*RUBUTUNKA TUNANINKA*
*MARUBUTA DA KARE-KAREN HARSHEN HAUSA*
Gabatarwa
*KARIN HARSHEN HAUSA*
Da farko ya kamata marubuta su san mene ne "karin harshe": *Karin harshe yana nufin 'yan bambance-bambancen lafazi da na kalmomi da jimloli da kan faru tsakanin rukunan al'umma ko shiyyoyin kasa mai harshe ɗaya.*
Kuma a ƙasar Hausa kusan kowacce tsohuwar daula ko masarauta tana da karin harshenta daban da na sauran 'yan'uwanta. Sannan akan yi wa karin harshen laƙabi da masarautar ko daular, misali Dauranci daga Daura, Kananci daga Kano, Katsinanci daga Katsina, Zazzaganci daga Zazzau, Bausanci daga Bauci da sauransu.
Abin nufi a nan shi ne, yadda wasu jihohi ko shiyyoyin ƙasa suke furta wasu lafazai kalmomi ko jimloli da bambanci da na sauran jihohi ko shiyyoyi.
Wasu na iya kallon karin harshe a matsayin "Hausar baka" saboda zuwa da samuwar "daidaitacciyar Hausa". A nan abubuwa biyu nake fatan marubuta su fahimta domin sanin muhimmancin karin harshe a rubuce-rubucensu; (1) daidaitacciyar Hausa (2) kare-karen harshen Hausa.
A dunƙule za a iya raba karin harshen Hausa da na nahiya dangane da muhimmanci da irin bambance-bambancen da ake samu a tsakaninsu, wato dai akwai:
*HAUSAR GABAS:* su ne dangin Kanancin, waɗanda suka haɗar da:
-Kananci (Kano)
-Bausanci (Bauci)
-Zazzaganci (Zariya)
-Ƙudduranci/Gudduranci (Bauci)
-Hadejanci (Hadeja)
*HAUSAR YAMMA;* dangin Sakkwatanci, waɗanda suka haɗar da:-
-Sakkwatanci (Sakkwato)
-Kabanci (Kabi/Kebbi)
-Gobiranci (Gobir)
-Zamfaranci (Zamfara)
*HAUSAR AREWA;* wadda ta haɗa da:-
-Dauranci (Daura)
-Gumalanci (Gumel)
-Katsinanci (Katsina)
-Damagaranci (Damagaran)
Da sauransu.
*DAIDAITACCIYAR HAUSA*
Tsari ne ko nau'i ne na harshen Hausa da ake amfani da shi wajen koyarwa a makarantu ko kotuna da kafofin watsa labarai da wajen "buge-bugen littattafai da mujallu" da sauransu.
Ita wannan Hausar (daidaitacciya) haɗe-haɗe ce daga karorin harshen Hausa da Hausawa suke amfani da shi, sai dai kawai an fifita Kananci fiye da sauran kare-karen harshen Hausa kuma dalilin da ya sa daidaitacciyar Hausa ta fi kunsar Kananci shi ne; yanayin birnin Kano saboda kasancewarsa wajen harkokin kasuwanci ne daga dukkan sassan Najeriya da kuma waɗansu ƙasashen waje. Ita wannan dama ta cudanya da mutane ya sa Kananci saurin yaduwa da kuma saukin fahimta. Saboda haka amfani da Kananci don daidaita wannan harshe lamari ne mai muhimmanci domin a samu saukin rubutu da karatu a cikinsa. Don kuwa da an bar shi haka sakaka kowa ya yi yadda yake so wajen rubuta Hausa a cikin karin harshen da ya fi sabawa, tabbas da al'amura sun caccabe, sun taɓarɓare wanda daga bisani da harshen Hausa kuwa ya yi wuyar koya daga masu son su koye shi. Amma saboda yana ƙarƙashin inuwa daya to in kai Bahaɗeje ne ko Basakkwace ko Bazazzage ne ka zo nazartar Hausa to fa dole ne cikin daidaitacciyar Hausa za ka koya.
Haka ma wajen karanta labarai a radiyo da talabijin da wajen buga jaridu da mujallu da ƙasidu da sauransu duk da daidaitacciyar Hausa za ka yi, akwai tarin misalai na daidaitacciyar Hausa da sauran kare-karen harshen Hausa, zan kawo su a ƙasa.
*MISALAN KARE-KAREN HAUSA DA DAIDAITACCIYAR HAUSA (D/H)*
*Sakkwatanci D/H
swahe safe
ɗwaci daci
hwata fata
*Katsina D/H
Katcina katsina
hwarko farko
kihi kifi
*Bauchi D/H
shiki ciki
zushiya zuciya
shitta citta
shigiya cigiya
dagashi dagaci
takaishi takaici
*Dauranci D/H
akuhi akushi
huka shuka
*Gudduranci D/H
'afaa ƙofa
'ofa ƙafa
waro ƙwaro
Akwai tarin misalai da yawa, a sati mai zuwa zan kawo su.
