Saturday, October 27, 2018

GASAR RUBUTUN LITTATTAFAN HAUSA TA GUSAU INSTITUTE 2019


GASAR RUBUTUN LITTATTAFAN HAUSA TA GUSAU INSTITUTE 2019

Malumfashi Ibrahim
Wannan gasa ta rubutun littattafan Hausa ta Gusau Institute, wata gudunmuwa ce domin bunkasa rubuce-rubuce cikin Hausa da za a dinga gabatarwa kowace shekara, karkashin kulawar Cibiyar Tallafa Wa Harkokin Ilimi Ta Gusau da ke Kaduna. An aza wannan gasa ne domin fito da inganta ayyukan al’adu da adabin Hausawa.
Wannan gasa za ta bai wa wanda/wadda ya/ta lashe gasar damar samun kyautar kudi domin agaza wa marubuta su tace littafin da sake tsara shi domin bugawa.
Ga masu sha’awar shiga wannan gasa, ana bukatar su aiko da somin-tabi da tsakure na abin da littafin ya kunsa, kada tsakuren ya wuce kalmomi 500, shi kuma somin-tabin kada ya wuce shafi 10 na kwamfuta. A tabbata tsakuren da somin-tabin sun isa kai tsaye ga Hukumar Gudanar Da Gasar zuwa ranar 31 ga Janairu, 2019. Za a tace da zabar uku daga cikin somin-tabin da kuma tsakuren littattafan da aka aiko wadanda suka fi burgewa a watan Fabrairu, 2019. Daga nan za a nemi wadannan marubuta guda uku da suka yi zarra da su aiko da cikakken littafin zuwa karshen watan Afrilu, 2019. Za a bayyana wanda/wadda ya/ta yi nasara a watan Mayu, 2019.
Awalajar gasar dai N250,000 ce ga na daya, N150,000 ga na biyu, sai N100,000 ga na uku

DOKOKIN GASAR
Wannan gasar dama ce ga duk marubutan Hausa, sai dai ga yara kanana, ana bukatar amincewar iyaye ko marika domin shiga gasar. Ma’aikatan Cibiyar GI da makusantansu ba su da damar shiga wannan gasa ta kowace irin fuska. Littattafan da ake bukata su shiga gasar su ne wadanda ba a taba buga ko karanta su ba, kada mutum ya aiko da littafin da ya wuce daya. Masu shiga gasar su tabbatar littafin nasu ne na kashin kansu ne, kuma ba a rubuta su domin cin zarafi ko mutuncin wasu ba.

FASALIN LITTAFIN
A tabbata littafin da za a shigar domin gasar ba a taba buga ko karanta shi ba, kada kuma ya gasa kalmomi 40,000 ko ya wuce kalmomi 50,000. A wannan gasar rubutattun labaran, ana iya aiko da kagaggen labari ko kuma gajerun labarai a matsayin littafi, amma ya kasance rubutun mutum guda. Ba a amince a aiko da littafi na hadin gwiwa ba, wato rubutun mutum biyu ko mai dauke da gajerun labarai na mutane daban-daban ba. Haka ban da littafin wakoki ko wasan kwaikwayo.

ALKALANCIN GASA
Alkalan gasar za su yi aiki irin na ba-sani-ba-sabo. Abubuwan da za su kula da su, ba su wuce iya kaga labari da gwanintar iya sarrafa harshe da salo ba. Dukkan sakamakon alkalanci gasar shi ne zai zama a’ala, ba za a sake tattauna sakamakon da wani ko wasu ba.
A kuma kula da wadannan batutuwa a lokacin gasar:
• Ban da satar fasahar wasu don shiga wannan gasar.
• Ban da amfani da sunan karya ko wani abu makamancin haka.
• Duk bayanan da aka turo domin gasar za a sakaya su, kuma ba za a yi amfani da su domin wani abu da ba na gasar ba.
• Sakamakon da alkalai suka bayar shi ne kurungus, ba daukakawa zuwa gaba.

YADDA ZA A TURO LITTAFIN SHIGA GASAR
A turo da dukkan abubuwan da ake bukata; kamar somin-tabi na labarin (a cikin shafi 10 na kwamfuta, da tsakure mai yawan kalmomi 500), a tabbata sunan mai shiga gasar ba ya cikin somin tabin ko tsakuren, a kuma hado da dan takaitaccen bayanin rayuwar mai shiga gasar, wato cikakken suna da shekarar haihuwa da wani abu da zai sa a tabbatar da mai shiga gasar, wato hoton id card ko passport da kuma aminicewar iyaye ko marika, in hakan ya zama dole ta intanet zuwa ga info@gusauinstitute.com ko kuma gusau.institute@gmail.com, zuwa ranar 31 ga Janairu 2019. 

(A kula: Mutane uku da suka tsallake tantancewa ne kurum za a sanar da su sakamakon tantancewa zuwa watan Fabrairu na 2019, a kuma nemi su aiko da cikakken littafin zuwa karshen watan Afrilu na 2019).

Daga karshe ba za a amince da canza wani labari da wani ba, in an turo.
Ba a karbar littafin shiga gasar da aka rubuta da hannu.
Ba za a mayar wa ‘yan gasa da littattafansu ba in an kammala gasar.
Mun gode, Allah ya ba mai rabo sa’a.

4 comments:

  1. Tambaya

    Assalamu alaikum, ya kamata a Kara muna hasken shekarun da aka aminta, Mai shiga gasar!

    Domin ina da sha'awa. Sai dai ban sani ba Ko shekaruna sun yi yawa, Ko zan iya shiga. An haifeni a 9-8-1994. Ko zan iya shiga?

    ReplyDelete
  2. Idan ina da hurumin shiga, dan Allah kuna iya tura mini a akwatin Email Abdulmaliksaidu6@gmail.com Ko 08069807496

    ReplyDelete

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...