Abokin
DARIYA
Na
KABIRU YUSUF FAGGE (anka)
07030319787
Haqqin mallakar littafi (m) Kabir Yusuf Fagge Anka
Copyrights (c) Kabir Yusuf Fagge Anka
An fara bugawa a 2016
Bugawa da yaxawa
GIMBIYA PUBLISHERS FAGGE
Layin Kasuwar Mata, Fagge D2, Kano.
Bugawa a na'ura:
Anka-Graphics Fagge
709 G/Lemo, Fagge D2, Kano.
07030319787
YARO MAI
SURUTU
W
|
ani yaro ne
sarkin surutu ya tambayi mahaifiyarsa ya ce “Momy wai me ya sa wasu wurare
a gashin kanki ya koma fari?”
Mahaifiyar yaron nan ta yi shiru
tana tunani, can wata hikima ta faxo mata, ta yi tunanin bari ta yi amfani da
wannan damar wajen koyawa yaron darasin rayuwa, sai ta ce “Saboda kai ne hakan
ke faruwa xana. Wato duk lokacin da ka yi wani abu mara kyau sai gashina xaya
ya zama fari.”
Yaron nan ya yi shiru yana tunani
can ya ce, “Yanzu na gano dalilin da ya sa dukkan gashin Kaka ya ke fari fat.”
KUSKUREN
ADIRESHI
W
|
ani magidanci ne da matarsa suka sami hutu don haka suka
shirya yin tafiya zuwa garinsu, to amma matar tana da wani uzuri don haka sai
washegari za ta isa.
Yayin da wannan magidanci ya isa
garin ya kama otel, sai ya aikawa matarsa saqo. Yayin aika saqon sai ya
kuskure, ya aika saqon ga matar malaminsa wadda mijinta ya rasu kwanaki biyu da
suka wuce.
Matar tana tsaye saqon ya shigo,
tana karantawa ta yi wata qara sannan ta faxi qasa sumammiya.
Mutanen da ke kusa suka
shigo cikin tashin hankali suna faxin “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, me
ya faru?”
Xaya daga cikin matan da suka
shigo ta xauki wayarta da ta gani yashe a gefe, ta duba. Sai ta ga an rubuta:
“Matata ki shirya zuwanki inda
nake gobe, don na shirya miki komai.”
Wato matar malamin ta xauka mijinta
ne da ya mutu ya aiko mata da saqon ya isa lahira, ya shirya mata komai.
TALATIN
DA BIYAR
W
|
ani tsoho ne ya tsinci kuxi, sai ya tafi gidan rediyo ya yi
sanarwar ya tsinci kuxi har TALATIN DA BIYAR aka yi cigiya, har aka taki sa’a
aka sami wani mutum da ya jefar da kuxi Miliyan Talatin Da biyar ya ji, ya zo
gidan rediyon yana ta godiya, aka nuna masa tsohon da ya ce ya tsinci kuxin, ya
je ya yi ta yi masa godiya, sannan ya kawo ladan tsintuwa Naira dubu hamsin ya
baiwa tsoho.
Tsoho ya karva yana godiya,
sannan ya buxe buhun shi ya xauko Naira Talatin da biyar ya miqawa mutumin ya
ce, “Na daxe da tsintarsu da har zan kashe sai na ji tsoron Allah na ce bari
dai in zo in yi cigiya, kuma ga shi cigiyar ta yi amfani, har na sami toshi mai
tsoka.”
Idan kai ne mutumin nan ya za ka
yi da tsohon nan?
MUS - MUS
MAGE
A
|
n yi wanisaurayi mai suna Ididiya da ya yi sabon aure, ya je
gaida surukansa gidansu da daddare, domin ya nuna godiya ga auren da suka ba
shi. Aka sauki Ididiya a falo, duka matan gidan da maigidan da yaran gidan suka
zo falon ana gaggaisawa. Bayan sun gaisa, sai maigidan ya sa aka kawo masa
abinci da naman kaji zuqu-zuqu.
