Wednesday, June 24, 2020

SIYAMA na Yakub M. Kumo




SIYAMA
Sirrin afkawar al'amuransa cikin laulayi ya samo asali ne, sakamakon zazzafan zazzabin soyayya mai tsannain karfi da ya sarkafe zuciyarsa. Ko da tarin hannu-da-shuni da ya mallaka ba su zama katangar shiga tsakaninsa da Siyasama ba shu'umar matarsa mai matukar girman kai da ta dauki duniya a matsayin gidan-kashe-ahu, ba za ta taba barin macen da ba ta iya daurin kallabi ta zama kishiya gareta ba.

Shakka ta lullube zuciyarsa yayin da ya yi zaman farko da mahaifinta wanda miskilancinsa ya fifita a kan na mislika, duk da hakuri, juriya da kuma kasancewar sa ma'abocin riko da sunnah kamar Maimunatu sai da ya yi masa jagora ga hajijiya.
Zaman gida ya gagare shi, ya kuma gabatar da abubuwan al'ajab, amma duk da haka iya ruwansa bai kai shi ga kubuta ga siradin da ke gabansa ba.
Dankari, daga karshe ministan gidajen da ayyuka ya shiga rudanin da ya jefa duniyarsa ga hatsabibiyar rayuwa.
Sharhi daga Maje ElHajeej Hotoro
Siyama na Yakub Moddibo Kumo

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...