Thursday, December 6, 2018

TSARABAR EBEDI TARE DA MURYAR MACE.

 

NA BAR KADUNA...
Na bar Kaduna ranar shatakwas ga watan Nuwamba 18th Nov. Misalin karfe takwas na dare, 8pm mun isa Ibadan karfe tara da rabi cif 9:30am.
Alhmdulillah na yi tafiya maikyau mai dadi, tin tashinmu har muka isa Ibadan ban hadu da wani abu ko kadan na fargaba ko damuwa ba, na alakanta hakan da addu'o'in da na dinga jerawa.
An saukeni a Alakia by Breweries a in da na tadda Mr Dele yana jirana kamar yadda aka tsara, cewar shi zai daukeni zuwa babbar tashar Ibadan in da zan hau motar zuwa Oyo State.
Bayan mun gaisa yake cemun tin asuba yazo, ya zaci zamu iso da wuri, ya nemi layina bai samu ba, nace ntwk ne.
A tasha na dan yi zaman jira na wani takaitaccen lokaci, kafin motar mu ta cika, muka d'aga zuwa Oyo State.
Kafin mu tashi masu masaukinmu sun kira wayata har babu iyaka akan isowa da jin lafiyata, na isa kamar yadda aka tsara cewar mai aikin farin gida zata zo ta daukeni, yawan kirana da akeyi daga gida, da kuma mutanen Ibadan tare da karancin netwk na hanya ya sa wayata daukewa kafin in isa Oyo State.
Dan haka ina zuwa in da a kace in sauka, mai aikin gidan, wato Cecelia zata zo ta daukeni zuwa masaukina da naji suna ce mai White house.
Ban san yadda zan hadu da ita ba, tunda wayata ta dauke.
Sai nai dabara na tari Napep na ce ya kaini farin gida, wani dan tsaiko da muka samu shine yarbancin da ya dinga jeramun, na kuma fahimci baisan wani yare ba in ba shi ba.
Ga kuma gurin shiru ba wasu masu wucewa, naita gyada me kai dan na lura yasan gurin, amma bansan abin da yake cewa ba.
Kafin wani lokaci na ganni bakin wani katon farin gida, anan ne ma naji kirjina ya buga, gajiya da yunwa sun samoni nace ho'ni wannan gida? Gashi kuma dik Wanda muke mu'amalar kira da sauransu sai a hankali na ce oh ni Allah ya sa ba ruhina na kawo ba.
Amma da na tuna da tabbacin da Aunty Jut, Malam Khalid Imam suka ba dangina sai hankalina ya kwanta.
Balle da na tuna su Aunty Aha da Malam Hamza Dawaki harda murmusawa, ko ba komai sun shiga sun kuma fito lafiya.


TSARABAR EBEDI TARE DA MURYAR MACE.
Ebedi wani Mountain ne mai tsawo sosai, wani kan wani haka kamar gidan sama ya zagaye rukunin unguwar gabadaya, dalilin hakan ne ake kiran rukunin wajen da wannan suna.
Dan har munso mu hau, sai suka ce mana mata basa hawa sai dai maza.
Wanshekare misalin karfe tara da rabi na safiya Mr. Kofi ya iso ya kwankwasa daki na farko mai suna Abubakar Gimba, Nkem ta fito, na biyu Chinua Achebe Hauwa ta fito, Wole Soyinka Remi ta fito muka hadu gaba daya a sitting room.
Bayan an gaisa ya kara yi mana sannu da zuwa tare da kara isar da sakon uban gayya Dr. Wale Okediran, da Mr Bode dik dai akan barka da zuwa.
Daman tin kafin mu bar gidajenmu mun riga mun gabatar da abin da za mu je mu yi a can, wato za muje ne musamman don yin wani sabon aiki walau rubutu ko wake, ko kuma mu tafi da wanda muka fara mu karisa a can da yi ke ni na fara nawa tin a gida, kamar yadda na tura mishi har ya bukaci in gutsuro kadan daga abin da nake rubutu wannan yasa d'aurawa kawai zanyi a kai.
Sai abu na biyu wanda ke cikin sharuddan zaman wannan gurin, wato ziyarar wasu daga makarantunsu don koya musu wasu abubuwa walau na boko ko al'ada ya danganta.
A rana ta biyu da kammaluwarmu muka fara ziyarar makarantar farko wato IDGS in da muka gabatar da kanmu gurin Principal da daliban, daga nan muka wuce Ajayi Crowder School nan ma muka gabatar da kanmu.
A kan wanshekare zamu fara zuwa, ni dai na gabatar da kaina matsayin marubuciya wanda zata karantar da su rubutu da abin da ya kunshi rubutun kanshi, dik dai da wasu na cewa marubuci haihuwarsa akeyi, har nai musu misali da ni kaina cewar na fara rubutu tin ina primary dikda ni nasan da kayana a ka haifeni (I'm writer by Born) amma ban yadda wani bazai iya tashi akoya mishi yayi har abin da ni banyi ba.
Sai nai amfani da wadannan kalmomin Wanda na taba kawowa gidan dandalin Marubuta na Muhammad Lawal Barrister 2013 Wanda a kayi kwana da kwanaki ana sharhi a kai a karshe Na'ima Alfan ta bada amsar ina jin h