Aka yi aka yi da Ididiya ya ci
abincin nan, amma ya ce sam ya qoshi, sai dai ta ciki na ciki, domin yawunsa ya
tsinke. Daga haka sai aka ci gaba da hira ana dariya, shi kuwa hankalin Ididiya
yana kan kwanon abincin nan da ke buxe, yana haxiyar yawu. Kawai sai aka xauke
wutar lantarki.
Ididiya na ganin haka, ya yi
sauri ya xauki cinyar kaza ya kai bakinsa, wal! Kawai sai aka kawo wuta,
Ididiya bai gama kai nama bakinsa, kuma ya rabo shi da kwano, gaba xaya kuma
hankulan surukansa da ‘ya’yansu ya yo kansa. Ididiya ya rasa yadda zai yi kawai
sai ya fara shuna naman yana cewa.
“Mus! Mus! Mus! Mage, mus muskule
mage.”
Surukan nan nasa suka kalli juna,
suna shirin yin dariya sai surukinsa ya ce “Malam Ididiya ai a gidan nan babu
mage.”
Ididiya ya rasa yanda zai yi sai
ya ce “Ai na xauka a gidanmu ne da muke da tarin maguna.”
Suka qyalqyale da dariya.
MUKULLINA
NAKE NEMA
W
|
ani saurayi ne mai suna Tanko ya je zance wajen budurwarsa
Nene, bayan da suka gama zancen zai tafi sai ya xauko kuxi Naira dubu xaya ya
ba ta, ta qi karva, ya yi ya yi ta karva, amma sam ta qi karva, da ya ga haka,
sai ya jefa mata ya juya da sauri ya fita, ita ma ta shige cikin gida da sauri
don ya tabbatar ba za ta karva ba.
Can sai saurayin nan ya dawo
soron gidan budurwar yana laluben inda ya jefar da dubu xayansa don ya xauka,
yana kai hannu daidai wajen ashe itama budurwar ta dawo xaukar kuxin kawai sai
ya ji hannu a kusa da nasa hannun, suka ga juna, kawai sai ya yi farat ya ce.
“Ashe ke ce, ai dawowa na in duba
xan makullina.”
Itama sai ta ce “Nima xankunnena na
dawo dubawa ko a nan ya faxi.”
Tanko ya dube ta ya ce “Ba kin ce
min, kin daina sa xankunne ba har sai mun yi aure.”
Nene ta yi murmushi ta ce “Ai
kamar ka ce min yau ba da mota ka zo ba.”
Suka yi dariya.
SAI TA
KASHANCE ZAN FAXA
W
|
ani Xanfillo ne suna zaune suna hira shi da abokansa, sai ya
hango Kawunsa yana barci a gefen rijiya, kawai sai Xanfillo ya tuntsire da
dariya. Abokansa suka ce “Me ya faru kake dariya haka Ja’e?”
Ja’e ya kuma vasgewa da dariya ya
ce “Na ga wani abu na shirin faruwa amma ba zan faxa ba sai ta kashence.”
Can sun ci gaba da hirarsu, sai
Kawun nan nasa ya afka cikin rijiya ji kake tsundum, kawai sai Ja’e ya kuma
tuntsirewa da dariya ya ce “Wallah ta kashence, dama na she sai ta kashence zan
faxa.”
KAI
SARKIN FADA QARYA NE
W
|
ani Alhaji ne yana zaune a qofar gida tare da jama’arsa suna
hira. Can Alhaji ya sako wata hira a ciki ya rinqa sharfaxa qarya yana cewa, “A
lokacin da muka je Mongoliya can gabashin duniya mun ga wata tsuntsuwa wacce
fukafukinta ya kai girman fuloti uku.”
Mutanen Alhaji sai cewa “Wannan
haka yake, gaskiya ne wannan.”
Da wani yaron Alhaji ya ga qaryar
ta yi yawa, sai shima ya ce “Alhaji har ka tuna min da wata bishiya wacce in
aka sareta sai an yi shekara biyar ana amfani da itacen.”
Alhaji ya harareta ya ce “Haba
Malam wannan qarya ne ta ya ya haka za ta faru?”
