Friday, May 15, 2020

Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa Ta AMINIYA-TRUST 2020




Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa Ta AMINIYA-TRUST 2020

 


GABATARWA
Hukumar Gudanarwa ta GANDUN KALMOMI tare da haxin gwiwar OPEN
ARTS, Kaduna, na kira ga masu sha’awa zuwa shiga GASAR RUBUTUN GAJERUN LABARAN HAUSA TA AMINIYA-TRUST, TA SHEKARAR 2020.
Wannan sabuwar gasa ce ta rubutun gajeren labarin Hausa ta jaridun AminiyaTrust da ake fatar ta kasance wata kafa ko dama domin bunkasa rubuce-rubucen adabi cikin Hausa da za a dinga gabatarwa kowace shekara, karkashin kulawar GANDULKALMOMI da OPEN ARTS da ke Kaduna.

MAUDU’IN SHIGA GASA
Ba kamar saura gasa da aka saba yi a baya ba, wannan gasa za ta dinga zuwa da maudu’i na musamman da ake so masu shiga gasar su gabatar a cikin labaran nasu. Maudu’in wannan shekara ta 2020 shi ne MATSALOLI MULKIN DIMOKURADIYYA DA DAMBARWAR SIYASA A NIJERIYA.
Saboda haka ya zama dole masu shiga gasar su tunkari wannan batu a
cikin labarin nasu ta irin fuskar da suka ga dama, sai dai ana son labarin ya kasance an tsara shi ne ta fuskar ayyanawa, ba abin da ya faru a zahiri ba ko kuma a fassaro shi daga wani harshe ko wani rubutu na daban ba.

YAWAN KALMOMIN GAJEREN LABARIN
Kowane labari ana son kada ya gaza kalmomi 1,000, kada kuma ya wuce kalmomi 1,500, a kuma kayata shi da ka’idojin rubutun Hausa da salo mai birgewa, a kuma tabbata ba a jefa batsa ko wasu kalamai masu iya tada hayaniya ko tashin-tashina ba.

SU WA ZA SU SHIGA GASAR?
An shirya wannan gasa ne domin matasa, MAZA da MATA daga ko’ina suke a fadin duiya, sai dai dole su kasance ‘yan shekara 18 zuwa 35. Ga wadanda ke sha’awar shiga gasar ta hadin gwiwa, to kada su wuce mutum biyu, maza ko mata ko kuma a cakude.
Idan an kammala gasar, za a buga gajerun labaran da suka yi zarra daga na 1 zuwa a 15 a matsayin littafi don adanawa da kuma sayarwa da rarrabawa domin amfanin al’umma.

INA ZA A TURA GAJEREN LABARIN?
A tura gajeren labarin zuwa ga: wasikunaminiya@dailytrust.com tare da cikakken suna da dan takaitaccen bayanin mai shiga gasar da jawabi game da gajeren labarin da kuma adireshin gida ko ofis da na imel da lambar waya.

YAUSHE ZA A BUDE DA RUFE GASAR?
Za a bude amsar gajerun labarun gasar daga ranar 15 ga Watan MAYU, 2020, a kuma rufe karba daga sha biyun daren ranar 15 ga watan YULI, 2020. Duk gajeren labarin da ya zo bayan wannan lokaci da ranar da aka aje, ba za a bi ta kan sa ba.

WACE AWALAJA ZA A SAMU DAGA SHIGA WANNAN GASA?
Wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku ne kawai za su sami garabasar kyauta ta kudi kamar haka:
Na daya, Naira 250,000
Na biyu, Naira 150,000
Na uku, Naira 100,000
Bayan kammala gasar, za a buga gajerun labaran 15 da suka yi zarra a matsayin littafi, za a kuma ba marubutan labaran satifiket da wani kaso (da za a aminta da shi nan gaba) na littattafan kyauta.

JADAWALIN AIWATAR DA GASAR
• Daga 15 ga watan Mayu, 2020 za a bude damar shiga gasar, a kuma rufe karbar gajerun labaran daga 15 ga watan Yuli, 2020.
• Daga ranar 15 ga Watan Yuli 2020, za a fara tantance wadanda suka turo da labaransu, inda za a zabi guda 25 da aka tabbatar sun yi zarra.
• A mataki na biyu, wasu zabbabun masana gajerun labarai za su sake tatancewa su fitar da gajerun labarai 15.
• A cikin watan Agusta, 2020, za a tura wa alkalai 3 da aka zaba da gajeru labaran 15 su tantance na 1 zuwa na 15.
• A farkon watan Satumba 2020, za a bayyana wadanda suka lashe gasar baki daya, wato daga na 1 zuwa a 15.
• A cikin watan Satumba da Oktoba za a tace wadannan gajerun labarai guda 15, a kuma wallafa su a matsayi littafi, a kuma fassara na 1 zuwa na 3 zuwa Ingilishi don watsa wa duniya ta gani.
• A watan Nuwamba, 2020, za a yi hira da wadanda suka lashe gasar, wato na 1 zuwa na 15, da za a buga a cikin jaridun AMINIYA da
TRUST da kuma turakar GANDUN KALMOMI da OPEN ARTS, a Intanet.
• A watan Disamba, 2020 za a yi bikin karramawa da bayar da kyaututtuka ga zaratan wannan gasa, a Kaduna.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...