` A DALILIN SON KAI
(LABARIN ZAHARA’U)
Daga
IBRAHIM BIRNIWA
BABI NA XAYA
Zahara’u ta daxe tana jin ana cewa
Haxejiya Ginsau Birnin Doki, amma bata tava zuwa. Haxejiya ba sai yau tun da ta
sauka a mota take ta waige-waige don ta tabbatar da Haxejiya ta dace da yadda
take jin labarinta a bakin mutane musamman qawarta Maryam da ta zo bikin
baikonta a yau wannan rana ta Asabar.
Haxejiya ba ta yi qasa a gwiwa ba wajen gamsar da zuciyar Zahara’u cewa ta isa a bada labarin ta a ko’ina.
Zahara’u ta samu Haxejiya fiye da yadda
ta zata, babu wani abu da ta rasa, yawan jama’a ma’aikatu, cunkoson ababen
hawa, kasuwanci, karatu da sauransu. Ba ta ce Haxejiya ta kai Kano ba inda ta
baro, amma dai itama ta isa ta shiga cikin biranen qasar nan da idan an tashi
ambata za a abato.
Daga sabuwar tasha inda ta sauka a mota sai ta kira mai babur domin ya kaita
zuwa ga kwatancen da aka yi mata kamar yadda Maryam tace ta yi idan ta zo.
Galadima Sinima. Zahara’u tace da mai
mashin xin ‘Ka san wurin?’
‘Eh na sani.’ Xan acavan yace.
‘To kusa da wurin ne gidan da zan je,
saboda haka idan mun je sinimar zamu tambaya, don ni ban sani ba ka ga ni
baquwa ce.’
“Eh, amma ba damuwa ai, wataqilama zan
san inda ki ke tambaya xin.”
‘Yauwa, to ka san wata makarantar firamare
akusada sinima xin?’ Zahara’u ta tambaya.
‘Eh, na sani.’
‘Yauwa, to daga makarantar an ce ko
qaramin yaro aka tambaya gidan Malam Maktari Ali ya sani.’
‘Na sani nima ai.’
‘A’a don Allah fa?’ Zahara’u ta tambaya
tana murmushi.
‘Wallahi na sani.’ Xan acava ya ce, yana
murmushi shima.
‘Kai amma ta kwana gidan sauqi.’
Zahara’u ta ce, sannan ta xauki jakar ta ta miqa masa ‘ungo to riqe wannan a
gabanka.’ Ta xauqi xaya qaramar jakar ‘ni kuma bari na riqe wannan a hannu na
to amma fa sai ka karkato yanda zan iya hawa.’
‘To ina zuwa.’ Xan acava ya ce, sannan
ya ajiye jakar da ya karva, ya karkata mashin xin ta hau, kana ya xauki jakar
ya xora a gabansa ya ja mashin xin suka tafi.
A qofar gidan ya ajiye ta ‘Wannan shi ne
gidan Malam Muktari.’
‘Ok, amma naji daxi wallahi, ka ce kai
ko ina ka sani?’
‘A’a haba, ba dai ko ina ba, ai ni
layinmu yana nan baya shi ya sa.’
‘Ok.
To nawa ne kuxin ka?’ Zahara’u ta tambaya.
‘Naira ashirin ne.’
‘Ashirin?’ Ta ciro hamsin daga cikin
jakarta ta miqa masa. Ya karva, sannan ya fara laluben canji.
Zahara’u ta fahimta ‘A’a ka riqe duka,
na gode.’
‘Na gode nima.’ Xan acavar ya ce ‘Sai an
jima.’
Ya juya mashin xin domin komawa, ita
kuma ta dauki jakarta ta shige cikin gidan.
An haifi Zahara’u a Hausawa Sabon titi a
Kano. Mahaifinta kafin ya rasu qaramin xan kasuwa ne, yana da shagon siyar da
kayan P.Z anan kan Sabon titin Hausawa xin. Abin da ya fi dagewa a kansa kafin
ya mutu bai yi qasa a gwiiwa ba wajen xaukar nauyin karatun Zahara’u da sauran
qannenta. Ranar da ya mutu, Zahara’u da qannenta sun sha kuka kamar yadda
mutane suka saba yi idan mahaifinsu ya rasu.
