TALAKAWA SUN FI YIN AURE
Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge
An tambayi Sheikh Abu Yusufa Alfagawy cewar, "Aure a
kasar Hausa yana da tsada, to amma me ya sa sau tari talakawa sun fi yin aure
da yawa fiye da masu hannu da shuni. Kuma sun fi yin saki fiye da masu hannu da
shuni..."
Sheikh Alfagawy ya murmushi ya ce, "Ai idan ka ji an ce
an yi da yawa dole a yi sakin da yawa. To amma Alhamdulillahi, na yi farin ciki
da wannan tambayar taka matuka, ba don komai ba, sai don irin wannan abu ya
shafe ni sosai, kuma na sami kaina a cikinsa, wato..."
Ya fara ba da labari.
"Maganar gaskiya yawancin matan da muke aure a al'ummar
Hausa sun fi baiwa kudi ko abin hannu daraja fiye da soyayya ko zaman rayuwar
aure don Allah. Da zarar sun fuskanci da kyar kake kawo rabin kwanon shinkafa
ko kasa da haka gida, sannan suka fahimci sai sati-sati ake surka abin miya
wato nama, to za su zabtare kashi bakwai da rabi na biyayyar da suke yi maka,
idan a farkon aurenku tana yi maka wasu abubuwa da yawa na biyayya, to kuwain
sha Allahu watanni tara na giftawa za ta rage sama da rabi na daga biyayyar da
take yi makan," ya yi gyaran makogoro. Sannan ya dora.
"Haka ne ya faru da ni, da matata, mai suna Salaha,
saboda ba na son in yi saki nake zaune da ita, amma abubuwan da ta yi min da
tuni na aunata waje...
"Ina ba ka labari, wato sannu a hankali, muna zaune da
ita tana yi min yadda take so, ni kuma ba ta yi min yadda nake so, yau da gobe
Allah ya yi min arziki, na mallaki motoci da gidaje, abin da nake gaya maka, za
ka sha mamakin idan na ce maka wallahi a yanzu biyayyar da take yi min kamar ta
fi kowa iya biyayya a cikin matan duniya, kuma kamar in bude aljanna in watsa
ta a ciki...
"To amma da farko, na dade ina mamakin a ina ta koyo
wadannan abubuwa na kyautatawa a yanzu, tsaf da na yi tunani, sai na gano cewar
masu gidan rana take yiwa ladabin ba ni ba..."
Ya yi murmushi, kana ya ci gaba da cewa, "Maganar
gaskiya masu kudi suna samun biyayya daga matansu saboda suna da abin hannu,
idan ki ka yi masa rashin mutunci ko ki ka ki yin biyayya yanzu zai auro wata
ko da kuwa bai sakeki ba, wannan tunanin da kuma tunanin idan ya saketa ba ta
san hannun da za ta fada ba, ya sa suke yin biyayya yadda ya kamata...
"Kuma ka sani shi wannan mai kudin ko wata ya aure, zai
dai su yi ta yi masa biyayya a zahiri, amma a badini akwai abin da suke yiwa
biyayyar.
"Ita kuma macen da take auren talaka gani take yi ko ya
saketa, ko ya karo mata kishiya duk shammakal. Don haka shi kuma talaka da ya
rasa kulawar da ya kamata ya samu a wurin matarsa, da zarar ya sami faraga sai
ya ga ai gwara ya auro wata ko ya samu kulawar da ya rasa, ko kuma ya koya mata
yadda ya kamata ta zauna da shi, tun da wannan ta ki bi.
"Idan aka sami akasi, wani na iya korar matar tasa,
wani kuma zai ci gaba da hakurin zama da ita don ko ta yi koyi da wadda ya auro
din, idan itama ba ta bijire daga baya ba...
"Fata dai anan shi ne, Allah ya sa matan su fahimci
wannan mas'alar su gyara, don a samu daidaito, Allah ya sa mu gyara." Ya
tsahirta kafin ya dora da cewa, "Akwai wata tambayar?"
No comments:
Post a Comment