ADDU'AR MATA
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Hannayena a
sama, fuskata na fuskantar Ka'aba ba kiftawa, na zurfafa sosai a wajen yiwa kasata
addu'a, fatana Allah ya shiryi al'ummar cikinta tun daga talakawa, masu hannu
da shuni zuwa shugabanni.
A zahiri wani dan
siyasar gundumarmu ne ya biya min kudin Umra don in zo in yi masa addu'a ya
sami fada a wajen gwamna da shugaban kasa, sannan in yi masa addu'a Allah ya sa
ya kara lashe zabe mai zuwa.
Ni kuma a zahiri
tun lokacin da zai biya min, na so ya ba ni kudin na kara jari sannan na
taimaki makobta, amma na lura ba zai yi haka ba, idan ma na ce hakan to zan iya
yin biyu-babu. Don haka na hakura, aka biya min muka taho.
Da na zo kasa
mai tsarki na lura ba abin da ya fi muhimmanci da ya wuce in yiwa kasata
Nijeriya addu'ar Allah ya kintsata ya daidaita lamuran mutanen cikinta, don kowa
ya sani ana cikin matsala.
A yayin da na
fara yin kasa-kasa da addu'ar, sai na jiyo wata mata Bahaushiya da ke gefena
tana yin tata addu'ar wadda ta ja hankalina, cewa take:
"Allah don
kadaitar zatinka da kyawawan sunayenka, Allah don isar mulkinka, Allah ka sa
mijina ya talauce, Allah ka sa kafin na koma gida Nijeriya mijina ya zama fakiri."
Haka take ta
maimaitawa, dole ba shiri na tsaya da duk abin da nake yi, na koma gefe ina kallon
matar nan, har ta gama, ta taso za ta wuce ni. Na yi sauri na tare ta.
"Baiwar
Allah in tambayeki mana."
Ta kalle ni a
dake, "Ba sai ka tambayeni ba, ka ji ina addu'a ko?"
Na gyada kai,
"Addu'a mai ban mamaki kuwa."
Ta yi murmushi a
baibai, "A wajenka ce mai ban mamaki, amma mu a wajenmu mata wannan addu'a
ce mai kyau. Kwanan nan mijina ya yi kudi kuma shi ya biya min wannan Umrar da
na zo, na ga take-takensa ne daga yin kudin nan yana so ya kara aure shi ya sa
nake masa addu'ar ya koma gidan jiya, ka ga idan yana fakiri ba zai iya kara
aure ba."
"Amma kina
da abin mamaki baiwar Allah..." Na ce da ita.
Ta katse ni
"Nawa mai sauki ne Malam, da yawa matan da suke gida suna yiwa mazajensu
addu'ar kada su yi kudi. Masu sukunin kuma matansu suna yi musu addu'ar Allah
ya sa su talauce don kar su yi musu kishiya. Akwai wata tambayar?"
Na gyada kai na
ce "Babu, sai dai in ce Allah ya kyauta."
"Amin."
Ta ce, ta wuce.
No comments:
Post a Comment