*ABIN DA MARUBUCI ZAI LURA DA SHI*
A nan, abin da ake so marubuci ya lura da shi, shi ne, yana da damar yin rubutu da karin harshen kowacce jiha ko shiyya a matsayin maganganun taurarin labarin ba a matsayinsa na marubuci mai bayani a cikin littafi ba.
Misali;
Marubuci yana rubutu a kan tauraro wanda kuma Basakkwace ne, idan ya zo sai ya rubuta kamar haka:
_Alu ya shigo cikin rumfar ya dubi bakin nasa, ya ce "To sai da swahenku, ina hwatan mu yi kwana lahiya..."_
Maimakon _"To sai da safenku, ina fatan mu yi barci lafiya..."_
Wannan shi ne zai nuna wa mai karatu cewar tauraron ko taururuwar ko taurarin 'yan shiyyar Sakkwato ne .
Kuma kamar yadda aka sani marubuci na iya yin rubutu a kan taurari na kowacce shiyya, kuma maganganunsu da halayyarsu ce kan nuna asalin shiyyarsu.
*Ƙa'idojin Rubutun Hausa*
*ta ga* ba *taga* ba (kamar ta ga wani abu)
*ta sa* ba *tasa* ba
*ta ƙi* ba *taki* ba
*ta ce* ba *tace* ba
*ta so* ba *taso* ba
*ta yi* ba *tayi* ba
*Tabawa* ba *Ta-bawa* ba
*tafiyar da* ba *tafiyad da* ba
*tafiye-tafiye* ba *tafiye tafiye* ba
*takan* ba *ta kan* ba
*take* ba *ta ke* ba
*tambaya* ba *tanbaya* ba
*tana* ba *ta na* ba
*tashoshi* ba *tasosi* ba
*tinjim* ba *tinjin* ba
*tsai da* ba *tsaida* ba
*tsattsafe* ba *tsatstsafe* ba
*tsattsame* ba *tsartsame* ba
*tsattsara* ba *tsatstsara* ba
*tumfafiya* ba *tunfafiya* ba
*Turanci* ba *turanci* ba
*tutoci* ba *tutoti* ba
*waɗancan* ba **waɗan can* ba
*waɗanda* ba *waɗan da* ba
*waɗansu* ba *waɗan su* ba
*wacce ce?* ba *waccece?* ba
*wakensa* ba *waken sa* ba
*wancan* ba *wan can* ba
*wanda* ba *wan da* ba
*wandonmu* ba *wandommu* ba
*wandonsa* ba *wandon sa* ba
*wannan* ba *wan nan* ba
*wanne ne* ba *wan nene* ba
*wash!* ba *wash* ba
*wasula* ba *wasulla* ba
*wataƙila* ba *wata ƙila* ba
*wayonmu* ba *wayommu* ba
*wayyo!* ba *wayyo* ba
*ya sa* ba *yasa* ba
*ya ga* ba *yaga* ba
*ya ƙi* ba *yaƙi* ba
*ya bi* ba *yabi* ba
*ya ce* ba *yace* ba
*ya yi* ba *yayi* ba
*yakan* ba *ya kan* ba
*yana* ba *ya na* ba
*yanka wa yara* ba *yankawa yara* ba
*Yarbanci* ba *yarbanci* ba
*yayyafi* ba *yaiyafi* ba
*yi da* ba *yida* ba
*yi shi* ba *yishi* ba
*yin sa* ba *yinsa* ba
*yin ka* ba *yinka* ba
*yin ku* ba *yinku* ba
*yin mu* ba *yinmu* ba
*yin sa* ba *yinsa* ba
*yin ta* ba *yinta* ba
*za ka* ba *zaka* ba
*za a* ba *za'a* ba
*za ki* ba *zaki* ba
*za ku* ba *zaku* ba
*za mu* ba *zamu* ba
*za ni* ba *zani* ba
*za shi* ba *zashi* ba
*za su* ba *zasu* ba
*za ta* ba *zata* ba
*za ya* ba *zaya* ba
*zamba* ba *zanba* ba
*zambo* ba *zanbo* ba
*Zamfara* ba *Zanfara* ba
*zana wa Isa* ba *zanawa Isa* ba
*zanawa take* ba *zana wa take* ba
*Zariya* ba *Zaria* ba
*zo da* ba *zoda* ba
*zub da* ba *zubda* ba
*zugum* ba *zugun* ba
*zumbuɗa* ba *zunbuɗa* ba
(A nan na kammala rubuta wannan ƙa'idojin rubutun, suna da yawa)
Na gode
Kabiru Yusuf Fagge

Da kyau abin ya bada ma'ana
ReplyDeleteDa kyau sosai. Allah y kara basira
ReplyDelete