Thursday, December 5, 2019
Tuesday, November 19, 2019
Saturday, November 9, 2019
LABARIN LAIFUKA KO TASHIN HANKALI
*Rubutunka
Tunaninka*
Kabiru
Yusuf Fagge
*Labarin Laifuka Ko Tashin Hankali*
A ko'ina a fadin duniya
ana samun tashe-tashen hankula, hakan ya zama wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum. Saboda haka ne ake
samun yawan rubuce-rubucen labarai a kan tashe-tashen hankula.
Tuesday, October 29, 2019
DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI
*RUBUTUNKA TUNANINKA*
DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI
1. Maimaici: Maimaita karanta labarin tare
da sake kwafewa fiye da sau daya.
2. Farawa da wani rikici.
3. Farawa da labarin ainihin abin da ke
faruwa a lokacin, ba farawa da tunanin baya ba ko mafarki.
4. Kar ka sakar wa mai karatu ragamar sanin
inda labari ya dosa daga farko zuwa karshe.
5. Kar ka tsawaita bayani – amma ban da
tsanantawa wajen boye
abubuwa da yawa.
6. Kana iya kirkirar matsaloli guda biyu. Cikin gidan
tauraron labari da waje.
7. Ka dinga furta magana ko kalaman dake
cikin labarinka a fili, musamman yayin maimaita karantawa, don gane cancantarsu
ko rashin dacewarsu.
8. Yi amfani da siffatau, aikatau da
maganganu ma fi dacewa.
9. Ka tabbatar abubuwan da ka sa ko bayanan
da ka yi amfani da su a labarinka sun bayar da ma’ana.
Wednesday, October 9, 2019
LABARAI UKU DA SUKA CANCANCI LASHE GASAR HIKAYATA
LABARAI UKU DA SUKA CANCANCI LASHE GASAR HIKAYATA
Salo na cikin ma'aunan da alkalan Hikayata suka yi amfani da su
Masu iya magana kan ce "Ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.
Tuesday, October 8, 2019
RUBUTU MAI KYAU: MAFITA GA SABON MARUBUCI
Rubutunka Tunaninka
Kabiru Yusuf Fagge
RUBUTU MAI KYAU: MAFITA GA SABON MARUBUCI
Akwai abubuwa da suke taimaka wa sabon marubuci ya inganta rubutunsa ya zamo mai kyau. Sau tari marubuta sukan manta da wadannan abubuwa, kuma suna bayar da matsala a rubutu. Wadannan abubuwa su ne kamar:-
(1) Saka sauye-sauye ko sabani a tsakanin taurari, ko a rayuwar tauraro. Misali: Da farko sun tsani juna – A karshe sun koma son juna.
(2) Sauyin halayya: Da farko ya kasance mashayi – a karshe ya shiryu.
(3) Sauyi a zuciyar makaranci: Da farko kowa ya dauka tauraron labarin ne ya aikata wani laifi – a karshe ashe ba shi ya aikata ba.
(4) Ka da ka dora taurarin labarinka a kan rayuwar farin ciki tun daga farkon labari har karshe. Idan ya kasance haka, bai zama labari ba. Don haka dole ne ka gindaya musu wasu matsaloli ko tangarda, wacce za ta yi kamar ba za a iya warwarewa ba, sai a karshe a samu mafita.
Matsalolin da ake samarwa a labari sun hadar da:
(1) A tsakanin taurarin labarin da wani daga waje.
Misali – Wata tsohuwar budurwar tauraron ta kudirin aniyar ruguza auren tauraron ko ta halin kaka.
-Tsakanin tauraron da abokiyar zamansa.
Misali – Mijinta ne ya kasance cikakken mashayi. Kullum babu zaman lafiya.
-Tsakanin tauraron labarin da wani hali na rayuwa.
Misali – Takaici, wata cuta ko lalura da sauransu.
ABUBUWAN DA MARUBUCI ZAI SANI GAME DA TAURARO
Ya kamata marubuci ya san tauraronsa, don haka akwai wasu manya abubuwa da ya kamata lallai marubuci ya sani game da tauraronsa; babba ko yaro (wannan ya shafi tauraro mace da namiji)
Tauraro (a matsayin babban mutum)
1. Suna
2. Shekaru
3. Fasalinsa/Siffofinsa
4. Gidansa
5. Dangantakarsa/iyayen sa
6. Danginsa/iyalinsa
7. Abokansa a labarin
8. Alakarsa da sauran mutane
9. Aiki ko sana'arsa a labarin
10. Dabi'u ko halayyarsa
11. Irin abincin da ya fi so
12. Yanayin kayan da yake sawa
13. Yadda jama'a suke kallon sa
14. Ra'ayin sa
15. Burin sa
16. Muhimmin abin da ya kamata a sani a tare da shi
17. Shin makaranta za su so shi a ransu ko za su tsane shi?
Tauraro (karamin yaro)
1. Suna
2. Shekaru
3. Ranar haihuwar sa
4. Fasalinsa/Siffofinsa
5. Gidansu
6. Sunan mahaifinsa
7. Sunan mahaifiyarsa
8. 'Yan uwansa maza da mata
9. Matsayinsa a gidansu (na nawa ne?)
10. Abokansa na kusa
11. Abokansa na musamman
12. Abin da ya fi so (karatu, kallo ko kade-kade?)
13. Abin da ya fi ki
14. Matsayinsa a makaranta
15. Halayyarsa a makaranta
16. Wasannin da ya fi so
17. Abincin da ya fi so
18. Kayan da ya fi son sa wa
19. Alakar sa da sauran yara
20. Mutumin da ya fi masa muhimmanci a rayuwarsa (uwa, uba ko dan'uwa)
21. Halayyar sa a gida
22. Yadda mutane suke kallon sa
23. Ra'ayin sa
24. Shin zai shiga ran makaranta ko za su ji sun tsane shi?
KARIN BAYANI A KAN ABUBUWAN DA SUKA GABATA
1. Idan tauraron labarin yana aiki ko sana'a; shin yana jin dadin yi?
2. Daga cikin dabi'un tauraron akwai munana? Wadanne iri ne?
3. Wane irin buri ya ke da shi? Wane irin mutum yake son zama?
4. Me ya fi tsoro?
5. Mene ne aibun sa? Me ya rasa a rayuwarsa?
6. Wa ya fara so a ransa?
7. Wane abu mara kyau ne ya taba samun sa?
8. Dangane da burin sa na rayuwa. Ya cimma burin? Ta ya ya?
(c) Kabiru Yusuf Fagge
Subscribe to:
Posts (Atom)
MAKAHO MAI FITILA
MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...