Mutanen wajen suka ce “Gaskiya
qarya ne.”
Alhaji ya ci gaba da cewa, “Idan
har gaske ne a ina wannan bishiyar take?”
Wannan mutumin ya ce “Yawwa
Alhaji, ai wannan tsuntsuwar da ka ba mu labari a wannan bishiyar take da sheqa
da ‘ya’yanta.”
Alhaji ya ce “Au to to, haka ne,
na gane bishiyar ai in mutum mai tattali ne sai ya kai shekara bakwai ana
amfani da ita a gidansa.”
YO SUN
IYA WANNAN ABIN ARZIQIN NE
W
|
ani dattijo ne ya kamu da rashin lafiya, sai aka kai shi
asibiti aka duba shi, inda aka kwantar da shi. Don haka sai aka rinqa kawo masa
abinci, komai aka kawo masa irin su tuwo da shinkafa da fura duk sai ya ce ba
zai iya ci ba saboda rashin lafiya.
Ana haka sai wani abokin ‘ya’yan
wannan dattijo ya zo dubiya, ya ga duk abin da aka ba shi ya qi ci, sai ya ce
“To a samo masa hanta mana da qwai da naman kaji a gani ko zai ci.”
Suruf Dattijon nan ya miqe zaune
ya ce “To sun iya wannan abin arziqin ne. Ba sai dai su yi ta neman kashe ni da
tuwo da kunu ba.”
INA FA
ALLAH YA KIYAYE?
W
|
ata Bafulatana ce ta xauko kayan nono tana sauri za ta
kasuwa, ba ta ankara ba ta yi kicivis da wani mutum ta hankaxe shi, nonon ya
zube qorai suka fashe. Mutumin nan ya dudduba ya ga nonon bai vata kowa ba, sai
ya ce “Kai amma fa Allah ya kiyaye.”
Da jin haka sai Bafulatana ta ce
“Haba Malam, ina fa Allah ya kiyaye nonona ya zube.”
BAN NA
GOMA...
W
|
ani Xanfulani ne ya je kanti ya ce a bashi lemon kwalba. Mai
kantin ya ce Naira saba’in ne.
“Yo ba zan iya shiya ba ne, maza xauko
wa Fullo.”
Aka xauke masa aka buxe masa
lemon, yana gani gas ya taso ta cikin kwalba, sai ya yi sauri ya ce “Kai aradun
Allah ya yi min yawa, xauko leda ka ban na goma.”
IKON ALLAH, YAU KUMA RUWAN NAMA
AKE YI
K
|
wana biyu da yin babbar sallah wani Kaxo ya kai ziyara gidan
surukansa, bayan sun gaggaisa aka kawo masa nama cike da kwano. Sannan aka ba
shi wuri. Kaxo ya yi ta gabzar nama ba ji ba gani har ya qoshi. Da ya tashi
tafiya ya rasa yadda zai yi, sai ya xauki ragowa naman nan ya sauke hularsa ya
juye a ciki.
Sannan ya fito tsakar gida don
tafiya, ya durqusa da qyar ya ce “To Inna, Baba ni zan tafi. Allah ya maimaita
mana.”
Suka amsa amin. Ya miqe zai tafi
sai ga nama yana zubowa ta hularsa, cikin sauri Kaxo ya wage baki yana cewa,
“Ikon Allah yau kuma ruwan nama ake yi. Kai Allah mun gode maka.”
Surukan nan nasa suka rasa yadda
za su riqe dariya, kawai sauka qyalqyale da dariya.
NA YI MIKI DODO KO?
W
|
ata rana wani mutum matarsa ta yi yaji, shiru-shiru ba ta
dawo ba, har tsawon mako guda, sai ya shirya ya niqi gari ya tafi qauyen matar
tasa. Bayan ya isa sun gaisa da surukarsa, ya huta, sai ta kawo masa fura cike
da langa, domin ta lura ya jin 'yar bahuwa.
