja hankalin masu zuba jari a labari ba masu zallar sauraro ba, Nasarar wannan salon labarin shi ne ya karbu a wajen masu hannu da tsaki don ya zamo "Screenplay" har ya iso matakin hoto mai motsi.

 

Mahadar abubuwan biyu kuwa a bayyane take a salon ba ni gishiri-in ba-ka manda tsakanin labari da rubutun fim, domin a yayin da labarin ke zama jari ko uwar kudin "Screenplay", Shi kuma "Screenplay" shi ne ribar wannan uwar kudi wato labari.

 

Daraja daya Labari ke iya nuna wa "Screenplay" a wannan dangantaka shi ne: A kowane "Screenplay" akwai labari, amma ba a kowane labari ne akwai "Screenplay" ba ko kuma a wani salon mu ce gundarin labari ne ke haifar da tsararren labarin film.

 

Hakan na nufin duka abubuwan biyu na bukatar marubuci ne ya rubuta su, amma kuma abin mamakin shi ne hakan baya nufin kowane marubucin labari ne marubucin fim, sai dai a ce ya fi yi wa marubucin labari saukin zama marubucin fim fiye da farar hula a harkar.

 

Dalilai fiye da daya sun zamo sanadiyyar hakan cikinsu akwai:

1. Rubutun Fim, labari ne da ake shirya shi bisa ka'idoji tsaurara da ba su da jimirin bai wa marubuci uziri kamar wanda sauran labarai ke ba shi.

 

2. Labarin Fim tun daga samansa zuwa kasansa kasuwanci ne da ke bukatar kwarewa maimakon zallar kirkira da tunani don a mafi yawan lokuta yana dauke ne da jarin wanin marubuci ba marubucin kai tsaye ba.

 

3. Samar da Idea ba ta tattare da wata asara ko kuma uwar kudi, domin aikin kwanya mai tunani ne, ita kuma kwanya mai tunani tana kasancewa ne cikin aikinta na tunani yana so ko ba ya so, da riba ko hasara, amma inda gizo ke sakar, shi ne wannan Idea din na iya zame masa babban jari idan ya iya sarrafa shi ta hanyar rubuta labarin Fim.

 

Wani producer ya taba samun wani marubuci yana bayar da wani labari da na kirkira, ka da bakinsa sai ya ce "kana ta bayar da labari idan aka sace maka fa?" Marubucin ya yi dariya na amsa masa "Sai na kirkiro wani, wannan ne ya sanya ake kira na storyteller, saboda a duk inda nake ya kamata na iya samar da sinima ga abokan hirata ko da babu majigi. Amma idan na mai da shi Script to ya tashi daga Story ya zama jari har ya hau kan takarda, a nan ne ba zan bari kowa ya saci jari na ba"

Don haka Labari shi ne uwar kudi amma ba shi ne jari ba, iya mayar da labarin jari shi ne jari, shi kuma iya mai da labari jari ana yin sa ne bisa kwarewa da bin matakan ilminsa wanda su aka tattara a wannan littafin da muka taru don karramawa Da fatan duk wanda ke wurin nan zai yi kokari ya mallaki wannan dabara.

Assalamu alaikum


an karanta wannan rubutu a ranar da aka gabatar da littafin Rubutun Fim na Bala Anas Babinlata

Sunday, July 19, 2020

KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA A SAUKAKE -Na Nasiru G. Ahmad 'Yan'awaki




ABUBUWAN DA SUKE CIKI

 

Gabatarwar Mawallafi                      1

Qa’idojin Rubutun Hausa                        4

Baqaqe da Wasulan Hausa              4

Qa’idojin Raba Kalmomi                 11

Hukunce-hukuncen “Wa”                        18   

Wasu Kalmomi Masu Rikitarwa      19

Hukunce-hukuncen Wasalin “a”      23

Gutsirarren Aikatau Xaurarre          24

Kalmomin Sharaxi                           25

Qarfafawa                                                26

Hausar Shiyya                                 26

Alamomin Rubutu                           28

QA’IDOJIN RUBUTUN HAUSA

 

Ma’anar Qa’idojin Rubutu

          Qa’idojin rubutu, wasu dokoki ne da aka yi ittifaqin yin amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa. Ita kuwa daidaitacciyar Hausa, xaya daga cikin kare-karen harshen Hausa ce da aka zava, aka daidaita mata qa’idojin nahawu, don yin amfani da ita cikin rubuce-rubuce da harkokin yaxa labarai a dukkan qasashen Hausa da sauran duniya baki xaya.