Zahara’u ita ce babba a cikin ‘ya’ya
bakwai da babansu ya mutu ya bari.biye da ita Aisha ce, sai kuma Abubakar sai
Rabi’u da Saratu da Sa’adatu da kuma xan autansu Abdul-Azeez.
Zahara’u zata iya kasan cewa ko ina
tsakanin shekaru ashirin da biyu zuwa da uku.
Bayan kwanaki arba’in da rasuwar
mahaifinsu, sai suka bude shagon Abubakar ya shiga aka ci gaba da gudanar da
kasuwanci. Ribar da ake samu a shagon ce ta zama cinsu da shansu da sutturarsu
da kuma kuxin makaran tarsu. Kasancewar Abubakar yaro mai hankali ya sa
al’amura sun zomusu da sauqi, saboda Abubakar ya maida hankalinsa wajen
tabbatar da bai bari wani cikas ya samu shagon ba. Komai ya siyar sai ya
tattara ya sake sayo wani, ribar ya tattara ya kaiwa Mahaifiyarsu.
Mahaifiyarsu
Hauwa’u mace ce jaruma, ta tsaya tsayi daka wajen ganin rashin mahaifibai
tarwatsa tarbiyyar ‘ya’yanta ba. Ta dage wajen tanqwaro kan manyan, su Zahara’u
da Abubakar da Aisha, yayin da su kuma suke ta gazawa wajen tanqwaro mata kan
qananan har zama saiti a gidan.
Saboda yadda rayuwa take bunqasa kuma ababen
buqata kullumsuna qara tsada ga kuma kuxaxen makaranta kullum suna yin sama,
sai ya zaman shagon ya fara gazawa wajen xaukar xawainiyar su, yana buqatar
wani abu da zasu haxa qarfi da shi su tarairayi bayan Malam Nasiru Hausawa.
Ganin haka sai Hauwa’u ta ga ya kamata
suyi wani abu, ta kuma qudire a ranta ga abinda ya dace su yi, saboda haka ta
kira manyan ‘ya’yanta domin suyi shawara.
‘Ina son ku san cewa yanzu al’amura sun canza kuma kullum suna daxa
canjawa, ya bayyana qarara a garemu shagon nan ba zai iya riqemu ba. Muna
buqatar qarawa da wani abin.’ Hauwa’u ta ce da yaranta.
‘Gaskiya ne.’ Suka ce gaba xayansu.
‘Yauwa.’ Hauwa’u ta ci gaba ‘To na kira
ku ne don mu shawarta ni da ku mu ga me ya kamata a yi, saboda haka me ku ke
gani za a yi?’
Yaran suka xan yi shiru, wannan ya dubi
wannan, wancan ya dubi wannan. Sannan sai Zahara’u ta ce ‘Ni ina ganin a qara bunqasa
shagon ya zama ya yi girma, kun ga zai ke kawo riba mai tsoka, wanda yawanta
zai iya riqemu.’
‘Haka ne.’ Hauwa’u ta ce ‘To amma ta ya
ya za a yi a bunkasa shagon, don wannan abu ne da ke buqatar kuxi, ba kuma sai
na faxa muku cewa bamu da kuxi ba.’
‘To a ranta mana tunda dai sana’a za a yi.’
Aisha ta ce ‘Idan ya so daga baya ma biya.’
‘Kai, a’a.’ Abubakar ya ce ‘Ka da mu
bari kuxin rance ya shiga cikin kasuwancinmu.’
‘Gaskiya ne.’ Zahara’u ta ce ‘Kuma ma
idan munyi rance mun bunqasa shago, da ciyar da kanmu zamu ji ko kuma da tara
kuxin biyan bashi. Gara duk abin da za
mu yi ya kasance da abin da yake mallakinmu zamu yi.’
‘To yanzu tunda dai bunqasa shagon shine
mafita,to ya za mu yi mu bunqasa shi? Aisha ta ce ‘Ina nufin me ake ganin za a
yi a samo kuxin da za a bunqasa shagon da su?’
Aka xan qara yin shir, sannan Abubakar
ya yi magana.
