Friday, June 26, 2020

BAKAR ANIYA




BAKAR ANIYA
Na Aminu Ladan Abubakar (Ala)
2002
(tsohuwar taskar)

Kakkarfar iska mai sanyi ta cigaba da kadawa hade da kugin ruwa da ke gudana ta karkashin gadar, karfin kadawar iskar dake kokarin fisgar mayafin dake jikinta, shi ya bai wa doguwar rigar dake jikinta damar kadawa tamkar tuta.

Wadansu zafafan hawaye, suka cigaba da sintiri wasu na bin wasu suna disa bisa jaririn dake tallabe a hannunta. wanda lokaci zuwa lokaci cikin wutsilniya yakan canyara kuka a lokaci guda kuma sai ka ga ya sanya hannunsa a baki yana tsotsa.

Wani lokaci kuma a garin wautsilniyarsa har yakan yakushi fuskarsa da faratansa a lokacin ne to za ka ji sautin kukansa ya yi amsa kuwwa a sararin wannan bigire da ake kokarin yi masa muhalli a gurin.

A lokacin da ta doshi karkashin gadar zuciyarta ta yi bakikkirin ta duhunta ganinta, kugi da ambaliyar da ruwan ya rika yi, yana marin juna, shi ya haifar da juwa a tare da ita sai ta rinka jin tamkar fizgarta ake yi izuwa cikin wannan ruwa. Sannu a hankali tana bin gefen ruwan ba ta ankara ba kafarta ta zame...
-Aminu Ala

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...