BBC za ta karrama taurarin Hikayata na 2018
Safiyyah Jibril Abubakar ne ya yi
zarra a cikin labarai kusan 300 da aka shigar gasar
BBC za ta karrama taurarin Hikayata
na bana a ranar Juma'a a Abuja.
A watan Satumba ne alkalan Gasar
Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana ''Ya
Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.
Wata malamar makarantar sakandare
mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar gasar ta bana.
Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe
gasar ne da labarinta mai suna ''Ya Mace'.
Da take bayyana yadda ta ji bayan da
ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, "Lokacin da aka kira
ni a waya aka shaida min labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce.
"Sai da na sake duba wayata don
na tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kira na aka yi aka shaida min na yi
nasara."
Labarin
'Ya Mace' a takaice
'Ya Mace, labari ne na wata budurwa
mai suna Halima wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 babu wani
tsayayye, alhali a bisa al'adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar
da ita.
Matsin lambar da take fuskanta daga
iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri Garba duk da cewa ba a gudanar
da wani bincike a kan shi ba.
Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata
kunne cewa kada ta kuskura a sake ta don idan ta dawo gida ba shi da halin
daukar nauyinta.
Sanin hakan ya sa Garba yi wa Halima
wulakanci iri-iri, har lamarin ya kai ga duka da zagi.
A karshe dai auren ya mutu; da ta
koma gida mahaifinta ya kore ta bayan ya lakada mata duka, sannan ya sha
alwashin tsine wa duk wanda ya ba ta masauki a cikin 'yan uwa.
Wannan ya sa Halima ta yanke
shawarar tsayawa da kafafunta ta hanyar kama hayar daki a cikin gari da yin
ayyukan hannu don ciyar da kanta.
Sai dai ba a jima ba mai gidan ya
samu labarin cewa ba ta da miji, ya ba ta notis yana mai cewa bai kamata mace
irinta ta zauna a tsakanin mutanen kwarai ba.
Dalilin
zaben 'Ya Mace
A cewar alkalan gasar, wannan
labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma'aunan da aka yi amfani
da su don tantance labarai 25 din da suka duba.
"Labarin ya tabo wata matsala
da ke faruwa a wannan zamanin, inda iyaye ke Allah-Allah su aurar da 'ya'yansu
mata.
Tun da aka fara labarin ake hawa,
ake tashin hankali da jan hankalin mai karatu", inji Bilkisu Yusuf Ali,
daya daga cikin alkalan.
Jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim
Malumfashi, ya kara da cewa, "Matsalar labarin daya ce kawai: tun daga
farko har karshe ake hawa, ba sauka. To amma shi ma wata dabara ce ta
marubuta".
Marubutan
da suka yi nasara a gasar bana
- Safiyyah Jibril Abubakar malamar makarantar sakandare ce, kuma daliba mai karatun digiri na biyu, wato Master's, a fannin Kimiyyar Kasar Noma a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Ta yi makarantar firamare a birnin
na Zariya, sannan ta yi karatun gaba da firamare a garin Gwandu na Jihar Kebbi.
An fi sanin ta da suna Safiyyah Ummu
Abdoul a duniyar marubuta. Labarainta, 'Ya Mace, shi ne ya zo na daya a
gasar Hikayata ta 2018.
- An haifi Sakina Lawal ne a birnin Kaduna na arewacin Najeriya, inda ta yi karatunta na firamare da na sakandare.
Tana da takardar digiri a fannin
Harshen Hausa wadda ta samu daga Jami'ar Jihar Kaduna.
Ita ce marubuciyar labarin Sunanmu
Daya, wanda ya zo na biyu a gasar ta Hikayata.
- Ita kuwa wacce ta zo ta uku a gasar, Bilkisu Muhammad Abubakar, a birnin Kano na arewacin Najeriyar aka haife ta.
Yanzu haka daliba ce a Jami'ar
Bayero ta Kano, inda take karatun Shari'a, wato Law. Labarin da ta
rubuta wanda ya kai ta wannan matsayi shi ne Zaina.
Labarin da ya zo na biyu
Sakina Lawal ce ta rubuta labarin da
ya zo na biyu .
Labarin da ya zo na biyu shi ne
'Sunanmu Daya' na Sakina Lawal.
Shi ma labarin wata budurwa ne wadda
kyawunta ya rude ta har take ganin duk yadda ta ga dama za ta yi da maza.
Da ta samu wani wanda take ganin ya
dace ta aura shi kuma yana da mata, sai ta sa ya saki matar, amma bayan ta aure
shi sai ta ga ashe dai kallon kitse ta yi wa rogo don haka ta fita.
Daga bisani ta sake samun wani mai
matar, amma suna son juna tsakani da Allah.
Sai dai kuma bayan ta aure shi sai
ta tarar ba wata ba ce matar illa wacce ta sa mijinta na farko ya saka.
Labarin da ya zo na uku
Labarin Bilkisu Muhammad Abubakar ne
ya zo na uku a gasar Hikayata.
Labarin da ya zo na uku shi ne
Zaina, wanda Bilkisu Muhammed Abubakar ta rubuta.
Shi kuma labari ne na wata mai suna
Zaina wacce mijinta ya yi batan dabo bayan tashin bam.
Bayan ta shekara shida tana jiran
tsammani iyayen mijin suka matsa mata lamba a kan ta sake aure.
A karshe dai ta ba da kai ba don
tana so ba, ta auri abokin mijin.
Wata rana suna zaune sai ga mijin ya
dawo ba zato ba tsammani.
A ranar Juma'a ne dai za a karrama
marubutan uku yayin wani biki a Abuja.
Wannan ce shekara ta uku ta wannan
gasa, wadda aka kirkira don bai wa mata damar fadin albarcin bakinsu.
Labaran
da suka cancanci yabo
Baya ga labaran da suka yi na daya,
da na biyu, da na uku, alkalan gasar sun kuma zabi wadansu da suka cananci yabo
guda 12:
- Aurena 12
- Kururuwar Ibilis
- Lauren Tirmi
- Nadama
- Da Kyar Na Sha
- Bakar Rana
- Kulu
- Matallafina
- Nakasa
- Rubutaccen Al'amari
- Kalubale
- Da Na Sani
No comments:
Post a Comment