‘Ni ina ganin tunda yake gidan namu bene
ne, mu bada hayar sama mu zauna qasa dukanmu. Kuxin da za a bamu na hayar ina
ganin ya ishemu mu bunqasa shagon sashi. Kuma duk shekara daga mun karvi kuxin
sai mu riqa qara shagon dashi ko kuwa me kuka gani?’
‘Gaskiya haka ne.’ Zahara’u ta ce
‘Wannan ita ce dabara.’
‘Gaskiya kam.’ Aisha ta ce ‘Nima na goyi
da bayan wannan dabara.’
‘Ni ban goya ba.’ Hauwa’u ta ce. “Ba zan
so ba mu maida gidanmu gidan haya, ya zamana bamu da wani sirri ko kuma wata
cikakkiyar sakewa a cikin gidanmu. Ya zamana ‘ya’yana su cukuxu da ‘ya’yan
waxanda za su zo su zauna alhali ni ban san irin tarbiyyarsu ba. Sannan kuma ya
kasance mu duka mun zo mun tarumun matsu a qasan nan.” Ta girgiza kai, “Ban
yarda da haka ba.”
“To ai laluri ne Umma.” A’isha ta ce.
“A’a.” Umma Hauwa ta ce, “Abin bai kai
ga zama haka ba tukunna.”
“To Yanzu ya ya za’ayi?” Abubakar ya
tambaya.
“Ni da ina da wata shawara a raina.”
Umma Hauwa ta ce.
“To faxa mana.” Zahra’u ta ce.
“Yauwa.” Umma Hauwa ta ce “Kun ga gidan
nan namu ya na kusa da bakin titi, kuma wuri ne na jama’a. Me zai hana to kama
sana’ar abincin sayarwa, mutane suan zuwa suna saya. Kun ga cikinabincin da
nake dafawa sai mu ci ribar abincin kuma da kuma ribar da za ta ke zuwa mana
daga shago in sha Allahu sun isa su tallafemu.”
Yaran suka xan yi shiru, suna dubana
juna, suna tunani, sannan Zahra’u ta yi magana, bayan ta yi nazarin komai a
ranta.
“Wannan shawarar ta yi, ni a ganina, sai
dai kuma shi kan sayin abincin yana
buqatar kuxi ne. A ita zamu samu kuxin da za su zama jarin abincin?”
“Kayayyaki na zan fidda in sayar mu yi
jari da kuxin.” Umma Hauwa ta ce.
“Kai Umma.” A’isha ta ce, “Kya sayar da
kayayyakin ki kuwa?”
“gaskiya Umma gara a yi wani tunanin,
bai kamata ki sayar da komai naki ba.” Abubakar ya ce.
“Babu komai.” Umma Hauwa ta ce, “Idan
Allah ya taimake mu komai ya yi yadda muke so, ai sai na sayi duk abin da na
sayar xin harma na sayi wani abin da da bani dashi.”
A qarshe, lokacin da aka kawo qarshen tattauanwar,
kowa ya amince da shawarar Umma Hauwa.
Sati xaya bayan haka Umma Hauwa ta fara
dafa abincin sayarwa. Shinkafa da miya da nama daga safe har rana. Allah ya
taimaka Umma Hauwa gwana ce wajen iya girki sai abinci samu karvuwa a wajen
jama’a. Mutane suka fara gano gidan suna zuwa suna maganin yunwa.
Ba a jima ba sai ya zamanto abincin da
Umma Hauwa ke dafawa ya yiwa mutanen da ke zuwa saye kaxan. Don wata rana ma
sai bayan abincin ya qare sai sama da rabin mutanen da suka sayi abincin su zo
nema babu. Ganin haka sai Umma Hauwa ta qara daga abin da take dafawa da, kuma
ya zamanto idan wanda ta dafa ya qare ana kuma ta zuwa nema sai ta xora tukunya
ta dafa wani.
Shekara ba ta zagayo ba sai da abincin
ya bunqasa-bunqasar da ba su yi tsammani ba, ya zama kullum Umma Hauwa ta xora
tukunya da safe, to ta yi ta dafa abincin ana sayewa kenan har dare. Falonsu na
qasa aka kwashe komai dake ciki, aka mayar da shi cikin gidan, nan kuma aka yi
mata bencina ta zuba ciki, mutane suka riqa zama a ciki suna sayen abincin suna
ci.
