Tuesday, May 26, 2020

DABARUN RUBUTA GAJEREN LABARI



DABARUN RUBUTA GAJEREN LABARI
Kabiru Yusuf Fagge

-Da yawan marubuta da masana sun bayyana hanyoyi da dabarun rubuta gajeren labari, kowannensu ya kawo irin hangensa, kuma da yawa suna taimakawa marubuta wajen kwarewa ga rubuta gajeren labarin.
-A nan, ni ma na dan leka inda ya kamata, na tattara tunanin wasu masana da marubuta don taimaka wa 'yan'uwa marubuta. A sha karatu lafiya.


GAJEREN LABARI
-Gajeren labari na nufin labari ne da zarar marubuci ya fara shi sai yiwuwar zuwa kololuwa sai karshe - don komai a kuntace yake, ba kamar littafi ba da marubuci zai yi ta sukuwa yana zamiya.
-Gajeren labari yana makale da taurari ne da abubuwan da ke faruwa a cikinsa, cikin mayar da hankali ga taratsi ko rigima guda daya tare da cigaba da faruwa ba tare da tsammani ba.
-A haka marubuci zai ci gaba da tafiyar da labarin yana dan gutsiro 'yan wasu abubuwa na rayuwar taurarin - masu karatu ba sa bukatar sanin komai da komai da kai marubuci ka sani game da taurarin naka ba.
 *Gajeren labari yana farawa ne daga kalmomi 1,500 zuwa 5000. (amma ana iya yin kasa da haka)

IYA RUBUTA GAJEREN LABARI
Rubuta gajeren labari kwarewa ce, duk da cewa akwai takaita abubuwa fiye da littafi. Ga wasu hanyoyi da za a bi wajen rubuta gajeren labari yadda ya kamata:
(1) Marubuci ya yi tunanin yadda labarin yake, me zai faru a labarin. Ya tabbatar da sanin abin da labarin ke kunshe da shi.
Misali:
-marubuci ya fara bayar da labarin yadda babban tauraronsa zai tunkari wani mummunan yanayi ko abu - ko kuma wani abu da ya dirar wa rayuwar babban tauraronsa bakatatan ba shiri.
-ko kuma wani abu mai rikitarwa
(Idan kuma an ba marubuci jigon da ake son ya yi rubutu a kai, shikenan sai ya fara da gabar da za ta ja hankali kai tsaye)

(2) MATSALAR BABBAN TAURARO
-Marubuci ya mayar da hankali wajen matsalar babban tauraro, -me babban tauraro ke bukata da kuma irin tarnakin da ke gabansa. Domin yawancin gajerun labarai sukan mayar da hankali ga babban tauraro daya ko biyu ne.
-Marubuci ya tsara babban tauraronsa ya zama gagarabadau ko ko'ina-akan-zace shi a gan shi. Kar ka mayar da shi sassauka, ko kuma mawuyaci.

SAMAR DA TAURARI MASU SHIGA RAI
A baya, mun yi darasi guda a a kan taurari saboda muhimmancinsu a labari, amma ga wani dan kari kamar haka:
-A matsayinka na marubuci ka nazarci yadda rayuwar mutane daidaiku suke da yadda suke gudanar da al'amuransu na yau da kullum, wani mai fushi ne, wani mai sanyin rai ne, wani mai saurin magana ne, wani shiru-shiru ne da sauransu.
-Sanin ainihin rayuwar taurari da ta gabata. (backstory)
-Kirkirar tauraro ko tauraruwar da za ta iya tafiyar da labarinka ba tare da tasgwaro ba. (Misali, tauraronka raggo ne a labarin jarumta, wannan zai bai wa labarin matsala.)

(3) KIRKIRAR TARATSI
Marubuci ya kirkiri taratsi (rashin jituwa ko rigima) ga babban tauraronsa.
-Kowanne kyakkyawan labari yana tare da taratsi (rashin jituwa/rigima) wanda babban tauraro yake tunkara a matsayin matsala.
-Marubuci ya fara da taratsin tun da farko-farko a gajeren labarinsa.
-Marubuci ya sa tauraronsa a cikin mawuyacin hali ko taratsi.
Misali: watakil babban tauraron yana son fita daga cikin wani mawuyacin halin da yake ciki, yana neman yadda zai yi ya tsira da rayuwarsu.

(4) KA ZABI GURBI (WURI) DA LABARIN YA FARU
-Wani muhimmin abu a gajeren labari shi ne gurbi (wuri, muhalli/gari/nahiya) da labarin ya faru ko ace afku.
-Marubuci ya samu gurbin da ya dace da labarinsa, wanda ya gamsar da shi, kuma ya tabbatar zai gamsar da masu karatu.

