NI MA HAKA NAKE!
Gajeren Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Ina isa wajen dan restaurant din na yi kici6is da wata
kyakkyawa mace wadda ta sha hoda da gazal da jan baki tana yi min murmushin
sace zuciya da ilahirin jiki.
Ban yi kasa a gwiwa ba ni ma na mayar mata da lallausan
murmushi, don an ce yaba kyauta, tukwici.
To amma kuma me zai faru? Ban yi aune ba, na ji saukar wani
wawan mari a kuncina na dama, har sai da na daina ji da kunnen bangaren na
mintuna biyar, idona daya ya kanne. Bayan na warware ne, na juya a tsanake, na
kalli gwanin da ya sharara min wannan mahaukacin marin.
Wani tikeken kato na gani tsaye a kaina yana huci, cikin
zubar kwalla na ce, "Bawan Allah me na yi maka, ka yi min wannan
marin?"
Ya nuna matar da muka yi musaya murmushi da ita,
"Wannan matata ce, me ya sa ka yi mata murmushi? Na ga lokacin da ka bi ta
da murmushi."
"To amma Bawan Allah, ba ka ga lokacin da ita ta fara
yi min murmushin ba."
Ya yi dariya, "Ai ita haka yanayinta yake, haka
fuskarta take, saboda tsabar kyanta, duk wanda ta kalla sai ya ga kamar
murmushi take yi masa...."
Bai rufe baki ba, ni ma na takarkare tun karfina na sharara
masa mari, sannan ban tsaya bata lokaci ba, na ci gaba da cewa, "Idan haka
yanayinta yake, ni ma haka nawa yanayin yake, duk wanda na kalla sai ya ga ina
murmushi idan ya yi tunanin murmushin nake, idan kuma ya yi tunanin fushi nake,
sai ya ga kamar ina kuka..."
Mamaki ya kama shi, mamakin ya aka yi dan firit da ni, na
iya zabga masa mari haka, yana cikin tunanin irin matakin da zai dauka, wasu
sojoji guda uku suka iso wajen suna kallona, "Ya aka yi Anka ashe har ka
riga mu zuwa."
"Alhamdulillahi." Na furta a raina, a fili kuma
ina kallonsu, na ce "Wallahi na iso, ai dole in zo da wuri, don amsa
gayyatar Babban Maigida."
Suka yi dariya, muka tafi, ina yiwa kato mai mata
gwalo, shi kuma yana cije baki.
No comments:
Post a Comment