Wednesday, December 12, 2018

Kirkirarren Labari: MAI WAINA

MAI WAINA

Akwai abin mamaki, ka ga tun safe zukekiyar budurwa dauke da roba cike da waina tana bi shago-shago tana talla cikin murmushin sace zuciya da rikita, rikitaccen saurayi ko tsohon banza.
Hakan ya sa da wuya ka ga a cikin shaguna goma da ta je, ba a siya a shaguna takwas zuwa tara ba, ragowar shaguna biyun kuwa sai idan babu yadda za su yi kamar rashin kudi ko wani abin daban zai sa ba su siya ba.

Amma sai ka ga yarinyar nan ta wuni ba ta siyar da wannan wainar ba. Kuma ba gida take komawa ta karo ba.
Wannan dalilin ne ya sa na kudiri niyyar ganin kwakwaf in ga me ya ke sa a haihu a ragaya.
Da safe misalin karfe takwas na binciko wasu tsofaffin kayan sawata na sanya - don wandon ma ya dan yage ta gefe, sannan, na je makota, na ari tsohuwar robar wani almajiri ta bara, na tsallaka zuwa bakin kasuwar Sabongari ta Kanon dabo.

A kofar shiga kasuwar da ake kira Kofar 'Yankura na riski 'yanmata masu siyar da waina su shida, kowacce daga cikinsu ta zambada hoda 'yar-bajau a fuskarta, ta yi kwalliyarsu irin ta budurwoyin bayan-gari ko kauye, dukkansu sun yi radau da su. A tare da su akwai almajirai, da alamar tare suke. Sai da na duba daya daga cikin 'yanmatan nan, kuma cikakkiyar budurwa, akalla 'yar sha takwas zuwa ashirin da wani abu, ta cika, ta yi tsirtsir da ita, kuma na lura bata da almajirai da yawa, don su uku ne kawai a tare da ita, kawai na bi bayanta.
Ta dube ni, 'Kai ma almajirin ne?" Tana mai tambayata.
Na gyada kai, "Kwarai kuwa..."
Tana yi min kallon biyu ahu, ta ce "Ka dai san yadda muke yi ko? Don na ga kai din iwa sabo."
"Na sani mana...." Na amsa mata a matsayin na sani, alhalin sanin nake nema.
"To ai hikenan, sai ka biyo mu mu higa..."
Misalin karfe takwas da mintuna arba'in da biyar aka bude kofar shiga kasuwar, muka ranka ciki. Ba mu fara bin shaguna ba sai da muka kai rabin kasuwar, a lokacin da yawa masu shagunan sun fara bude shagunansu, haka muna bi, yarinya Mai Waina tana yi musu talla cikin yanayi mai cike da shubuhar 'yan kasuwa, su kuma suna siya. Da zarar an siya sai ta raba mana.
A wasu shagunan ma har wasa suke yi da masu shagunan, wasu su tsokaneta, wasu su yi kalamansu na 'yan kasuwa da 'yanmatan kasuwa, mu dai muna biye, idan aka siya a raba mana, ina yi ina nazarin yadda rayuwar ke gudana.
A daidai lokacin da aka siyi rabin wainar, anan na fuskanci yadda harkar take, na kara samun wani ilimin - Ashe wainonin da aka babbamu sadaka su almajiran suke sake siyarwa yarinyar, ita kuma sai ta mayar cikin robarta ta ci gaba da siyarwar.
Mai Waina tana siyar da wainar ga masu shaguna a kan Naira Talatin, ita kuma idan an raba, sai ta siye daga hannun almajiran a kan Naira goma ko Naira biyar ma. Yadda ake yi kuwa shi ne;
Wani layi dake cike da sito-sito mara mutane da yawa muka shiga, Mai Waina ta sami wuri, ta zauna, muka isa kusa da ita - almajiri na farko ya mika mata kwanonsa cike da waina, yana mai fadin, "Guda tara ce."
Ta kirga, sannan ta juye a cikin robarta, ta dauko kudi Naira casa'in ta mika masa, ya karba, kowacce waina ta tashi a Naira goma kenan.
Na gaba ma ya karasa, ya mika mata, ta kirga guda goma sha uku ce, ta juye, ta mika masa Naira dari da ashirin, ta rage naira goma kenan, ya yi tirjiya, ta dube shi.
"Kar ka yi min iskanci to miye?" Ya yi shiru.
A haka, har aka zo kaina, na tsaya ban mika mata ba, ita kuma ta tsaya, tana kallona.
"Kai ba za ka kawo ba? Haka fa muke yi, kuma kai ma dole haka za ka yi, ba ni in irga, in ba ka kudinka?" Ta warci robar dake hannuna, ta kidaya, ta juye, ta ba ni kudin. Sannan ta dauki robarta muka kara gaba.
Haka ake yi, idan aka yi ciniki sosai kamar rabi ko fiye da rabi, sai mu samu wani lungu ta siye, ta juye, mu sake rankayawa.
Sai dai idan almajiri yana jin yunwa zai iya ci daga cikin wainar, amma na lura akwai sharadin ba zai cinye duka ba, sai dai idan ba zai ci gaba da bin ta ba.
Da zarar rana ta doso faduwa yammaci ya yi, sai kuma wanda zai ci wainarsa ya ci, don ba za ta sake siya ba. A haka har wadda ke cikin robarta ta kare. Haka har zuwa yammaci, kamar karfe shida. To a lokacin ne na ga abin da ban taba zaton gani ba.
Wani lungu Mai Waina ta shiga, ta sami wuri ta rakube, ni da ragowar almajiran da muke bin ta, muka tsattsaya, ni kan tunani na tsaya ina yi, shin me kuma za a yi tunda waina ta kare? Ta daina siyen ta hannunmu.
Na ga almajiri na farko ya shiga lokon da take, jim kadan ya fito yana murmushi - haka ma na biyu, a haka a haka har rage saura ni kadai. Kodayaushe ni nake zama na karshe a duk abin da ake, ko don ina bako?
"Ka je mana?" Na ji daya daga cikin almajiran yana cewa da ni. Ba musu na isa wurin.
Babbar magana, ashe 'yan kudin da almajiran suka samu Mai Waina take karbewa, ta hanyar idan suka je, sai ta bude musu gabanta ko kirjinta, su gani, su ba ta kudin da ta bukata.
Za ka kalli gabanta a N50, kirji kuma a N30 a 'yan sakanni ko mintuna. Iya adadin lokacin da ka diba - iya adadin kudin da za ka bayar. Kirji da gaba ya kama Naira tamanin kenan cikin sauki, amma idan ka saki baki sakanninka suka tafi, mintuna suka gifta za ka tarar ba ka shirya ba ka kalli sama da dari biyu ma.
Bayan ta gama yi min bayani, ta dora da cewa, "Na yi maka wannan bayanin ne saboda na fahimci kai bako ne, ya kake gani, zaka bi sawu ne ko za ka noke, don mu haka muke yi, idan kuma ba ka yi ba, gobe ba za ka bi ni ba... kar ka wani tsaye wani yane-yane....."
Wannan kalma ta Mai Waina ta karshe ta ba ni mamaki. A lokaci guda na fada tunanin ko in bi sawun ne don in ga zahiri, ko kuma in noke?
Ya ku ka gani?

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...