KUDIN KORONA
Gajeren Labari
Rubutawa: Kabiru
Yusuf Fagge
Na yi sharkaf da
gumi, saboda irin yadda tun safe nake ratsa unguwanni da kasuwanni a cikin
rana, abin ne ya hadar min goma da ashirin, ga rashin kudi, ga rana, ga shi
mutane sun ki siyen maganin beran da nake tallan.
A wannan hali da ake
ciki mutane ba ta maganin bera suke yi ba, ta abincin da za su ci suke. Fatan
da nake yi in samu wadanda ko tayawa su yi in karyar musu in sami abin da zan
ci ni da iyalina.
A kwanar shiga
unguwar Fagge, n a ji wasu matasa suna hira, hirar ta ja hankalina na koma gefe
na rakube ina sauraronsu.
"Da farko duk
mutum daya mai cutar Korona idan yana da iyali za a kai mi shi kayan abinci,
buhungunan shinkafa da taliya da sauran kayayyaki, sannan kuma ana ba shi
N80,000 a kullum..."
Ban gama jin
karashen zancen ba na tashi ai guje tare da yankewa zuciyata abin da zan yi.
"Gida zan je,
in ajiye kayana, ina da lambar hukumar NCDC in kira su, su zo, su tafi da ni,
don a killace ni."
A gida ban yi wa
matata bayani ba, na ari N100 a wurinta na sa a wayata, na fara kiran lambar
hukumar, amma na yi kira ya fi sau shurin masaki ba a dauka ba. Dole na gaya wa
Hauwa halin da ake ciki.
"Haba maigida
kawai don kana mura da zazzabi sai ka kai kanka wurin nan a zo ana kyamar mu.
To wane ne baya yin murar..."
"Tawa ba irin
taku ba ce, ke dai ko da an zo gare ku, ki ce sati na daya a killace a daki,
yau ne ana kira ba a zo ba, shi ne na tafi." Na ce mata, tare da kwantar
mata da hankali.
"Ai shi ke nan.
Batun abinci fa?"
"Za a kawo
muku."
"Wane ne zai
kawo, aikowa za ka yi?"
"HUkuma da
gwamnati ne za su kawo, ki kwantar da hankalinki, haka ake yi wa duk wanda aka
killace."
"To ko dai
akwai abin da kake shiryawa ban sani ba?"
"Ba wani abu,
bari in je kar ki bata min lokaci."
Na fita da sauri.
Daga unguwar Koki zuwa asibitin Malam Aminu Kano inda ake killacewa tafiya ce
mai nisa, kuma ga shi ba ni da kudi. Amma faduwa ce ta zo daidai da zama, a
kasa na tafi, domin yin hakan ma wata ribar kafar ce.
Ina zuwa, na tambayi
bangaren 'yan koronar, daga nesa-nesa aka nuna min, na isa wajen wujiga-wujiga
da ni, likitar da ta gan ni, tun kafin in kammala bayani ta tausaya min, nan aka shiga auna ni, take aka tabbatar
temperature ta, ta yi sama, kuma ian tare da korona.
Na yi dariya a
raina, na ce "Ba su san tsabar dukan sayyada da yunwa da tension ne suka
harzuka temperature tawa ba, suke ganin kamar ina da koronar."
Bayan rubuce-rubuce
na suna da inda nake da sauransu aka ba ni gado, tare da hada ni da abinci.
Lokacin da na
kammala cin abinci na nutsu da a ce a lokacin za su sake auna ni da za su
tabbatar kalau nake don tuni temperature ta din tawa ta sauka. Sai lokacin ma
na lura da mutane ukun da suke dakin, daya dattijo ne, biyu matasa, suna
kallona. Daya ne daga matasan ya matso kusa da ni.
"Kai ma an kawo
ka ke nan?" Ya ce da ni.
"A'a, ni na kwo
kaina."
Suka yi min wani
irin kallo.
"E mana, ni na
kawo kaina don in tserar da wasu."
Zancen nawa bai kai
zuci ba.
Bayan kwana biyu,
ban ji zancen kudi ba. Na fara tunanin ko dai sai mun yi mako biyun za a hada
mana a ba mu. Ban yi zurfinc iki ba, na tambayi daya saurain nan mai suna
Nazifi.
"Wai ba kullum
ake biya ba?"
Nazifi ya kalle ni.
"Kullum ana
cirewa duk mai cutar wasu makudan kudi."
"Yawwa, to
yaushe ake bayarwa?"
"Malam ba kai
za a bai wa ba. Ni dai na san ana cirewa ko kakshewa duk wani mai korona
kudaden nan, watakil haka ake kashewa mutum ke nan."
"To me ake
kashe mana? Tun da na zo ni dai na san ana ba ni abinci mai kimar, N250 sau uku
sai kuma bitamin C da ake ba mu, mu sha, da shawarwarin kare lafiya da ake gaya
mana, ko ana mana abin da ya wuce hakan?"
"Wadannan
abubuwan da ka lissafa su ne naka, sauran na masu aiki ne da wadanda ba mu sani
ba. kai dai tund aan kai ma abinci gida, to Allah ya ba mu lafiya."
"NI kam lafiya
ta lau." Na ce a raina, "Kawai ina fama da rashin lafiyar aljihu ne,
na so na magance ya sa na kawo kaina, ashe akwai wadanda suke gabana masu son
magance matsalar aljifansu."
Wannan ma a zuci na
yi ta fada, ashe zancen ya fito fili.
Suka kyalkyale da
dariya, Dattijon ne ya yi magana.
"Yaro idan kai
sammako ka yi to mutanen nan a tafe suka kwana. Maganar gaskiya, duk mutum daya
ana kashe masa kudi da yawa a matsayin mara lafiyar korona, inda kudin ke
tafiya ne ni ban sani ba, sai Allah."
Ya dan yi shiru.
"Dazu na ji a labarai
gwamnatin jihar Lagos na cewa, tana kshe N50,000 ga gwaji na kwoane mutum daya
da yake da cutar. Sannan kamar yadda kake tsammani, kuma kowa yake fada a
kullum ana ware makudan kudade ga mai cutar tare da kashewa a rubuce ba aikace
ba." Daya saurayin ya ce.
Ina shirin yin
magana, Dattijo ya riga ni.
"Ai kai dai ka
zama kadara, ka gode Allah za ka tsira da kayan abinci da aka kai
gidanka."
"Ai kuwa
wallahi guduwa zan yi."
"A banza don
kuwa ka riga, ka shiga cikin lissafi, ka hutar da su."
Muka yi jugum cikin
damuwa.
-Kabiru Yusuf Fagge.
Da kyau Allah ya ƙara fikrah
ReplyDelete