Wednesday, January 9, 2019

Gajeren Labari: SANYI NE

SANYI NE...

Gajeren Labari


(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Wani mahaukaci ya zo wucewa ta bakin Kasuwar Sabongari, kawai sai ya ji wani mai sayar da maganin gargajiya yana talla, mahaukaci ya tsaya cike da mamaki yana kallo tare da sauraron mai maganin nan kunne bude, bakin wangame a lokaci guda kuma ido tarwas.

Shi kuwa mai magani, bai san me ke gudana ba, yana ta tallansa bilhakki:


"Mayawuya, sanyi ne,

Radadin mukamuki, sanyi ne,

Makaki da zogi, sanyi ne,

Kora ta dami yaro, sanyi ne,

Amosani ka, sanyi ne,

Ciwon baya, sanyi ne,

Yawan atishawa, sanyi ne,

Ido yana wani duru-duru, sanyi ne,

Yawan hamma, sanyi ne,

Jiri-jiri, sanyi ne,

Yawan tusa, sanyi ne,

Sanyi ne, sanyi ne, sanyi ne......

Wannan talla ta ishi mahaukacin nan, kawai sai ya sudada ta bayan mai tallar maganin nan, ya zage tun karfinsa ya sharara masa mari, ji kake "Kauuuuuuu!"

Mai tallan magani ya yi saurin kallon mahaukaci, tare da rike kumatunsa wanda ba tare da bata lokaci ba, tuni har ya kumbura, bai iya cewa komai ba face fashewa da kuka da ya yi.

Wasu mutane da ke gefe ne suka iya magana, suka daka wa mahaukacin nan tsawo, suna cewa "Kai me ya sa ka mare shi?"

Mahaukacin nan ya yi dariya yana kallonsu, ya ce, "SANYI NE!!"

Mutanen suka kwashe da dariya, suka jinjina kai, suna fadin "E, lallai kam sanyi ne."


1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...