 

Baqaqe da Wasulan Hausa

          Jimillar baqaqen da ake amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa, su Talatin da biyu (32) ne. Ashirin da huxu (24) daga cikinsu sauqaqa ne, Takwas (8) kuma masu goyo. Akwai kuma wasula goma sha biyu (12).

 

Sauqaqan Baqaqe

Manya:

B, V, C, D, X, F, G, H, J, K, Q, L, M, N, R (ta cikin biyar), R (ta cikin ruwa), S, SH, T, TS, W, Y, Z, ‘(alhamza).

 

 

Qanana:

b, v, c, d, x, f, g, h, j, k, q, l, m, n, r (ta cikin biyar), r (ta cikin ruwa), s, sh, t, ts, w, y, z, ‘ (alhamza).

 

Masu Goyo

Manya: FY, GW, GY, KW, KY, QW, QY, ‘Y,

Qanana: fy, gw, gy, kw, ky, qw, qy, ‘y

 

Wasula

Gajeru      Manya:       A, I, O, U, E,

Qanana:      a, i, o, u, e

 

Dogaye     Manya:       AA,II, OO, UU, EE,

Qanana:      aa, ii, oo, uu, ee

 

Masu aure:                 auren /a/ da /i/ = /ai/

auren /a/ da /u/ = /au/

 

Akwai kuma auren /u/ da /i/ kamar a kalmar a:

          Ya yi targaxe a guiwa.

          Ya kiwata xan kuikuyo.

          mui gaba (mu yi gaba)

 

          Kamar yadda muka sani, an samo wannan salon rubutu ne daga rubutun Rumawa wanda Turawa suka kawo mana. To daga cikin ainihin baqaqen abacadan Turanci akwai wasu baqaqe huxu da ba a amfani da su a Hausa, saboda ba mu da irin sautukansu. Baqaqen su ne: /p/, /q/, /v/ da /x/. Furucin kowannensu na da takwara a bakin Bahaushe da yake amfani da shi a madadinsa. Maimakon /p/ ana amfani da /f/ ne. /q/ a madadin /q/, /b/ a madadin /v/, sai /s/ a madadin /x/.

          Duk da haka, akan rubuta /p/ a wasu sunayen yanka da ba ainihin na Hausa ba ne, kamar Pakistan, Potiskum, Pankshin, da makamantansu.

          Babu sautin /ch/ a Hausa, sai dai /c/. Shi ma akan bar wasu sunaye, musamman na garuruwa waxanda Turawa suka rubuta imla’insu a hakan da /ch/. Kamar Bauchi, Bichi, Chiranchi, dm.

          Ba a nuna dogon wasali ta hanyar ruvanya shi a rubutun Hausa na yau da kullum, kamar a ce /zoomoo/, sai dai /zomo/. Don haka kuskure ne rubuta wasu sunaye irin su Sameera, Haleema, Ameen, dm. haka ma qara baqin /h/ da wasu kan yi a wasu sunaye, musamman na mata kamar Aminah, Samirah, dm. Hasali ma ba imla’in rubutun Hausa ba ne, na Turanci ne.

          Yayin ruvanya baqaqe masu goyo, ana ruvanya baqin farko ne kaxai, ba duka biyun ba. Misali:

Gwaggwaro     ba      gwagwgwaro       ba

Kyakkyawa     ba      kyakykyawa         ba

Fyaffyaxe       ba      fyafyfyaxe           ba

 

Haka ma

Shasshaka       ba      shashshaka                     ba

Matsattsaku    ba      matsatstsaku        ba

Domin karanta littafin nan duka maza garzaya Kasuwar Sabongari, Gimbiya Bookshop, ko a tuntubi wannan lambar 07030319787

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...