KWANAKI SHA TARA (K-19)
(Gajeren labari - Covid -19)
Kabiru Yusuf Fagge
Misalin karfe goma da rabi na safiya, mun kammala karyawa, ina zaune a gida a killace cikin iyalina, na jiyo mata daga makobta suna hirar da ta ja hankalina, na yi kuri ina sauraronsu.
"Ji nai an ce daga jiya da yamma zuwa yau da safen nan mutane goma sha tara ne suka mutu a unguwar Rafin Sabo..." Cewar daya daga cikin matan.
"Ke Haule, wa ya gaya miki? Hatsari suka yi?" Wata ta so karyatata.
"Ba hatsarin mota ba ce, rashin lafiya suka yi, ina jin maleriya ce." Haule ta ba ta amsa.
Wata ta amsa ita ma.
"Ni ma na ji, amma ni cewa aka yi mutane tara ne suka mutu, kuma duk a jiya suka mutu din, ban ji na yau ba."
Hankalina ne ya tafi ga tunani, yayin da su kuma matan suka cigaba da hirarsu.
Zama bai same ni ba, ana cikin wannan hali na annobar korona idan maganar wannan mata ta tabbata, to akwai abin dubawa da nazari a wannan unguwa, kai tsaye na shirya, na nufi unguwar Rafin Sabo cikin kiyayewa kamar yadda jami'an hukumar lafiya suka sanar.
Kamar yadda Haula ta fada haka na tarar a wannan unguwa ta Rafin Sabo, a wurare da dama ana zaman makoki, ke nan an samu mace-macen a unguwar. A matsayina na marubuci abubuwa hudu nake bukatar sani a yanzu; mafari, sanadi (dalili), halin da ake ciki da kuma mafita, don haka ina bukatar in tattauna da kuma yin bincike ga ahalin wadannan matattun, ta ya aka fara.
Mintuna talatin da wani abu na isa unguwar.
*
Kwanaki goma sha tara da suka wuce, a washegarin ranar da Alhaji Isa ya dawo daga harkar kasuwancinsa daga kasar Switzerland yana zaune a shagonsa na kasuwa, abokinsa Alhaji Sanda ya shigo wajensa suka gaisa.
"Na yi mamaki da kuka samu damar dawowa Najeriya, ba a hana ku ba." Cewar Alhaji Sanda yana dariya.
"Ni ma na yi mamakin." Cewar Alhaji Isa, "amma mun gano cewar an bar mu mun dawo ne saboda alfarmar wasu shafaffu da mai a gwamnatin kasar nan da kuma wasu zaratan 'yan kasuwa, lokacin da aka ce an rufe tashoshin jiragen saman kasar nan muna can har mun saduda, sai muka ji wata dama ta samu ta dawowa gida Najeriya, muka dauko hanya. Akwai ani abu da ya ba ni mamaki." Ya dan yi shiru.
"Kamar wane abu fa?"
"Daga can babu jirgin da zai kawo mu jihar Kano don an ce an rufe filin jirgin, sai dai filayen jirgin saman Abuja da na Lagos duk a bude suke, kuma da muka iso filin jirgin ko irin feshin nan na ma'aikatar lafiya da auna mu ba a yi ba, haka muka kwarara zuwa jihohinmu da gidajenmu." Yana da dariya, "Duk da mu, mun san ba ma dauke da cutar kororo din."
Alhaji Sanda ya yi dariya, "Ba kororo sunanta ba, Korona Virus dai. Amma ta ya ka san ba ka dauke da ita bayan ka ce ba a auna ka ba?"
Ya nuna kwanjinsa, "Ina ka ga alamunta a nan, garau nake cikin koshin lafiya."
"Ai ba ta nuna wa sai bayan wasu kwanaki."
"Ka ga ni fa garau nake Alhaji. Da ina da ita, ai ba ka zo gurina ba." Cewar Alhaji Isa yana dariya.
A daidai lokacin da suke wannan hirar, wata yarinya mai tallan wainar sadaka da ke unguwar Rafin Sabo tare da wasu almajirai su kusan goma, biyar daga cikinsu duk 'yan unguwar Rafin Sabo ne, suka karaso kofar shagon Alhaji Isa.
