Saturday, October 27, 2018

LABARI CIKIN HOTUNA: YADDA AKA KARRAMA GWARZUWAR HIKAYATA 2018









GASAR RUBUTUN LITTATTAFAN HAUSA TA GUSAU INSTITUTE 2019


GASAR RUBUTUN LITTATTAFAN HAUSA TA GUSAU INSTITUTE 2019

Malumfashi Ibrahim
Wannan gasa ta rubutun littattafan Hausa ta Gusau Institute, wata gudunmuwa ce domin bunkasa rubuce-rubuce cikin Hausa da za a dinga gabatarwa kowace shekara, karkashin kulawar Cibiyar Tallafa Wa Harkokin Ilimi Ta Gusau da ke Kaduna. An aza wannan gasa ne domin fito da inganta ayyukan al’adu da adabin Hausawa.
Wannan gasa za ta bai wa wanda/wadda ya/ta lashe gasar damar samun kyautar kudi domin agaza wa marubuta su tace littafin da sake tsara shi domin bugawa.
Ga masu sha’awar shiga wannan gasa, ana bukatar su aiko da somin-tabi da tsakure na abin da littafin ya kunsa, kada tsakuren ya wuce kalmomi 500, shi kuma somin-tabin kada ya wuce shafi 10 na kwamfuta. A tabbata tsakuren da somin-tabin sun isa kai tsaye ga Hukumar Gudanar Da Gasar zuwa ranar 31 ga Janairu, 2019. Za a tace da zabar uku daga cikin somin-tabin da kuma tsakuren littattafan da aka aiko wadanda suka fi burgewa a watan Fabrairu, 2019. Daga nan za a nemi wadannan marubuta guda uku da suka yi zarra da su aiko da cikakken littafin zuwa karshen watan Afrilu, 2019. Za a bayyana wanda/wadda ya/ta yi nasara a watan Mayu, 2019.
Awalajar gasar dai N250,000 ce ga na daya, N150,000 ga na biyu, sai N100,000 ga na uku

DOKOKIN GASAR
Wannan gasar dama ce ga duk marubutan Hausa, sai dai ga yara kanana, ana bukatar amincewar iyaye ko marika domin shiga gasar. Ma’aikatan Cibiyar GI da makusantansu ba su da damar shiga wannan gasa ta kowace irin fuska. Littattafan da ake bukata su shiga gasar su ne wadanda ba a taba buga ko karanta su ba, kada mutum ya aiko da littafin da ya wuce daya. Masu shiga gasar su tabbatar littafin nasu ne na kashin kansu ne, kuma ba a rubuta su domin cin zarafi ko mutuncin wasu ba.

FASALIN LITTAFIN
A tabbata littafin da za a shigar domin gasar ba a taba buga ko karanta shi ba, kada kuma ya gasa kalmomi 40,000 ko ya wuce kalmomi 50,000. A wannan gasar rubutattun labaran, ana iya aiko da kagaggen labari ko kuma gajerun labarai a matsayin littafi, amma ya kasance rubutun mutum guda. Ba a amince a aiko da littafi na hadin gwiwa ba, wato rubutun mutum biyu ko mai dauke da gajerun labarai na mutane daban-daban ba. Haka ban da littafin wakoki ko wasan kwaikwayo.

ALKALANCIN GASA
Alkalan gasar za su yi aiki irin na ba-sani-ba-sabo. Abubuwan da za su kula da su, ba su wuce iya kaga labari da gwanintar iya sarrafa harshe da salo ba. Dukkan sakamakon alkalanci gasar shi ne zai zama a’ala, ba za a sake tattauna sakamakon da wani ko wasu ba.
A kuma kula da wadannan batutuwa a lokacin gasar:
• Ban da satar fasahar wasu don shiga wannan gasar.
• Ban da amfani da sunan karya ko wani abu makamancin haka.
• Duk bayanan da aka turo domin gasar za a sakaya su, kuma ba za a yi amfani da su domin wani abu da ba na gasar ba.
• Sakamakon da alkalai suka bayar shi ne kurungus, ba daukakawa zuwa gaba.

