Monday, June 29, 2020

MUJALLAR "INUWAR MARUBUTA" (don cigaban marubuta)



INUWAR MARUBUTA (don cigaban marubuta)

(Fitowa Ta 2, Fabarairu 2005)

Tuna baya: Labarun shekaru 15 baya

Kudinta N50

LABARUN DA SUKE CIKI

-MARUBUTA ZA SU DAIDAITA SAHU?

Taron marubuta da hukumar A Daidaita Sahu, domin daidaita sahun fannin rubuce-rubuce

-BAN GOYI BAYAN RUBUTUN BATSA BA...- ZAINAB LAWAN BIRGET

Hira da marubuciya, Zainab Lawan Birget, inda ta nuna rashin goyon bayanta ga rubutun batsa.

 

A DALILIN SON KAI -1



` A DALILIN SON KAI

(LABARIN ZAHARA’U)

 

Daga

 

IBRAHIM BIRNIWA

birniwaalmout@yahoo.com


BABI NA XAYA

Zahara’u ta daxe tana jin ana cewa Haxejiya Ginsau Birnin Doki, amma bata tava zuwa. Haxejiya ba sai yau tun da ta sauka a mota take ta waige-waige don ta tabbatar da Haxejiya ta dace da yadda take jin labarinta a bakin mutane musamman qawarta Maryam da ta zo bikin baikonta a yau wannan rana ta Asabar.

Haxejiya ba ta yi qasa a gwiwa ba wajen gamsar da zuciyar Zahara’u cewa ta isa a bada labarin ta a ko’ina.

HAJIJIYA na IBRAHIM BIRNIWA


Friday, June 26, 2020

BAKAR ANIYA




BAKAR ANIYA
Na Aminu Ladan Abubakar (Ala)
2002
(tsohuwar taskar)

Kakkarfar iska mai sanyi ta cigaba da kadawa hade da kugin ruwa da ke gudana ta karkashin gadar, karfin kadawar iskar dake kokarin fisgar mayafin dake jikinta, shi ya bai wa doguwar rigar dake jikinta damar kadawa tamkar tuta.

Wadansu zafafan hawaye, suka cigaba da sintiri wasu na bin wasu suna disa bisa jaririn dake tallabe a hannunta. wanda lokaci zuwa lokaci cikin wutsilniya yakan canyara kuka a lokaci guda kuma sai ka ga ya sanya hannunsa a baki yana tsotsa.

Wani lokaci kuma a garin wautsilniyarsa har yakan yakushi fuskarsa da faratansa a lokacin ne to za ka ji sautin kukansa ya yi amsa kuwwa a sararin wannan bigire da ake kokarin yi masa muhalli a gurin.

A lokacin da ta doshi karkashin gadar zuciyarta ta yi bakikkirin ta duhunta ganinta, kugi da ambaliyar da ruwan ya rika yi, yana marin juna, shi ya haifar da juwa a tare da ita sai ta rinka jin tamkar fizgarta ake yi izuwa cikin wannan ruwa. Sannu a hankali tana bin gefen ruwan ba ta ankara ba kafarta ta zame...
-Aminu Ala

Wednesday, June 24, 2020

SIYAMA na Yakub M. Kumo




SIYAMA
Sirrin afkawar al'amuransa cikin laulayi ya samo asali ne, sakamakon zazzafan zazzabin soyayya mai tsannain karfi da ya sarkafe zuciyarsa. Ko da tarin hannu-da-shuni da ya mallaka ba su zama katangar shiga tsakaninsa da Siyasama ba shu'umar matarsa mai matukar girman kai da ta dauki duniya a matsayin gidan-kashe-ahu, ba za ta taba barin macen da ba ta iya daurin kallabi ta zama kishiya gareta ba.