Da fitar surukar tasa sai wannan
mutum ya miqe ya leqa, sai da ya tabbatar ta bar wurin, sai ya rinqa tsalle
yana rawa yana cewa "In sha fura, sannan kuma a ba ni matata in tafi da
ita. Lallai ni mai nasara ne." Yana tsalle bai lura ba, sai ya daki langar
furar nan, take ya faxi, fuskarsa ta faxa kan langar nan, fuskarsa ta yi buya-buya
da fura.
Hankalinsa ya tashi, ya duba gefe
ko zai ga ruwa ya wanke, bai ga ruwa ba, ya duba ko zai ga tsumma ya goge, nan
ma babu. Yana cikin wannan halin sai ga surukar tasa ta dawo, ta kawo masa
ruwa. Kawai sai ta ga wannan abin mamaki, ta yi turus tana kallonsa cikin
mamaki da tsoro.
Shi kuma ganin zamiya ta qare,
sai ya dubi surukar tasa ya yi tsuru yana kaxa gashin baki yana faxin, "Na
yi miki dodo ko? Na tuna lokacin muna yara ne."
Surukar nan tasa ta saki ruwa ta
yi waje tana faxin "Surukin namu ya haukace."
KO'INA AKWAI NA ALLAH
W
|
atarana wani Alhajin Birni, gogaggen xan bariki ya je wani
gidan karuwa don hutawa, sai ya tarar da karuwan gidan da 'yan daudu da manema
duk a cikin wani hali, sun yi jugum-jugum, sai ya rava ya tambayi wani mai
siyar da sigari da ke gefe ya ce.
"Kai yau me yake faruwa a
gidan nan, gidan da na saba ganin ana shargalle da harkoki?"
Mai sigarin ya ce "Ai Alhaji
yau kusan sati guda kenan babu harka, babu kuxi a gari babu dalilin samunsu shi
ya sa ka ga haka."
Alhajin Birni ya yi dariya ya
zaro kuxi ya rinqa rabawa kowa yana cewa "A tashi a sha sha'ani a yi
shargalle da kalelesuwa."
Wani xan daudu da ke gefe cikin
jin daxi ya dubi Alhajin Birni ya ce "Allah mai iko, a ko ina akan samu na
Allah."
Alhajin nan ya harare shi ya ce,
"Ni ba na Allah ba ne, na shaixan ne."
MAHASSADANKA FADAWANKA
W
|
ani maroqi ne ya zo wajen wasu fadawa, ya yi ta roqonsu su ba
shi dama ya yiwa sarki kirari ko ya samu 'yar taguwa. Da qyar suka qyale shi
bisa sharaxin idan ya samu zai basu wani abu.
Sarki na zaune maroqi ya je ya
fara koxa shi Fadawa na cewa "Gaskiya ne wannan."
Maroqi na cewa "Taka gaba
salamun xan toron giwa, zamanka lafiya tashinka lafiya mai taqama da girman
Allah, kai kaxai gayya..."
Fadawa na faxin "Daidai
ne."
Can sai Maroqi ya manta ya ce
"Mahassadanka sai sun ji kunya, Xan Marayan zaki, mahassadanka fadawanka
Sarki."
Fadawa suka yi caraf suka ce
"Hattara mahaukacin Maroqi, ashe ba ka warke ba, hattara, a yi waje da
shi."
Suka cafe shi yana zillo suka yi
waje da shi.
AKUYAR
NAKE YIWA RUKIYYA
W
|
ani saurayi ne xan qarya, wanda ake kira da suna Xanhutu,
kullum idan ya je wajen 'yanmatansa sai ya yi ta zabga musu qarya yana nuna shi
wani ne, mahaifinsa mai tarin kuxi ne da sauransu.
A cikin 'yanmata Xanhutu akwai
wata mai suna Ladidi, mahaifinta ya ce ta fito da mijin aure, don haka ta yi ta
jira Xanhutu bai zo ba, sai ta je gidansu nemansa, tun da aka kwatanta mata
gidan ta ga irin gidan talakawa ne sai jikinta ya yi sanyi, amma kuma ba ta
same shi ba, don haka watarana sai ta yi sammako ta je da sassafe don tana sa
ran samunsa.