YADDA ZA A TURO LITTAFIN SHIGA GASAR
A turo da dukkan abubuwan da ake bukata; kamar somin-tabi na labarin (a cikin shafi 10 na kwamfuta, da tsakure mai yawan kalmomi 500), a tabbata sunan mai shiga gasar ba ya cikin somin tabin ko tsakuren, a kuma hado da dan takaitaccen bayanin rayuwar mai shiga gasar, wato cikakken suna da shekarar haihuwa da wani abu da zai sa a tabbatar da mai shiga gasar, wato hoton id card ko passport da kuma aminicewar iyaye ko marika, in hakan ya zama dole ta intanet zuwa ga info@gusauinstitute.com ko kuma gusau.institute@gmail.com, zuwa ranar 31 ga Janairu 2019. 

(A kula: Mutane uku da suka tsallake tantancewa ne kurum za a sanar da su sakamakon tantancewa zuwa watan Fabrairu na 2019, a kuma nemi su aiko da cikakken littafin zuwa karshen watan Afrilu na 2019).

Daga karshe ba za a amince da canza wani labari da wani ba, in an turo.
Ba a karbar littafin shiga gasar da aka rubuta da hannu.
Ba za a mayar wa ‘yan gasa da littattafansu ba in an kammala gasar.
Mun gode, Allah ya ba mai rabo sa’a.

Friday, October 26, 2018

TAURARIN GASAR HIKAYATA 2018


BBC za ta karrama taurarin Hikayata na 2018



BBC za ta karrama taurarin Hikayata na 2018
Safiyyah Jibril Abubakar ne ya yi zarra a cikin labarai kusan 300 da aka shigar gasar
BBC za ta karrama taurarin Hikayata na bana a ranar Juma'a a Abuja.
A watan Satumba ne alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana ''Ya Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.
Wata malamar makarantar sakandare mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar gasar ta bana.
Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna ''Ya Mace'.
Da take bayyana yadda ta ji bayan da ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, "Lokacin da aka kira ni a waya aka shaida min labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce.
"Sai da na sake duba wayata don na tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kira na aka yi aka shaida min na yi nasara."

Tuesday, October 23, 2018

Kaima Ka Dara: I UNDERSTAND (NA FAHIMTA)


I UNDERSTAND (NA FAHIMTA)

W

ani saurayi ne mai suna Nazir suka yi zasu hadu da budurwarsa Mima a gidansu don ya dauketa su tafi yawon shakatawa.


Nazir yana zuwa sai aka yi rashin sa’a mahaifin Mima yana gida. Kuma yana gefe ma yana shakatawa, ganin haka ya sa Mima ta yi sauri ta cewa Nazir “Yawwa Allah ya sa ka taho min da littafin nan na “SPEAK TO ME IN ENGLISH, MY FATHER DOESN’T UNDERSTAND.”(ka yi min magana da Turanci mahaifina baya ji (fahimta))

Kaima Ka Dara: JIBRILU NE DAGA SAMA





 

JIBRILU NE DAGA SAMA

 
Wani yaro ne mai suna Jibrilu Musa aka kai shi makarantar kwana ta boarding. Sannan kuma a dakin kwanan daliban (hostel) da aka kai shi gadon da ya samu hawa hudu ne, kuma aka bashi hawan karshe.

Tuesday, October 9, 2018

Short story: ADDU'AR MATA


ADDU'AR MATA

Kabiru Yusuf Fagge (anka)



Hannayena a sama, fuskata na fuskantar Ka'aba ba kiftawa, na zurfafa sosai a wajen yiwa kasata addu'a, fatana Allah ya shiryi al'ummar cikinta tun daga talakawa, masu hannu da shuni zuwa shugabanni.

A zahiri wani dan siyasar gundumarmu ne ya biya min kudin Umra don in zo in yi masa addu'a ya sami fada a wajen gwamna da shugaban kasa, sannan in yi masa addu'a Allah ya sa ya kara lashe zabe mai zuwa.

Ni kuma a zahiri tun lokacin da zai biya min, na so ya ba ni kudin na kara jari sannan na taimaki makobta, amma na lura ba zai yi haka ba, idan ma na ce hakan to zan iya yin biyu-babu. Don haka na hakura, aka biya min muka taho.

