I UNDERSTAND (NA FAHIMTA)
W
|
ani saurayi ne mai suna Nazir suka yi zasu hadu da budurwarsa
Mima a gidansu don ya dauketa su tafi yawon shakatawa.
Nazir yana zuwa sai aka yi rashin sa’a mahaifin Mima yana
gida. Kuma yana gefe ma yana shakatawa, ganin haka ya sa Mima ta yi sauri ta
cewa Nazir “Yawwa Allah ya sa ka taho min da littafin nan na “SPEAK TO ME IN
ENGLISH, MY FATHER DOESN’T UNDERSTAND.”(ka yi min magana da Turanci
mahaifina baya ji (fahimta))
Nazir ya yi murmushi ya ce, “Kash! Sai dai kuma jiya na bada
shi aro, amma na taho miki da “HOW IS OUR OUTING GOING TO BE?”(ya ya fitarmu
za ta kasance)
Sai Mima ta ce “To shi kenan, amma dai na fi bukatar “WAIT
FOR ME UNDER THE TREE OUTSIDE.”(ka jira ni a gindin bishiya a waje)
Nazir ya ce “To gobe in Allah ya kaimu zan aiko miki, har da
“DON’T STAY LONG PLS”(kar ki dade don Allah)
Kafin saurayin ya fita sai mahaifin Mima ya yi caraf ya ce,
“To ka hado mata da “I UNDERSTAND EVERYTHING YOU SAID”(na
fahimci duk abin da ku ka ce) ‘yan
iskan yara marasa kunya. Sai ki fita na gani.”
No comments:
Post a Comment