A daidai wannan lokacin Xanhutu
yana kwance a inda yake kwana a qofar gida, a kan tsohuwar yagaggiyar tabarmar
kaba, da wani cuburbuxaxxen tsohon bargonsa, a gefensa kuma akuyarsa ce kwance
a jikinsa, daman haka kullum suke kwana. Da Ladidi da qawarta suka zo wajen aka
ce musu shi ne a kwance sun yi mamaki, har Ladidi ta yi fushi ta cewa qawarta
kawai su tafi, sai qawar ta ce "Ai bai kamata mu zo ba, kuma mu tafi ba
tare da mun yi magana da shi ba."
Don haka qawar Ladidi ta fara
qoqarin tashinsa, har ya farka, Xanhutu yana tashi da ya lura budurwarsa ce
Ladidi kawai sai ya yi sauri ya jawo kan akuyar nan ya dafa ya fara karatu yana
cewa "A'uzu billahi minash shaixanir rajim, fita ku fita na ce, ku fita
A'uzu billahi...."
Qawar Ladidi ta qyalqyale da
dariya, ita kuma Ladidi ranta ne ya vaci ta dube shi ta ce "Me kake yi
kenan?"
Xanhutu ya vata rai ya ce
"Ruqiyya nake yi mata, kin san muna yiwa mutane da dabbobi ruqiyya, idan
zamu yiwa dabbobi ruqiyya dole sai kin ganmu a cikin wannan yanayi na dauxa da
qazanta."
Ladidi ba ta san lokacin da ta
fashe da dariya ba.
XAN WANKA
DA LADAN
W
|
atarana ne Xanwanka ya shiga gidan wata mata kwartanci, suna
zaune suna hira kafin su fara sha'ani, sai suka juyo sallama, suka tsorata,
take matar ta ce "Ga maigida nan."
Da sauri ta xaga qasan gado ta ce
Xanwanka ya shiga, ya yi sauri ya shige. Sannan ta ba wa mai sallamar damar
shigowa, ashe wani kwarton nan Ladan ya zo, ta sauke shi, suka zauna suna hira,
ba su daxe da fara hirar ba sai suka jiyo wata sallamar.
Gaban matar ta tashi, domin ta
san wannan lokacin Maigidan nata ne ya zo, don haka ta cewa Ladan ya ya za a
yi? Kafin Ladan ya yi magana, kawai sai ya Ladan ya xaga qasan gado ya afka.
Kawai sai ya yi kicivis da gashin
bakin Xanwanka buyu-buyu a qarqashin gadon. Daman Xanwanka da Ladan ba sa ga
maciji, kullum cikin faxa suke. Xanwanka ya harari Ladan.
"Allah ya kamaka yau ka
shigo hannuna, sai yadda na yi da kai."
Ladan ya ce "Kai dai Allah
ya kama don na san za ka zo, shi ya sa na shigo nan don in kamaka in kawo
qarshen iskancinka da rashin mutuncin da kake yi min."
Xanwanka ya ce "To mu fita
mu ga wanda aka kama." Ya daqumi kwalar Ladan.
Ladan ya yi sauri ya ce "Kai
kai kai, kai wane irin mai taurin kan mutum ne."
Maigida yana tsaye yana jin
wannan cacar bakin daga qarqashin gadonsa, sai ya dubi matarsa ya ce "Me
yake faruwa a gidan nan ne?"
Matar ta dube shi ta ce
"Haba maigida rediyo na kunna ake yin wasan kwaikwayo."
Maigida ya ce "A qarqashin
gadon nawa ake wasan kwaikwayo?"
Kafin ya rufe baki Xanwanka da
Ladan suka yi wuf suka fito suna cewa "Qwarai kuwa bari ma ka ga yadda ake
faxa a wasan kwaikwayon."
Ladan ya zabgawa Xanwanka mari ya
ruga da gudu, Xanwanka ya rufa masa baya yana ihu.
