Saturday, December 8, 2018
TSAKURE DAGA GWARZON LITTAFIN SHEKARA 2018 - SABO DA MAZA
TSAKURE:
Sabo da Maza labari ne na wani Soja mai suna Bashir Bello wanda ya bace a dajin Sambisa, rayuwarsa abin nazari ce, rayuwar da ya taso a cikin bariki tsakanin kabilu, rayuwar da ya yi tare da Yar Aljanna karuwar da ta haska mashi rayuwa, ta koya mashi lakashewa da holewa, karuwar da taso ta aure shi da karancin shekarunsa. An zarge shi da kashe Blessing, yarinyar ta taso cikin maraici da soyayya Bashir wanda ya yi sanadiyar shigarsa kurkuku inda ya hadu da hatsabibai: Ajimbo,
Makuba, Rabbauna da Audu Adaka yaran wani hamsakin dan siyasa da suke yi wa safarar makamai da kwayoyi tsakanin Kaduna, Abuja, Bauchi da Jos. Hatta rayuwar mahaifan Bashir watau Bello da Indo Aishatou rayuwarce mai cike da abubuwan mamaki, rayuwar da suka yi tsakanin gungun barayi, mahaifin Aishatou mai suna Harouna bafillace ne da yake zaune a cikin wata ruga dake dajin Garin Dan Galadima a Kasar Zamfara, ya shahara sosai wajen sace-sace da kuma boyewa cikin Dajin Rugu, Dajin Falgore, Dajin Kamuku da Dajin Mangu dake cikin kasar Najeriya. Labarin Sabo a Maza labari ne da ya haska yadda kasar Nageriya ta fada cikin rashin tsaro, ya bayyana yadda matsalolin tsaro suka yi tasiri a cikin al’ummar kasar da kuma yadda jami’an tsaro suka tsunduma cikin harkokin cin hanci da rashawa. Sannan labarin ya haskaka yadda jami’an tsaro musamman Sojoji suke shan wahala wajen yaki da tsageru da kuma tsageranci a cikin kasa, labarin ya haskaka yadda sojoji suka kasance madubi guda daya da ya yi saura wanda ke haskawa da kare matsalolin tashe-tashen hankulla a cikin kasa. Labarin Sabo da Maza shi ne labarin da ya lashe gasar Aliyu Muhammad Books Prize 2018 wanda cibiyar Gusau Institute Kaduna ta sanya a shekarar dubu biyu da goma sha takwas. Marubuci Bello Hamisu Ida ne ya rubuta labarin.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...
No comments:
Post a Comment