Zahra’u da A’isha suke taimaka mata, da
kuma wasu ‘yan mata guda biyu da ta xauka tana biyansu, saboda su Zahra’u suna
tafiya makaranta.
Abubakar kuma ya ci gaba da zama a
shago, sannu a hankali suka bunqasa shagon da kuxin da suke samu ta hanyar
sayar da abincin. Da haka suka ci gaba da fin qarfin buqatunsu na yau da
kullum, da haka ne kuma Zahra’u tayi karatunta na diploma a makarantar F.C.E.
ta gama ba tare da ta xora hannu aka ba.
Yanzu Hausawa Sabon Titi idan ana
maganar abinci, dole ne a ambato Umma Hauwa.
Zahra’u da Maryam sun haxu ne a
makarantar F.C.E. har suka zama qawaye. A shekara guda suka shiga makarantar
kuma kwas guda suke karanta. Haka kawai Allah ya haxa jininsu suka zama koda
yaushe tare. Komai na su tare suke yi, sun shaqu sosai irin shaquwar da idan
kana neman xaya ka haxu da xaya sai kawai ka ba ta saqo ka koma. Da yake Maryam
‘yar Haxejia ce karatu ne kawai ya kai ta Kano sai yazamana idan ka ganta ta
fito daga makaranta to tare da Zahra’u ne za su je gidansu Zahra’u. Sukan haxu
tare su taimaka wa Umma Hauwa a wajen girki, kusan kullum suka je gidan, har ya
kai Maryam ta zama tamkar itama xaya ce daga cikin ‘ya’yan da Malam Nasiru
Hausawa ya rasu ya bari.
Har su Zahra’u suka kama gama karatun su
shekaru biyu Zahra’u ba ta tava zuwa Haxejia ba, sai dai hotunan ta sun jejje,
kuma duk wani rayayye dake gidan su Maryam ya ji labarin Zahara’u a bakin
Maryam. A yanzu suna cikin watansu na huxu da kammalaka diplomarsu.
Wannan zuwa da Zahra’u ta yi Haxejia ta
zo ne domin halartar baikon Maryam (Engagement) Wanda za a yi ranar Talata,
tsakanin ita da masoyinta attajiri
Faruq. Takanas Maryam ta tashi qaninta, ta aike shi da wasiqa da kuma katin
baikon ta yi masa kyakkyawan kwatance, yakaiwa Zahra’u saqon har gida.
Umma Hauwa ba za ta iya hana Zahra’u
zuwa baikon Maryam ba.
Zahra’u ta aikowa Maryam ta tabbatar a
cikin wasiqar cewa za ta zo ranar Asabar 20 ga wata. Kwanaki uku kenan kafin
ranar fatin baikon, saboda haka da ta zo gidna dama ana jiran zuwanta.
An yi mata shimfixar fuska, kuma an yi
mata shimfixar tabarma.
Zahra’u ba kyakkyawa ce can ba, sai dai
tana da matuqar tsafta, ga ta gwana wajen iya kwalliya. Duk namijin da ya ganta
cikin kwalliya sai ya tuna shi namiji
ne. Tana daga cikin matan da Allah ya albarkace su da qirar jiki mai kyau. Duk
da yake ita ba fara ba ce, ko da yake ba zaka ce mata baqa ba, takaniya sace
zuciyoyin wazaje goma, kafin wata farar macen ta sace zuciyar mutum xaya. Allah
ya hore mata tattausar daddaxar murya, ya kuma yi ta qwararriya wajen iya
sarrafa kalamai a cikin magana. Gwana ce wajen iya tausa da lallashin wanda
ransa yavaci, kuma ta juce bai sani ba. Savanin uwarta ita ita ba jaruma ba ce,
koda yake ba za ka ce malalaciya ba ce, amma kuma ba za ka gantaba wajen aikin
wahalar da ya yawaita. Ta yarda da Hausawa da suka ce rai dangin goro ne hutu
yake so.
Yarinya ce mai tabbatar da ta samu duk wani abu da ya gani tana so. Mai son nuna ta san komai, ma’abociyar iya yi da gwalli da kisisina. Mai ilimi a makaranta mai son mutane, mai surutu mai haba-haba da jama’a.
Lallai labari ya yi ma,ana so said.
ReplyDeleteAllah ya kara hazaka