KWAMITIN SHIRAYA TARON RANAR MARUBUTA HAUSA HADIN GUIWA DA GAME CHANGER GROUP (TGCG),
GASAR RUBUTUN GAJERUN LABARAI TA RANAR MARUBUTAN HAUSA TA DUNIYA 2026
A shirye-shiryen bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na shekarar 2026 wanda za a gabatar a Birnin Katsina a ranakun 31/12/2026 zuwa 01/01/2027. An shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan batun Tu'ammali da miyagun ƙwayoyi daidai da taken taron na bana, wato Gudunmuwar Marubuta Wajen Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi. Damar shiga gasar a buɗe take ga dukkan masu sha'awar shiga daga marubuta maza da mata sanannu da sababbi da ma masu sha'awar fara rubutu matuƙar za su kiyaye ƙa'idojin gasar.
MAUDU'IN GASAR
Yaƙi da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi
MANUFOFIN GASAR
1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari kan yadda tu'ammali da miyagun ƙwayoyi ke shafar goben ƙasarmu tare da haska dabaru na yaƙi da matsalar.
2. Samar da sababbin ra’ayoyi da mafita na zamani da za su iya taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
3. Sake fito da wata kafa ta musayar ra’ayi kan alaƙar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi da taɓarɓarewar tarbiyyar al'umma.
4. Ba wa marubuta damar nuna fasaha da basira da ƙwarewarsu a fannin rubutu da bincike ko ƙirƙira, musamman a kan abin da ya shafi tu'ammali da miyagun ƙwayoyi.
5. Samar da ƙarin abin karatu mai inganci da manufa cikin harshen Hausa.
TSARE-TSAREN SHIGA GASAR
1. Za a aiko da samfurin labarin da za a rubuta cikin kalmomin da ba su gaza 500 ba kuma ba su wuce 800 ba, ta wannan adireshin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com daga ranar 05/10/2026 zuwa ranar 30/10/2026.
2. Za a tace a zaɓi 30 cikin samfurin labaran da aka turo waɗanda suka fi burgewa a cikin kwanaki bakwai (30/10/2026 zuwa 7/11/2026).
3. Za a yi bita ta musamman ga masu waɗannan samfurin labaran 20 a kan wasu batutuwa da suke da alaƙa tu'ammali da miyagun ƙwayoyi da gasa da kuma rubutun gajerun labarai.
4. Bayan bitar, za a buƙaci kowannensu ya rubuto cikakken labarinsa wanda bai gaza kalmomi 1000 ba kuma bai wuce kalmomi 1,500 ba bayan bitar, daga 15/11/2026 zuwa 15/12/2026.
5. Za a bayyana labaran da suka yi nasara a wajen bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2026.
*SHARUƊƊAN SHIGA GASAR*
1. A tabbatar rubutun ya dace da batutuwan da suka shafi yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
2. A tabbatar an yi amfani da daidaitacciyar Hausa kuma an kiyaye ƙa'idojin rubutun Hausa.Dole ne amfani da haruffa masu lanƙwasa(ɓ, ɗ, ƙ, 'y).
3. A tabbatar an aiko da rubutun a tsarin Microsoft word kawai zuwa ga wannan email ɗin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com. tare da shedar yin rijista.
4. A tabbatar ba a taɓa shiga wata gasa da labarin da za a turo ba, kuma ba a taɓa bugawa a jarida ko wata kafa ko zaurukan kafafen sadarwa na zamani ba.
5. Wanda yayi rijista da taron Ranar Marubuta Hausa ta 2026 ne kaɗai zai iya shiga gasar.
6. Mutane biyu za su iya shiga gasar da labari ɗaya. Kuma dole ne a aiko da labari cikin lokacin da aka ƙayyade.
7. Kada labarin ya zamto ya ci zarafi ko tozarta wata al'umma ko ɗaiɗaikun mutane.
7. Ba a yarda a sake ɗaukar duk labarin da aka shiga da shi gasar a sake shiga wata gasar da shi ba.
8. A sani, hukunci da sakamakon alƙalan gasar shi ne na ƙarshe, ba za a sake tattauna shi ba a wani waje.
9. Kowane marubuci na iya shiga gasar ban da mambobin kwamitin ƙoli na shirya wannan taro.
KYAUTUTTUKAN DA GASAR ZA TA SAMAR
1. Za a bayar da kyaututtuka ga labarai uku da suka yi zarra a matakin na 1 zuwa na 3.
2. Za a bayar da takardar shaidar karramawa da awalajar litattafai ga waɗanda suka shiga gasar daga na 1 zuwa na 15 kuma za a duba yiwuwar buga labaran nasu cikin littafin da za a ƙaddamar da shi a taron shekara mai zuwa ta 2027.
Dr. Mujaheed Abdullahi Kudan,
A madadin Kwamitin Shirya Gasa na Ranar Marubutan Hausa 2026.
Ga link na yin rijistar
https://ranarmarubuta.com.ng