Wednesday, December 26, 2018

GWARZON LITTAFIN SHEKARA 2018


GWARZON LITTAFIN SHEKARA 2018

Adamu Yusuf Indabo


Littattafai da yawan da ba za su lissafu da yatsun hannu ko na kafa ba ne suka fito a cikin shekara ta 2018 da muke bankwana da ita. Wasu an wallafa su sun shiga kasuwa, wasu kuma an wallafa su ne a iya yanar gizo. Wasunsu na al'amuran rayuwarmu na yau da kullum, wasu na jarumta, wasu na barkwanci, wasu na kimiyya da dai sauransu.


Don haka shafin Adabi na jaridarku mai farin jini wato LEADERSHIP A YAU LAHADI ya dauki nauyin wallafa ra'ayoyinku na gwarzon littafinku na shekarar 2018.

Sai ku turo da ra'ayoyinku na littafin da kuke ganin shi ya kamata ya dau wannan kambu na GWARZON SHEKARA ta akwatun sakwannin ay1indabo@gmail.com ko kuma ta manhajar whatsapp ta wannan lamba +2347038339244 

Za ku fadi ra'ayin naku ne ta hanyar fadar sunan littafin, da sunan marubuci ko marubuciyar da ta rubuta littafin tare da hujjojinku na zabar littafin.


Sharadi:
- Littafin da aka wallafa a shekarar 2018 kawai ake da damar zaba.
- Ana da damar zabar littafi daya ne kacal.
- Mai fadar ra'ayin ya fadi cikakken sunansa da kuma adireshi.
- A turo da sakon daga yanzu zuwa karfe 9 na daren ranar Juma'a 28/12/2018.

Ku kasance da jaridar LEADERSHIP A YAU LAHADI ranar 30/12/2018.


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...