Tuesday, June 9, 2020

YADDA TARON KADDAMAR DA LITTAFIN RUBUTUN FIM YA WAKANA



YADDA TARON KADDAMAR DA LITTAFIN RUBUTUN FIM YA WAKANA

Kabiru Yusuf  Fagge

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya da yabo ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).

Taron wanda aka gabatar da shi a ranar Litinin 8-6-2020, a yanar gizo (online), mahalarta sun fara halartar taron tun karfe 8:59 lokacin da marubucin Malam Bala Anas ya bude wajen taron, har zuwa bayan karfe goma sha daya, lokacin da Bala Anas Babinlata ya mika ragamar taron ga Malam Ahmad Alkanawy wanda shi ne ya jagoranci taron a matsayin MC.

Manyan mahalarta taron irin su Hamisu Iyantama, tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano, Malam Khalid Musa, Ahmad Mohammad Sarari, Ahmad Amaryawa, Ado Ahmad Gidan Dabino MON da sauransu suka fara tofa albarkacin bakinsu na wannan hobbasa da Bala Anas ya yi.
Daga bisani an saurari takardar sharhin littafin daga bakin marubuci, kuma malami a jami'a Farfesa Yusuf Adamu ta hannun Sadiq Gwarzo, sannan sai Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya gabatar da ta shi takardar mai taken GUDUMMAWAR MARUBUTA A SHIRIN FIM A TAKAICE, sannan Rahma Abdulmajid ta gabatar da tata takardar wadda ke fashin bakin kalmomin
story by, screenplay by written by, da yadda marubuci yake.

 Bayan kammala takardu, an gabatar da mai kaddamar da littafi, wato Malam Isma'il Na'abba Afakallah, wanda ya yi sharhi da jawabi, sannan ya kaddamar da littafin, inda ya siyi nasa, sannan ya siya a madadin hukumar Tace Finafinai, wato Kano Censor Board.

Daga nan aka bude damar kaddamar da littafi ga kowa da kowa, inda aka samu mutane da dama suka rinka siya, har zuwa lokacin da aka tashi daga taron wato bayan karfe daya da rabi.

Kafin rufe taron marubucin Bala Anas Babinlata ya gabatar da na shi jawabin mai taken Kasuwancin Zamani Na Littattafai da Finafinan Hausa.

Amma da yake abu ne online, kuma kofa a bude take, an cigaba da siyen littafin har zuwa yanzu kowa yana da damar mallakar littafin.

Masha Allahu

 

(a biyo ni domin karanta takardun da aka gabatar da kuma wadanda suka halarci taron)

Kabiru Yusuf Fagge

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...