KANO LITERARY WEEK
HALACCIN MAI MARTABA SARKIN KANO GA MARUBUTA
Ga marubutan da ba su ji bayanin Sarkin Kano ba.
Da farko, duk dalibin da ya yi asarar wata gagarumar lakca
mai matukar muhimmanci zai ta bibiya don a gaya masa yadda lakcar ta gudana, ko
don dai ya ci jarrabawa ko kuma don ya kara lilimi.
Da yawa marubuta suna ta son su ji me mai martaba Sarkin
Kano ya ce a taron marubuta. Mu marubutan da muke wurin gaskiya mun gode Allah,
mun gode Manzon Allah (S.A.W.), mun gode wa Sarkin Kano.
Da farko, kafin jawabin Sarkin, marubuta sun ga kauna
miraran daga Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II yadda ya jingine
dukkanin wasu abubuwa da tarurruka da ke gabansa, ya halarci taron marubuta
kuma ya zauna da marubuta tsawon lokaci cikin nutsuwa da soyayya garemu
talakawansa.
Abu na biyu Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi
II ya yi jawabi na isasshen lokaci a nutse da ya sa kowanne mahalarcin taron ya
nutsu, a ilimance, ya ilimantar da kowa, kuma a gamshe ya gamsar da kowa.
Mai martaba ya hasko kafatanin matsalolin rayuwar Hausawa da
hanyoyin gyarasu, sannan ya dora alhakin wani bangare don taimakawa a gyara na
wadannan matsalolin ga marubuta, don a sami ingantacciyar al'umma nan gaba.
Mai martaba ya kasa jawabin nasa kamar haka:
ILIMI
"A kwanaki jami'ar Maiduguri ta yi wani bincike da
nazari ta gano yadda jihar Legas ta yiwa jihohin arewa fintinkau ta fuskar
ilimi, wadda ko da an tashi haikan ana neman ilimin to sai an shafe tsawon
shekaru dari biyu kafin a kamo su..."
Tirkashi, dole kowa ya nutsu, sannu a hankali mai martaba ya
zayyano wasu hanyoyi ga marubuta da masu sarauta (masu mulki) da hukumomi da za
su bi a inganta ilimi kuma a wayar da kai dangane da yadda za a sami ilimi ga
yankin Arewa, ta yadda kowane bangare zai ba da tashi gudunmawar don ganin haka
ta cimma ruwa.
Sannan sai batun karfafa gwiwa wajen koyar da fannonin ilimi
da harshen Hausa, ya kawo misalai da dama cewar duk wasu kasashe suna koyar da
iliminsu ne da yarukansu ta yadda mai koyo zai yi saurin fahimta.
BATUN AUREN WURI DA TSARIN IYALI
Mai martaba ya yi cikakken bayanin yadda za a inganta
rayuwar iyali ta yadda za a samar da ingantacciyar al'umma akasin wacce ake
ciki a yanzu. Ya fito da hanyoyi da marubuta za su isar da wannan sakon cikin
rubuce-rubucensu.
Ya yi bayanin yadda za a gujewa samar da matasa da ake
amfani da su wajen harkokin daba da yawan sake-saken aure, da yadda wasu mazan
suke dukan mazajensu.
Hakika Mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II ya nuna wa
marubuta gata, ya ilimantarsu, kuma marubuta suna godiya ga sarki, Allah ya ja
da ran sarki, Allah ya saka da alkhairi.
Sannan marubuta suna godiya ga Hajiya Sa'adatu Baba, da take
zama tsani tsakanin marubuta da mai martaba, Allah ya saka da alheri.
No comments:
Post a Comment