Monday, March 23, 2020
GWARAZAN ZEWA AWARD 2019-2020
A ranar Lahadi 22-3-2020 kungiyar marubuta ta Zazzau Emirate Writers Association ta bayar da kyautar karramawa ga marubuta shida (6) da suka sami damar lashe kyautar gajerun labarai da ta sanya mai suna "MUTUM DA MAHALICCINSA AWARD" a karkarshin kungiyar Zewa din.
Ga tsarin wadanda suka samu damar lashe gasar kamar haka:
Mussadam Potiskum daga jihar Yobe -A matsayi na 1
Zubairu Ballannaji daga jihar Kano - A matsayi na 2
Abdullahi Kangala daga jihar Kano - A matsayi na 3
Sauran su ne:
Gimbiya Rahma daga jihar Kano
Adam Miyatti daga jihar Kano
A yayin taron an karrama wasu shahararrun mutane ciki har da marubuta Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) da Fatima El-Ladan da sauran masu rike da mukaman siyasa da sarautun gargajiya da kuma mawaka da masu hidimtawa al'umma.
Sannan an kaddamar da littafin mawallafi Yahaya S. Kaya mai suna "Mutum Da Mahaliccinsa."
An yi taro lafiya, an tashi lafiya.
daga Kabiru Yusuf Fagge
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...
No comments:
Post a Comment