Sunday, October 7, 2018

MARUBUCIYA MARYAM KABIR MASHI NA CIKIN RASHIN LAFIYA

 
MARUBUCIYA MARYAM KABIR MASHI NA CIKIN RASHIN LAFIYA 

Fauziyya D. Sulaiman
Shahararriyar Marubuciyar littafan Hausa Maryam Kabir Mashi na neman taimako gurin Al'ummar Musulmi.
Maryam ta na fama da larurar ciwon koda wacce ta yi yawon zuwa Asibitoci daga Jahar Katsina har zuwa Asibitin Malam Aminu Kano, bayan gwaje gwajen aka tabbatar da kodarta ta hannun dama ce ta samu matsala sai an cire ta, amman da taimakon Yan'uwanta aka fita da ita Egypt. Bayan gwaje-gwaje da suka yi mata sun tabbatar da ciwon Kodar sannan suka karo gano wata Matsalar, wata tsoka ta danne lakarta(Spianl cord injury) don haka suka ce dole bayan wata biyu idan kodar ta sami sauki sai ta koma an yi mata aiki, idan ba haka ba zata iya yin flat paralise. Amman har zuwa kusan shekaru uku ba su sami abin da za su koma ba, wanda hakan ya ja Maryam ba ta iya motsa jikinta a yanzu ko tashi bata iya yi komai sai an yi mata, ga wani irin kumburi da kyalli da jikinta ke yi.
Abin da ake nema domin yiwa Maryam aiki Naira Miliyan Uku da rabi. Maryam marubuciya ce da ta bayar da taimako ga Al'umma, ku taimaki rayuwarta a yanzu da ta ke bukatar taimakonku yan'uwa. Ga wanda za su je kai tsaye tana zaune a garin Katsina Unguwar wado, kwanar shiga Kanyar 'ya'yan Mage, sai a tambayi gidan su Auta ko gidan Malama. Ko ku saka taimakon ta wannan account din 0098631815 diamond bank, Fauziyya Danladi. Ko a kira wannan lambar domin karin bayani 07037147070. Allah ya bada ikon taimakon rayuwar Maryam, amin.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...