Saturday, April 11, 2020

GASAR GUSAU INSTITUTE KADUNA, KARIN LOKACI

*KARIN LOKACIN TURO DA TSAKUREN LABARI NA GASAR MARUBUTA HAUSA NA ALIYU MOHAMMED RESEARCH LIBRARY, GUSAU INSTITUTE (GI) KADUNA*
Biyo bayan bullar cutar Covid-19 watau corona virus a fadin duniya. Hukumar Gusau Institute sun kara lokacin turo da tsakuren labaran masu sha’awar shiga wannan gasa, zuwa 31 ga watan mayu na 2020 (31 May 2020), domin bama sauran marubuta daman turo da tsakuren labarin su.
Cibiyar Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute (GI) Kaduna ke shirya wannan gasa, da kuma ba da kyaututtukan kudade domin tallafawa marubutan adabin Hausa.
Gasar da ake yin ta a kowace shekara, tana daukar siffa da tsari na kagaggun labarai ko wasu irin labaran adabin Hausa.
Ga masu sha’awar shiga wannan gasa, ana bukatar marubuta su kiyaye da wadennan ka’idoji da dokoki:
1. Ana bukatar marubuta su aiko da tsakuren labarinsu shafi goma watau 10 Pages (Tsarin taypin na komfuta samfari Microsoft Word watau MS Word ko PDF) zuwa ga adireshin email: info@gusauinstitute.com ko gusau.institute@gmail.com ko ta WhatsApp Number: +2347087808036
2. Dole ne cikkaken labarin da za’a turo a gasar ya kai kalmomi dubu arba'in (40,000) zuwa dubu arba'in da biyar (45,000).
3. Duk marubuci ko marubuciya da basu kai shekara sha takwas ba, ana bukatar su da su turo da shaidar izini ko amincewar iyayensu domin shiga gasar.
4. Ba a yarda wani ko wata daga cikin ma’aikatan Gusau Institute ko danginsu su shiga wannan gasa ba.
5. Ba a yarda a turo da labarin da aka taba bugawa, ko aka taba karantawa a daya daga cikin kafofin watsa labarai.
6. Ba’a yarda ayi satar fasahar wani ba ta hayyan turo da rubutun wani a gasar.
7. Duk wanda ya shiga wannan gasar, to ya kwana da sanin cewa duk abinda alkalan gasar suka zartar shine daidai kuma babu daukaka kara.
8. Za a turo da ID Card Mai dauke da hoton marubuci da kuma cikkakken adireshi.
9. Duk labarin da marubuta suka turo, babu hurumin canza wani fasali ko tsari labarin.
Mungode.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...