Shakka ta lullube zuciyarsa yayin da ya yi zaman farko da mahaifinta wanda miskilancinsa ya fifita a kan na mislika, duk da hakuri, juriya da kuma kasancewar sa ma'abocin riko da sunnah kamar Maimunatu sai da ya yi masa jagora ga hajijiya.
Zaman gida ya gagare shi, ya kuma gabatar da abubuwan al'ajab, amma duk da haka iya ruwansa bai kai shi ga kubuta ga siradin da ke gabansa ba.
Dankari, daga karshe ministan gidajen da ayyuka ya shiga rudanin da ya jefa duniyarsa ga hatsabibiyar rayuwa.
Sharhi daga Maje ElHajeej Hotoro
Siyama na Yakub Moddibo Kumo

HANJI WAJE



(tsohuwar ajiya)
HANJI WAJE

"Soyayya mai wuyar fassara, mai matukar dadi, dauke da wasu al'amura masu wuyar ganewa. Wadannan abubuwa da muka lissafa mun hadu da su a shekaru goma da muka yi muna tare a matsayin masoya. Amma wasu abubuwa masu daukar hankali a wannan rayuwa tamu su ne; matukar shakuwa, sadaukarwa, taimako, tausayi, shawarta tare da matukar kara wa juna kwarin gwiwa a duk wasu abubuwa da muka sa a gaba. Wani abin ban sha'awa wajen wadanda suka san mu shi ne, yadda muke mutunta juna tare da matukar zolayar juna domin tsabar fahimtar juna."
-Marigayi Auwal Sa'ad.
Allah ya gafarta masa, amin summa amin.

Tuesday, June 9, 2020

MAHALARTA TARON RUBUTUN FIM





MAHALARTA TARO

Wadannan su ne wadanda suka samu halartar taron da aka yi na kaddamar da littafin Rubutun Fim na Bala Anas Babinlata har zuwa lokacin da aka tashi daga taron, duk da wasu

