Thursday, March 26, 2020

WANI ABU A KAN MATAR SARKI



Idan baka taba karanta littafin WANI ABU A KAN MATAR SARKI ba, to wannnan lokaci na annubar CORONA VIRUS shi ne lokacin da yafi cancanta ka karanta.
WANI ABU A KAN MATAR SARKI littafi ne dake ilimantarwa a kan yanda mutum zai kiyaye lafiyarsa da ma rayuwarsa ta hanyar yin riga kafin kamuwa da rashin lafiya a dalilin kwayoyin halittu kamar irinsu CORINA VIRUS.
Littafin yana koyar da yanda mutum zai tsare kansa daga hare-haren 'ya'yan halittu kamar CORONA VIRUS da kullum muke tare dasu a cikin abincinmu, ruwan shanmu da ma jikinmu. Ba ma iya ganin 'yan'yan halittun da kwayar idonmu, sai da taimakon na'ura mai girmama abu (microscope).
WANI ABU A KAN MATAR SARKI littafi ne na tatsuniyar kimiyya (science fiction) irinsa na farko da aka rubuta da harshen Hausa. Farfesa Faruk Sarkinfada na sahen Ilinmin 'Ya'yan halittu na jami'ar Bayero ya rubuta. Ya fassara sa daga na Turancinsa mai suna A MICROBIOL WORLD: MYSTERIOUS JOURNEY wanda masanin kimiyyar ne dai ya rubuta. Ya fassara sa ne domin amfanuwar al'ummar Hausa. Ya fassarasa ne izuwa Hausa domin amfanuwar Hausawa, musamman a lokacin annobar CORINA VIRUS irin wannan.
WANI ABU A KAN MATAR SARKI littafi ne da marubucin ya rubutasa a salon barkwanci domin isar da sako ga mai karatu ba tare da gajiyar da kwakwalwarsa ba.
Idan baka karanta littafin ba, to me kake jira? Domin mallakar na ka, hanzarta:
1) Sadaraki Stores, Zoo road
2) Masama Stores, Rijiyar Lemo
3) Chapter One bookshop, mai kallon asibitin kashi na Dala
4) Umar Peace Production, Tudun Murtala, jikin masallacin Sheikh Ja'far
5) Gazza Stores, Hotoro Dan Marke
6) Garba Karfe Investment, Kabuga, Kano.
Allah ya tsare mu daga kamuwa daga wannan cutar, wadanda suka kamu kuma, Allah ya warkar da su.
Bello Sagir

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...