Maigida ya saki baki yana kallon
abin mamaki.
NAWA NE
KUXIN AURE
W
|
ani saurayi ne yake son aure, ya rasa yadda zai tambayi
mahaifinsa, sai watarana suna zaune, sai ya yi dabara, ya ce "Abba wai ko
kuxin aure suna kaiwa nawa?"
Mahaifin nasa ya dube shi ya
kawar da kai ya ce "Ban sani ba."
Yaro ya yi mamaki, ya ce
"Abba ya kamar ba ka sani ba?"
Mahaifin ya yi dariya ya ce
"To ai har yanzu biya nake yi. Ko ba ka ganin kullum sai na ba
mahaifiyarka kuxi."
DA FATAN
BA KA KALLON NAWA
A
|
wata makarantar boko, Malamin lissafi ya rubutawa xalibai
jarabawa, sai ya ke kewayawa don kar a samu wani ya satar amsa. Sai ya hango
Isa kamar yana leqa littafin Ali da ke zaune kusa da shi, sai ya dube shi ya
ce, "Isa da fatan ba jarrabawar Ali kake leqawa ba?"
Isa ya kalli Malam ya ce
"Kai ma Malam da fatan ba tawa jarrabawar ka leqa ba."
AI SHI YA
SA NAKE KUKAN
W
|
atarana wani magidanci da matarsa suna kwance, kawai sai
matar ta yi mafarki, sai ta tashi tana kuka, maigidan ya tashi hankalinsa a
tashe yana tambayarta.
"Uwargida me ya faru ki ke
kuka da tsakar daren nan?"
Sai matar ta kada baki ta ce,
"Mafarki na yi wani hamshaqin maikuxi ya sace ni, ya gudu da ni."
Maigida ya yi murmushi ya ce,
"Ki daina kuka ai mafarki ne kawai."
Matar ta harare shi ta ce,
"Ai saboda mafarki ne shi ya sa nake kuka, ina ma gaske ne."
Idan kai ne maigidan ya za ka yi?
MISS CALL
W
|
ata mata ce kullum idan tana waya sai ta yi awa bakwai awa
takwas zuwa goma sha tana waya, kullum cikin karvar kuxi take a wajen mijinta
don ta sayi katin waya. Haka nan idan aka kirata a waya ma sai ta yi sama da
awanni ashirin suna waya.
Da mijin ya gaji da wannan cacar
kuxin sai ya sata a gaba ya kai ta wajen iyayenta suka yi mata nasiha don ta
daina.
Washegari suna zaune suna hira,
sai ga kira ya shigo wayar wannan mata, ta xauka tana duban mijinta, sannan ta
koma gefe tana magana. Cikin ikon Allah wannan lokacin ba su fi mintuna arba'in
ba ta kashe wayar.
Mijin ya yi murmushin jin daxi,
don da alama matar tasa ta ji faxan iyayenta, ya dubeta ya ce "Yau ba ki
daxe a waya ba, kin ji nasiha kenan."
Matar ta yi dariya ta ce "Ai
miss call ne."
To mu haxu a littafin ABOKIN
DARIYA da GIDAN DARIYA da 'YA'YANMU
NakuKabiru Yusuf Fagge (anka)
07030319787
NEMI LITTAFAINA
·
KAI MA KA DARA
1-2
·
GIDAN DARIYA
·
LABARIN SARKIN
KARYA
·
ABOKIN DARIYA
·
MALAMIN
BAN-DARIYA
·
LABARUN HIKAYA
DA HIKIMOMIN HAUSAWA
·
TATSUNIYOYI DA
LABARUN HIKAYA
·
ZUNBULI KAKAN
MAROWATA
·
MU KOYI KARATU
1,2,3
·
‘YA’YANMU
·
DABARUN RUBUTA
KAGAGGUN LABARAI
NA KU: KABIRU YUSUF
FAGGE (ANKA)
07030319787
Nemi littafin'YA'YANMU
Domin ka sha labarin ban tausayi, mamaki da ban haushi na
'ya'yan Hausawa.
No comments:
Post a Comment