Mai waina ta yi sallama tare da cewa, "Sannu da dawowa Alhaji, za ka siyi wainar?"
"E, zuba ta dari biyu da casa'in." Alhaji ya ce kamar yadda malaminsa ya ba shi lakanin yin sadakar. Ya taso da kansa kamar yadda ya saba, ya karbi farantin wainar sadakar ya rarraba wa almajiran da suke wajen har ma da manyan mutane mabukata ya rarrabawa, suna ta godiya da sa albarka.
Kamar yadda Alhaji Isa ya ce ba a gwada shi ba, don haka ashe bai san tuni yana dauke da cutar Korona din, haka ya yi ta mu'amala da mutane da iyalansa, wasu sun kamu wasu kuma Allah ya tseratar da su.
Ina nan, ina tunani, ina zance ni kadai.
"Kamar yadda Alhaji Isa ya dawo kasar nan da cutar korona, haka fa gomiyar ire-irensa suka dawo, kuma ba tare da sun san suna dauke da cutar ba, ko kuma wasu sun sani amma ba su damu ba, sun ci gaba da mu'amularsu da 'yan'uwansu da iyalinsu da sauran al'umma, kuma wasu da yawa za su dauka ba tare da sun sani ba, su ci gaba da harkokinsu suma suna yadawa wasu, har zuwa lokacin da cutar za ta zama gagarumar illa a tattare da su, ta kawo karshen rayuwarsu idan kwana ya kare, kuma wasu ma su kamu. Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un."
Take hankalina ya koma kan tunanin al'ummar Rafin Sabo da sauran unguwannin da ka iya kasancewa wasu sun kamu da wannan cuta.
Shagon abokina Nura, mai aski dake unguwar na nufa, na tarar da shi yana yi wa wani aski, sannan suna hirar. Na shiga da sallama, muka gaisa, kana na nemi wuri, na zauna.
Nura yana kallona ta madubi, "Yau kai ne a unguwar tamu, fatan lafiya?"
"Lafiya kalau, ziyara kawai na kawo, don mu yi hira." Na ce da shi.
"To madalla, barka da zuwa, ga hirar kuwa ana yi. "
Ya juya, ya ci gaba da hirar da yake yi shi da samarin da na tarar.
"Ai wannan cutar sai a hankali, duk an bi mu ana turo mana wasu lambobi wai na hukumar kula da lafiya ta kasa, ga abu ana zargin ita ce, amma duk wadda ka kira ba za ka samu ba." Cewar saurayin dake yi wa askin.
Nura ya ce "Wai ku sai da kuka gwada kiran lambobin?"
"Kwarai kuwa, ai muna so mu sanar da su halin da ake ciki, don a dauki matakin gaggawa."
Daya saurayin da ke gefe ya tsomo baki, "Kuna bata wa kanku lokaci ne, ni fa sam ban yarda da wannan cutar ba, kawai wata cuwa-cuwa ce da harkalla ake kullawa don a ci wasu kudade."
Na yi saurin dubansa na ce, "Ba ka yarda da cutar ba? To wadannan mace-macen da aka yi fa, su ba alamu ba ne na cutar?"
Ya harare ni, "Alamun me? Yau muka saba ganin mutuwa, mutane dubu nawa maleriya da amai da gudawa suka kashe, su kansu wadannan da suka mutu, ni na fi tunanin maleriya ce, irin wannan sauron da ake yi."
"Kana wannan rashin tunanin naka, cutar na iya zuwa ta riske ka, kai ma ka mutu a banza." Saurayin da ake yi wa aski ya ce da shi.
"Kai ne dai za ka mutu a banza, amma ni ban yarda da wannan cutar ba."
Na girgiza kai, "Wannan halin ko in kula din shi zai iya haifar da yawaitar annobar, kamata ya yi, yadda kake wayayyen nan ka fara yarda da cewa cutar gaskiya ce, sannan ka kiyaye da dokoki da shawarwarin da hukumar lafiya suka bayar, don gudun yaduwarta."
Ya kura min ido, "Duk karyar banza ce, ba na ji ana gwaji ba, za ka nuna min inda ake gwajin."
Zan yi magana ya hana ni.
