MARUBUTA 10 SUN KARBI MAKUDAN KUDADE
A sakamakon lashe gasa ta gajeren labari da dandalin MARUBUTA WHATSAPP GROUP ya sa, karkashin filin Rubutunka Kamanninka, marubuta 10 sun sami nasarar lashe gasar, wanda kowannensu ya lashe makudan kudade a matsayin kyauta ta musamman naa gasar.
Gasar wadda tarin marubuta daga ciki da wajen kasar Nijeriya suka shiga, an tace tare da rerayewa daga alkalan gasar, inda suka zabo marubuta goma da suka lashe gasar.
Ba a ware wani takamaiman jigo da aka yi rubutun a kansa ba. Alkalan gasar sun duba dukkanin wasu ka'idoji da aka shimfida ga masu sha'awar shiga gasar, kamar kyakkyawan jigo, salo, tsari, yanayin gurabe a labari, ka'idojin rubutu da sauran abubuwan da suka dace ga mai shiga gasar gajeren labari.
Ba wannan ba ne karo na farko da mahukunta wannan zaure ke sanya gasar gajerun labaru don habaka tare da inganta rubuce-rubucen Hausa ba, a wannan karon sun so gabatar da gagarumin taro domin mika wadannan kyautuka ga marubutan, amma saboda yanayin da ake ciki na annobar Corona Virus, sun gabatar da kyautukan ta hanyar online, tare da aika satifiket da kyautukan kudaden ga asusun gwarazan gasar.
MARUBUTA 10 DA SUKA LASHE GASAR SU NE:
1. Hamza Dawaki (Dan Almajiri)
2. Bukar Mustapha (Bakar Talata)
3. Kamalar Muhammad Lawal (Wa Zan Hukunta?)
4. Jazuli Ya'u Hashim (Me Ke Faruwa?)
5. Asma'u Abdullahi Abraham (Sanadi)
6. Hassana Sulaiman Isma'il (Diya Mace)
7. Ummyn Yusrah (Burina)
8. Dalhat Suraj Mai Sharifiya (Kwadayi Mabudin Wahala)
9. Muhammad Bala Garba (Labarin Fauziyya)
10. Bilkisu Muhammad (Gani Ga Wane)
(wannan jadawalin baya nuna wane ne na 1 ko na 2 ko na 3, an jera ne kawai)
Allah ya kara basira.
Domin karin bayanin yadda gasar ta gudana za a iya lekawa MARUBUTA TV da ke kan Youtube, tare da sauran shirye-shiryen marubuta da ke gudana a wannan katafaren zaure.
-Kabiru Yusuf Fagge
No comments:
Post a Comment