UBANKI YANA GIDA YARINYA
(Gajeren Labari)
Kabiru Yusuf Fagge
Ina zaune a cikin Keke Napep muna tafe, don kai ziyara wajen
abokina Hakimin Wajila, mai suna Iro Mamman, kida ne kawai yake tashi a Napep
din, a wakar Lalakukulala, mai jan Napep din dattijo ne da ya doshi shekaru
hamsin zuwa hamsin da biyar, don ga furfura da gemu nan a tare da shi.
Sai gyada kai yake kamar kadangare, wani lokacin har wani
zabura yake ya kwaso Shoki a waje, sannan ya hankado shi cikin motar, ni kam
kallonsa kawai nake.
A daidai kwanar shiga unguwar Wajilar, wata kyakkyawar
yarinya 'yar birni, mai dauke da shekaru 15 zuwa 16 ta tsayar da mu.
"Wajila za ka kai ni."
"Hau mu je 'yanmata, kudinki Naira 50."
Ta hau, muka fara tafiya. Ko nisa ba mu yi da daukar
yarinyar nan ba, ta sake yin magana.
"Baba kai ma kana jin ire-iren wadannan wakoki na
'yan-bana-bakwai."
Wani irin ihu mutumin nan ya yi, sannan ya yi gefe da motar,
ya juyo, ya kalli yarinyar.
"Kuturun uban nan kayyasa! Yarinyar wane ne Babanki. Ai
ubanki yana gida."
"Ni kuwa na fadi haka ne don girmama furfurar da ke
kanka, da kuma gemu." Ta ce da shi.
"E, shekaru ne suka kawo wadannan abubuwa da kika fada,
amma ki sani, yanzu na fara cin duniyata, don kuwa a yadda nake gani yanzu ni
sa'anki ne, ba ni da aure, kuma ba zan yi ba a nan kusa, sai ma kin riga ni yin
aure, don sai na gama cin duniyar tawa. Saboda haka ki rinka sanin wane ne
Babanki, ko kuwa haka shi ma baban naki yake? "
"Gaskiya ba haka mahaifina yake ba."
"To, don haka Babanki yana gida, ki daina ganin kowanne
tsoho kina ce masa Baba."
"Haka ne. Na daina."
Lokacin da na kyalkyale da dariya, a lokacin shi kuma ya
zaro sigari ya banka mata wuta, bayan ya yi doguwar tsuka, ya karkace, ya
tuttulo mata hayakin a fuskar.
Haka kawai, na kasa cewa komai sai kallon ikon Allah. Ya
dora da cewa.
"Mu je ko kina da magana kawata?"
A sanyaye ta amsa, "Mu je kawai Malam."
"Kan uba. Wane ne Malam din?" Ya sake amsa mata.
Ta marairaice, "Don Allah ka yi hakuri, ba kai ba ne.
Kuma na daina. Mu je Dancaburos."
"Good! Girl, ko ki ce Caburos, ko ki ce Baabaa shi ne
sunana. Hakan ya sa an yafe miki kudin motar ba."
Ya fincike mu, ya yi gama yana rausayawa har da kwaso
Shokinsa, babu abin da ya dame shi.
Hahahaha lalle kuwa ga Baabaa🤣🤣🤣
ReplyDelete