Da na zo kasa mai tsarki na lura ba abin da ya fi muhimmanci da ya wuce in yiwa kasata Nijeriya addu'ar Allah ya kintsata ya daidaita lamuran mutanen cikinta, don kowa ya sani ana cikin matsala.

*

Sunday, October 7, 2018

MARUBUCIYA MARYAM KABIR MASHI NA CIKIN RASHIN LAFIYA

 
MARUBUCIYA MARYAM KABIR MASHI NA CIKIN RASHIN LAFIYA 

Fauziyya D. Sulaiman
Shahararriyar Marubuciyar littafan Hausa Maryam Kabir Mashi na neman taimako gurin Al'ummar Musulmi.
Maryam ta na fama da larurar ciwon koda wacce ta yi yawon zuwa Asibitoci daga Jahar Katsina har zuwa Asibitin Malam Aminu Kano, bayan gwaje gwajen aka tabbatar da kodarta ta hannun dama ce ta samu matsala sai an cire ta, amman da taimakon Yan'uwanta aka fita da ita Egypt. Bayan gwaje-gwaje da suka yi mata sun tabbatar da ciwon Kodar sannan suka karo gano wata Matsalar, wata tsoka ta danne lakarta(Spianl cord injury) don haka suka ce dole bayan wata biyu idan kodar ta sami sauki sai ta koma an yi mata aiki, idan ba haka ba zata iya yin flat paralise. Amman har zuwa kusan shekaru uku ba su sami abin da za su koma ba, wanda hakan ya ja Maryam ba ta iya motsa jikinta a yanzu ko tashi bata iya yi komai sai an yi mata, ga wani irin kumburi da kyalli da jikinta ke yi.
Abin da ake nema domin yiwa Maryam aiki Naira Miliyan Uku da rabi. Maryam marubuciya ce da ta bayar da taimako ga Al'umma, ku taimaki rayuwarta a yanzu da ta ke bukatar taimakonku yan'uwa. Ga wanda za su je kai tsaye tana zaune a garin Katsina Unguwar wado, kwanar shiga Kanyar 'ya'yan Mage, sai a tambayi gidan su Auta ko gidan Malama. Ko ku saka taimakon ta wannan account din 0098631815 diamond bank, Fauziyya Danladi. Ko a kira wannan lambar domin karin bayani 07037147070. Allah ya bada ikon taimakon rayuwar Maryam, amin.

Thursday, October 4, 2018

Hausa Novel Cover 4: HISABI (LABARIN JARRABIN RAYUWA) By Abubakar Auyo

Hisabi

A kasan zuciyarta akwai burika da yawa da ba ta cimmawa ba, akwai mafarkan da ba su tabbata ba, akwai muradan da ba su zo kusa ba.
A rayuwarta akwai sadaukarwa, irin wacce a lokuta barkatai ta sha rasa farin cikinta saboda farin cikin wasu. Ba zato rayuwarta ta afka tsanani, tsananin da take buqatar tallafi daga kowane bigire, a kuma wannan lokacin ne kowa ya nisance ta ciki har da mai neman aurenta.
Aziza ta fara lilo tsakanin rayuwa da mutuwa!

Hausa Novel Cover 3: HISABI (LABARIN JARRABIN RAYUWA) by Abubakar Auyo


Hisabi

A kasan zuciyarta akwai burika da yawa da ba ta cimmawa ba, akwai mafarkan da ba su tabbata ba, akwai muradan da ba su zo kusa ba.
A rayuwarta akwai sadaukarwa, irin wacce a lokuta barkatai ta sha rasa farin cikinta saboda farin cikin wasu. Ba zato rayuwarta ta afka tsanani, tsananin da take buqatar tallafi daga kowane bigire, a kuma wannan lokacin ne kowa ya nisance ta ciki har da mai neman aurenta.
Aziza ta fara lilo tsakanin rayuwa da mutuwa!

Hausa Novel Cover 2: HISABI (LABARIN JARRABIN RAYUWA) by Abubakar Auyo


Hausa Novel Cover: HISABI (Labarin Jarrabin Rayuwa)


RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...