"Ai ban gama tambayar taka ba. Shin ko za ka nuna min cibiyoyin da zan je a gwada ni?"
Na yi shiru don ya ci gaba.
"Ina da lambobin da ake turowa don kiran gaggawa, ko za ka kira min daya daga cikin wayar mu gaya musu a zo a auna mu, ko a duba 'yan'uwan mutanen da suka mutu?"
"Kai nake sauraro." Na ce da shi.
"A karshe nuna min mutum daya da ya kamu da cutar, ko ka gaya min abin da su hukumar lafiyar suka ce?" Ya kare yana hararata.
Na yi murmushi, "Da farko dai, kamar yadda na fada, ya kamata ka fara yarda da tabbatar cewar cutar gaskiya ce, kamar yadda ga shi a wannan unguwar taku abin da ya faru, da za ka bibiyi asalin abin da sauran mutane a wasu unguwannin za ka iya tarar da faruwar kwatankwacin wannan abu.
"Abu na biyu shi ne; ya kamata mu yawaita wanke hannayenmu sabulu ko omo da ruwa, ka san hannu yana da tara abubuwa irin cutukan nan. Kuma kamar yadda masana lafiya suka fada, cutar tana saurin yaduwa ne idan mutumin da ke dauke da ita ya yi tari kwayoyin cutar suka yadu a cikin iska. Ka ga mutum yana shakar iskar ko kuma wajen da kwayoyin cutar suka fada, sannan ya taba idonsa ko hancinsa ko bakinsa to zai iya kamuwa. Ka ga ya kamata mu kiyaye ko? Sannan shi kansa tarin ya kamata a rinka yin sa cikin tissue ko gefen gwiwar hannu, mu kuma guji taba fuskarmu musamman idanu, hanci da baki. Ko da kiyaye wannan muka yi, ai ka ga akalla za mu zauna lafiya."
Ya yi tsaki, "To me gwamnati za ta ba mu, za ta ce mu zauna a gida, ko mu ki zuwa masallaci yin jam'i?"
"Tun da alamu sun nuna ka fara saukowa, abu mafi muhimmanci ka kiyayewa wadancan sharuda da masana lafiya suka fada. Batun zama a gida kuwa, me kake tsammani idan ba ka zauna a gidan ba, ka kwaso cutar, ka ga kenan sai cutar ta zaunar da kai a gidan idan ba ka zauna ba.
"Sannan batun jam'i ai ba sallah aka hanaka ba, kuma idan ka zauna a gida ko a wani wajen ka yi, sallar taka ba ta karbu ba ne? Me kake tsammani idan ka kwaso cutar, za ka iya zuwa masallaci yin sallar ko za ka yi a gida ne?"
Nura ya karbe, "Ai sai dai a taimaka masa ya yi, idan ma mai kokarin yi ne."
Suka kyalkyale da dariya.
Da alama kokarina na wayar da kan wannan saurayi har ma da sauran, irin su Nura ya yi tasiri, sai dai ni kaina na san, na yi masa kwangen ba shi wasu amsoshin, kuma ina da wata shawara guda daya da zan bai wa gwamnati, duk da na san ba za ta karba ba.
Ina ma ace gwamnatinmu a cikin wannan halin za ta samar da abubuwa guda uku; to da ina da tabbacin zama a gidan zai zo da sauki, na farko
(1) ta samar da wutar lantarki
(2) na biyu ta samar da ruwan sha
(3) na uku ta samar da hanyar saukaka kayayyakin masarufi kafin lokaci ya kure mana.
"Ka ga hakan zai saukaka wa mutane musamman talakawa, kuma a samu wadanda za su zauna a gidan ba." Nura ya fada. Ashe maganganun da na yi sun fito fili.
Me zai faru, ina kunna rediyo sai na ji labari mafi muni, cewar wasu unguwanni ire-iren su Rafin Sabo an samu bullar cutar, amma wai ba gwaji ba ne ya tabbatar da ita ba, alamu ne, don babu kayan gwajin.
Allah mai iko, cikin kwanaki sha tara cutar ta watsu fiye da yadda ake zato, Allah ya kare, ya kuma kiyaye, amin.

No comments:
Post a Comment