TSARABAR EBEDI TARE DA MURYAR MACE.
A matsayina ta bahaushiya 'yar arewa, an nemi da in koyar da su 'kananan kalmomi da harshen hausa sai in fassara musu zuwa turanci ta yanda za su fahimta.
Sannan in koyar da su raye-raye da wakoki na al'adunmu, in kuma gaya musu ma'anar wakokin to Alhmdulillah a wannan fanni kam, dalibai su ka yi mun rututu, har a kanzo a rage su daga ajina kunsan bayerabe gurin rawa.
A bin da na lura da yaran harshen gida yai matukar tasiri a rayuwarsu, so sukan fahimci turanci ne dai dai iyawarsu.
Dan kuwa yawancin koyarwar wajajen idan an yi turanci na minti 20, za su yi yaren minti arba'in.
Suna himmanta harshensu, al'adunsu, addininsu.
Hausa kuwa ko ZO ba su sani ba, dan kokkoya musu da nayi babu laifi sun kakkama wasu, dan ranar babban taronma su ne za su yi ma baki maraba da harshen Hausa su fassara zuwa turanci.
Na manta a baya in fada muku cewar; bayan mun gama training din daliban dukanmu mu 4 to akwai babban taro a gaba Wanda Dr. Da abokanshi, zuwa jama'ar gari malaman makaranta 'yan jaridu da sauransu za su zo don kallon wannan program din.
Mu kuma za mu fito tare da dalibanmu da abubuwan da muka koya musu su nuna a gaban manyan baki.
A nanne 'yan jaridu za su yi mana tambayoyi.


TSARABAR EBEDI TARE DA MURYAR MACE.
Kafin muje gaba barin amsa tambayoyin da wasu ke yi kamar haka.
Wa ke daukar dawainiyar ku ta fuskar ci da sha, zuwa kudin da kuke amfani dashi gurin zirga-zirga
Wasu hanyoyi a ke bi, a samu zuwa?
Kowa zai iya zuwa ko sai Marubuta?
Dr. Wale Okediran shine me gayya me aiki. Medical doctor, dan siyasa memba ne na house of representative, abuja tsakanin 2003-2007.
Sannan ya taba rike mukamin shugaba na 'kungiyar nan ta Marubuta ta 'kasa wato Association of Nigerian Author's tsakanin 2005-2009.
Yana da kishi kwarai akan dik wani aiki na kirkira, mutumin Oyo state ne karamar hukumar Iseyin in da babban ginin White house yake babban gida mai dauke manyan *gate* biyu.
A cikin gidan gini biyu ne, da farko in ka shigo zaka taradda gini na farko wanda kaninshi da matarshi suke zaune, sai na biyu na Marubuta zaka gane hakanne ta hanyar 'katuwar banner da aka lika wadda ita ke alamta maka cewar wannan guri wani daba ne na marubuta bawai Nigerian kadai ba, harta kasashen ketare na zuwa suyi program din.
Shiyasa banner take kamar haka *Ebedi international writers residency*
Wajen ba ya yankewa da mutane, yanzu muna gama namu muka tafi, maza za su zo su yi nasu in sun gama wasu set na mata su kara zuwa haka gurin yake kodayaushe.
In mata sunyi sun tafi, sai maza su zo su yi.
Kana shiga ciki zaka taradda katon hall a hannun hagu mai dauke da kujeru masu yawa, sannan a gefe ga durowar karatu liabry masu kunshe da littafai kala-kala.
Daga gefen damanka dinning hall ne Wanda yake fuskantar kitchen akwai komai a ciki kai kace gidan macen aure ne.
In ka shiga daga ciki kuma falo ne haka babba da setin Kujeru da kayan kallo sai dakunan kwana ko wani mutum da dakin shi, da toilet, bath dik abin bukata.
Sunayen dakunan kawai za ka gani ka tabbatar ma da kanka cewar wannan mutumin dan kishin rubutu da Marubuta ne.
An kirkiri gurinne musamman don samun natsuwar marubuci, za kai aikinka cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
*Wani abin mamak



No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...