Abba Rabiu

Abdulhadi Nasidi

Abdulrahman Aliyu

Abdulrahman S. Nuhu

Abdulrashid Surajo Dokau

Abubakar Lawan

Abubakar Musa Anka

Adam Abba Muhammad

Adam Hadi Ibrahim

Adamu Ibrahim Shira

Adamu Idris Tanko

Ado Abubakar Bala

Ado Ahmad Gidan Dabino

Ahmad Abubakar Amaryawa

Ahmad Alkanawy

Ahmad Habu Danbatta

Ahmad Mohammad Sarari

Ahmad Nagudu

Ahmad Rabi'u Gumel

Alawiyya Wada Isah

Aleeyu Yusup Gusau

Al-Hussein Burji

Ali Abubakar Sadiq

Ali Muhammad

Almustapha Adam Muhammad

Amina Hassan Abdulsalam

Aminu Alamezon Amarawa

Aminu Dauda Giwa

Aminu Ladan Abubakar

Aminu Malami

Aminu Mannir Ke'eza

Aminu Trader

Amir Murtala Adam

Ashiru Abubakar Turaki

Ashiru Idris Rahama

Auwal Kabir

Auwal Zubair

Ayuba M. Diskudo

Ayuba Muhammad Danzaki

Bala Anas Babinlata

Basheer Reader

Bashir Jika

Bashir Lawal

Binta Spikin

Bukar Mada

Comrd Anas Bala Jega

Danladi Haruna

Danladi Yahaya AK

Dayyabu Gambo

Deejah Sharubutu

El-Ameen Daurawa

Engr Kabiru janare Dorayi

Faisal Haruna Alhunqawee

Farfesa Yusuf Adamu

Faruq Sayyadi

Habibu Hudu Ahmad D

Hadiza Nuhu Gudaji

Hafiz Koza Adamu

Hamisu Iyantama

Haseenor Sani

Hassan Bello Salih

Hassan Ismail Kankarofi

Hassan M. ringim

Ibraheem Slaeh Abdulrahman

Ibrahim Garba Nayaya

Ibrahim Londonboy

Ibrahim mandawari

Ibrahim Moddibo

Ibrahim Muhammad Indabwa

Ibrahim Umar Ibi Muhammad

Idris Muhammad Inda Saminaka

Ishaq Daneji

Ishaq Kabiru

Ismail Afakallah

Isyaku Abubakar Musa Kawu

Jamil Musa Baraden Anka

Jamila Abdullahi R/Lemo

Jamilu Alhassan

Jamilu haruna Jibeka

Jamilu Musa Baraden Anka

Jibrin Yusuf Kaila

Kabiru Ghali AbbanSaudat

Kabiru S. Hannu Daya

Kabiru Yusuf Fagge

Kamal Muhammad Lawal

Kamal Y. Iyantama

Kamal Zango

Khadeejatul Heedyah

Khalid Musa

Laminou Gonda

Lawal S Zazzau

Luqman Ismail Funtua

Ma'axu Hassan

Mahmud Abba Yusuf

Maimuna Idris Sani Beli

Mallam Yusuf Hassan

Maman Teemerh

Mohammed Abba Korni

Mohammed Idris Kumo

Mohd Ami Nullah

Mua Danazimi Baba

Mubaraak Abubakar Sualawa

Muhad Adam Harun Aisami

Muhammad Akhee Sabo usman

Muhammad Lawal PRP

Muhammad Maude Yau

Muhammadu Bala GArba

Muhd MC King

Mukhtar Dauda Ismail

Mukhtar Kabugawa

Mustapha Abbas

Mustapha Aminu ADK

Mustapha Jafar

Muzammil Mandawari

Nasir Abdulhamid Kazaure

Nasir S. Gwangwazo

Nasir Sulaiman

Nasiru B. Muhammad

Nazir Adam Salih

Nura Abdullahi Ahmad

Nura Ado Gezawa

Nura Sharrif

Prince Ahmad Amoeva

Rabi'u Musa Ramaz

Rahma Abdulmajid

Rahma Ramalan Zaria Rrsz

Ramlatu Umar

Real Abulwarakat Ayagi

Real Fauziyya D. Sulaiman

Sa'adatu Baba Ahmad

Saddiq Sanam

Sadiq Gwarzo

Sadiq Tukur Gwarzo

Sadiya Garba

Sa'id Mustapha

Sani Ahmad Yahalatta

Sanin Inna Maskwani

Sarari Lawal Muhammad

Shehu S Bello

Shuaibu A Adamu

Shuaibu Tanko

Sulaiman Abubakar Yahaya

Sulaiman Usman Khalid

Umar Mahmud Dembo

Umaru Sheikh Mohammed

Wahabiyya Muhammad Shugaba

Zahraddeen Salisu Bako

Zubair M. Balannaji

Zubairu Abdulrahman Kassim


YADDA TARON KADDAMAR DA LITTAFIN RUBUTUN FIM YA WAKANA



YADDA TARON KADDAMAR DA LITTAFIN RUBUTUN FIM YA WAKANA

Kabiru Yusuf  Fagge

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya da yabo ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).

Taron wanda aka gabatar da shi a ranar Litinin 8-6-2020, a yanar gizo (online), mahalarta sun fara halartar taron tun karfe 8:59 lokacin da marubucin Malam Bala Anas ya bude wajen taron, har zuwa bayan karfe goma sha daya, lokacin da Bala Anas Babinlata ya mika ragamar taron ga Malam Ahmad Alkanawy wanda shi ne ya jagoranci taron a matsayin MC.

Manyan mahalarta taron irin su Hamisu Iyantama, tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano, Malam Khalid Musa, Ahmad Mohammad Sarari, Ahmad Amaryawa, Ado Ahmad Gidan Dabino MON da sauransu suka fara tofa albarkacin bakinsu na wannan hobbasa da Bala Anas ya yi.
Daga bisani an saurari takardar sharhin littafin daga bakin marubuci, kuma malami a jami'a Farfesa Yusuf Adamu ta hannun Sadiq Gwarzo, sannan sai Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya gabatar da ta shi takardar mai taken GUDUMMAWAR MARUBUTA A SHIRIN FIM A TAKAICE, sannan Rahma Abdulmajid ta gabatar da tata takardar wadda ke fashin bakin kalmomin
story by, screenplay by written by, da yadda marubuci yake.

