BITA TA MUSAMMAN DOMIN MARUBUTA
Kasancewar yanzu lokaci ne na gasa da ake ta kokarin shiga,muna shiga gasa,muna da basira mun iya samo jigo mai kyau,mun iya kokarin bin duk wasu dokokin gasa,amma abu daya yasa da yawa muke faduwa tun a matakin farko,meye wannan abin? rashin sanin tsari da salon rubutun shiga gasar gajeren labari,wannan yasa manhajar Bakandamiya ta samar mana da bita ta musamman domin marubuta da kuma makaranta harma da manazarta.
Munada abubuwa da yawa da zamu gabatar wanda kuma duk akan Marubuta zamu yi shi,akwai gasa ma da akayi a baya,kuma har an shirya wata za ayi sai mukayi tunanin mu fara nunawa mutane dabarun yanda ake rubuta gajeren labari na shiga gasa,wanda Malam Danladi Haruna zai gabatar mana a manhajar nan
Zamu iya sauke wannan manjar kai tsaye acan za a gabatar da wannan bita.
Za a fara bita: ranar 15-20 june 2020
lokaci: 4:30 pm a (kullum agogon Nigeria)
Guri bita: Taskar Bakandamiya (zauren MARUBUTA)
Don meman karin bayani
08037442582
08030764060
Mun gode kwarai.
No comments:
Post a Comment