HANYAR TSARA GURBI (WURI) A LABARI
-Marubuci ya tsara inda (gurbi) labarin zai faru, ya tabbatar ya dace da labarin yadda ya kamata.
Misali: idan babban tauraron marubuci masunci ne, kuma labarin yana da alaka da sana'arsa, to yana bukatar gabar ruwa ne (kogi ko tafki dss), kar ka yarda a gan shi a bakin tasha, ko a gan shi a sinima, ko a gan shi a filin kwallo dss, idan har ba wani muhimmin abu ba ne a labarin.
-Kar marubuci ya samar da tarin wurare da gajeren labarin zai faru, hakan zai sa mai karatu ya kasa fahimtarka.

(5) KA YI TUNANIN JIGO GUDA DAYA
Yawancin gajerun labaru ba sa wuce jigo guda daya, kamar "soyayya", "fyade", "cin hanci da rashawa" da sauransu. Sannan ka yi nazarin jigo a kan babban tauraronka.
A kan iya  sayyade jigo da kamar "soyayyar matasa" ko "fyade ga matan aure" da sauransu.
Idan kuma bai wa marubuci jigon aka yi, kamar a ce ka yi rubutun gajeren labari a kan "sata" to sai marubuci ya yi nazarin jigon tare da yadda babban tauraronsa yake.

(6) TSARA KOLOLUWA MAI JAN HANKALI
-Kowanne gajeren labari yana da lokacin da babban tauraro ke kai wa kololuwa a labari (inda babu abin da yake nema sai mafita)
-Sau tari kololuwa na faruwa ne a kusa da kusan karshen labari ko wajen rufe labarin.
-A wannan lokacin ne babban tauraron labarin yake samun kansa cikin tsanani, ko cikin sarkakiya, ko cikin tsananin damuwa, ko ma ya fita daga hayyacinsa.
Don haka a nan marubuci zai nuna kwarewarsa wajen warware da rufe labarinsa. Idan ya yi batan kai, sai labarin ya lalace, idan kuma ya yi rufewa mai kyau, shikenan labari ya yi armashi.

(7) KARSHE (RUFEWA) MAI BAN MAMAKI
-Marubuci ya wasa kwakwalwarsa cikin tunanin yadda zai bai wa masu karatunsa mamaki, ya bar su cikin al'ajabi da zuwa da abin da ba su yi tsammani ba cikin gamsarwa a gajeren labarinsa.
-Kar ka yarda mai karatu ya kintaci yadda karshen labarinka zai kasance, kuma ya kasance hakan.
-Ka ba mai karatu kafa, yana tsammanin yadda labarin zai kare, sai ka ba shi mamaki, ya kare a yadda bai zata ba.
-Yadda za ka yi hakan kuwa shi ne; ka tsara yadda karshen labarin zai kasance a ranka, kuma ka tabbatar ya yi yadda ya kamata, sannan zai gamsar, ya zo da abin mamaki.
-Ka kiyayi karshe labarin mara gamsarwa ko kyau, gabadaya yake kashe labari.

(8) KARANTA GAJERUN LABARAI
Abu na karshe, kuma na farko shi ne, ka zama mai yawaita karance-karancen gajerun labaru, na kowanne jigo kana nazari da fahimtar yadda sauran marubutan suke amfani da taurarinsu, da jigonsu, da salonsu, da gurbi da tsarinsu yadda ya taimaka wa gajeren labarin gamsar da mai karatu.
Na gode
Kabiru Yusuf Fagge

INA TAFE DA SHARHIN JIGON GASAR DAILYTRUST. YADDA MARUBUTA ZA SU FAHIMCI RUBUTUN DA ZA SU YI
Manazarta:
Mukhtar, I  (2004) "Jagoran Nazarin Kagaggun Labarai." Usman Al'amin Publishers Company, Kano.
Bunza, A.M. (2002) "Rubutun Hausa: Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa. Don Masu Koyo Da Koyarwa." Ibrash Islamic Publications Centre LTD., Surulere, Lagos.
Indabawa, I.M da Fagge, K.Y (2000) Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai." Gimbiya Publishers, Fagge, Kano.
Zarruk, R.M. da wasu (2010) "Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Kananun Makarantun Sakandire." Ibadan Press Plc, Ibadan Nigeria.
Fagge, K.Y. (2020) "Rubutunka Tunaninka." AGF Multimedia Nig. Ltd., Kano.

1 comment:

  1. Na karu da abubuwa masu dama a ciki, daga yanzu zan san yadda zan fuskanci gajeren labari sosai.

    ReplyDelete

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...