 Bayan kammala takardu, an gabatar da mai kaddamar da littafi, wato Malam Isma'il Na'abba Afakallah, wanda ya yi sharhi da jawabi, sannan ya kaddamar da littafin, inda ya siyi nasa, sannan ya siya a madadin hukumar Tace Finafinai, wato Kano Censor Board.

Daga nan aka bude damar kaddamar da littafi ga kowa da kowa, inda aka samu mutane da dama suka rinka siya, har zuwa lokacin da aka tashi daga taron wato bayan karfe daya da rabi.

Kafin rufe taron marubucin Bala Anas Babinlata ya gabatar da na shi jawabin mai taken Kasuwancin Zamani Na Littattafai da Finafinan Hausa.

Amma da yake abu ne online, kuma kofa a bude take, an cigaba da siyen littafin har zuwa yanzu kowa yana da damar mallakar littafin.

Masha Allahu

 

(a biyo ni domin karanta takardun da aka gabatar da kuma wadanda suka halarci taron)

Kabiru Yusuf Fagge

Monday, June 8, 2020

MARUBUTA 10 SUN KARBI MAKUDAN KUDADE















MARUBUTA 10 SUN KARBI MAKUDAN KUDADE

A sakamakon lashe gasa ta gajeren labari da dandalin MARUBUTA WHATSAPP GROUP ya sa, karkashin filin Rubutunka Kamanninka, marubuta 10 sun sami nasarar lashe gasar, wanda kowannensu ya lashe makudan kudade a matsayin kyauta ta musamman naa gasar.

Gasar wadda tarin marubuta daga ciki da wajen kasar Nijeriya suka shiga, an tace tare da rerayewa daga alkalan gasar, inda suka zabo marubuta goma da suka lashe gasar.

Ba a ware wani takamaiman jigo da aka yi rubutun a kansa ba. Alkalan gasar sun duba dukkanin wasu ka'idoji da aka shimfida ga masu sha'awar shiga gasar, kamar kyakkyawan jigo, salo, tsari, yanayin gurabe a labari, ka'idojin rubutu da sauran abubuwan da suka dace ga mai shiga gasar gajeren labari.

Ba wannan ba ne karo na farko da mahukunta wannan zaure ke sanya gasar gajerun labaru don habaka tare da inganta rubuce-rubucen Hausa ba, a wannan karon sun so gabatar da gagarumin taro domin mika wadannan kyautuka ga marubutan, amma saboda yanayin da ake ciki na annobar Corona Virus, sun gabatar da kyautukan ta hanyar online, tare da aika satifiket da kyautukan kudaden ga asusun gwarazan gasar.

MARUBUTA 10  DA SUKA LASHE GASAR SU NE:

1. Hamza Dawaki (Dan Almajiri)

2. Bukar Mustapha (Bakar Talata)

3. Kamalar Muhammad Lawal (Wa Zan Hukunta?)

4. Jazuli Ya'u Hashim (Me Ke Faruwa?)

5. Asma'u Abdullahi Abraham (Sanadi)

6. Hassana Sulaiman Isma'il (Diya Mace)

7. Ummyn Yusrah (Burina)

8. Dalhat Suraj Mai Sharifiya (Kwadayi Mabudin Wahala)

9. Muhammad Bala Garba (Labarin Fauziyya)

10. Bilkisu Muhammad (Gani Ga Wane)

(wannan jadawalin baya nuna wane ne na 1 ko na 2 ko na 3, an jera ne kawai)

Allah ya kara basira.

Domin karin bayanin yadda gasar ta gudana  za a iya lekawa MARUBUTA TV da ke kan Youtube, tare da sauran shirye-shiryen marubuta da ke gudana a wannan katafaren zaure.

-Kabiru Yusuf Fagge









RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...