GASAR TSARA BANGON LITTAFI
Sunan Littafi: GOBARAR DAJI
Gidauniyar Adabi ta Dangiwa na gayyatar ƙwararrun masu zane da tsara bangon littattafai (Book Cover Designers) domin shiga gasar ƙirƙirar kyakkyawan bango na littafin GOBARAR DAJI.
Gobarar Daji littafi ne da ya yi magana kan matsalar barace-barace a cikin al’umma, illolin da take haifarwa, da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar. Saboda haka, ana buƙatar mai tsara bangon littafin ya fahimci ma’anar taken da kuma babban jigon littafin kafin ya ƙirƙiri zanen.
Abin da ake nema
Mai zane ya kamata ya samar da bango wanda:
- Zai bayyana ko ya yi ishara da ma’anar “Gobarar Daji” ta hanyar fasaha.
- Zai nuna matsalar barace-barace da kuma buƙatar samun hanyoyin magance ta.
- Zai kasance mai ɗaukar hankali
- Zai haɗa taken “GOBARAR DAJI” cikin rubutu mai kyau da sauƙin karantawa.
- Hotuna, alamomi ko zane-zanen da za a yi amfani da su su dace da taken littafin da jigon sa.
Muhimmin bayani ga masu shiga gasar
Hotunan da aka sanya a ƙasa misalai ne daga litattafai uku da gasar da aka gudanar a baya. An sanya su ne domin su taimaka wa masu shiga gasar fahimtar irin aikin da ake nema.
Ba a buƙatar a kwaikwayi waɗannan hotuna ko tsarin da aka yi amfani da su a baya.
Abin da muke son gani
Muna son ganin yadda mai zane zai iya mayar da taken “Gobarar Daji” zuwa bango mai ɗauke da saƙo mai zurf, bango wanda zai sa mai kallonsa ya fara fahimtar cewa littafin yana magana ne kan barace-barace, matsalolin da take haifarwa, da hanyoyin da za a bi wajen magance ta.
Saboda haka, muna buƙatar fasaha, tunani, ƙirƙira da fahimtar jigo.
Lokaci
Wannan gasa tsawon kwana uku me kacal daga gobe 2/10/2026 zuwa 5/10/2026 za a tura aikin da aka yi a Watsapp din wannan lambar 09033492760.
Za a zabi bango ɗaya da yayi fice inda za a yi amfani da shi a littafin kuma za a bayar da kyauta da karrama wanda yayi nasarar a taron da za a gabatar na bayar da kyaututtukan gasar a Katsina ba da dadewa ba.

No comments:
Post a Comment