ADDU'AR MAKABARTA
Gajeren Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Da zarar an binne mamaci kamar yadda shari'a ta tanadar, to
ana bukatar kowa ya watse yana mai yi masa addu'ar samun rahama, face 'yan'uwan
mamaci da za su tsaya su yi masa addu'a da tuni ga ababen shaidawa da gaskiya
don tambayar kabari, sai kuma wadanda za su iya tsayawa don yi wa iyalai da
'yan'uwan mamacin addu'a.
A ranar da muka kai Marigayi Adam Mai Dinki, tun kafin a
binne shi na hango Alarammomin unguwarmu su uku, wato Alaramma Malam Zakari
Mai-Buhun-Salati da Alaramma Malam Habu Mu-Cika-Da-Addu'a da Malam Kwana-Sallah
a rukuni guda, na tabbatar yau idan ba mu yi wasa ba sai mun yi rabin wuni a
makabartar nan suna yi mana addu'a.
Iya sanina da su Alaramma da zarar an kammala binne gawar
nan idan suka fara addu'o'i suna yi, suna mika wa juna fasin (passing) to sai
kowa ya gaji.
Ba zan manta ba, wata hudu da suka wuce, wata yarinya ta
rasu, muka kawo ta, ana kammala binne ta, Alaramma Mai Buhun-Salati ya fara
addu'a, ya fadi a karanta Kulhuwallahu kafa goma sha dai-dai ya fi sau bakwai,
Falaki Da Nasi ma haka, ya zarce zuwa su Ya Shafi, Ya Salamu, Ya Azizu sun fi
cikin carbuna takwas-takwas, haka Salatil Fatih kamar muna Musaffa, kai a ranar
har da ayoyin da ba na rahama ko gafara ba ma sai da Mai Buhun-Salati ya sa
muka biyo, ya tsahirta kuma ya sawa Malam Mai-Kwana-Sallah fasin, shi ma ya yi
ta yi, tun muna gumi a makabartar nan har guminmu ya fara kafewa.
Ina kammala wannan tunanin, na fara tunanin to mene ne
mafita a yau, don ga manyan sitirakokin (strikers) addu'a suna jiran a gama
binnewa su fara - kuma ga rana ta kwalle sosai. Take na fara tunanin kawai na
sumame, na gudu, na bar makabartar, ko banza ina mugun jin yunwa, ga rana.
Sai dai kuma, da na dubi tarin mutanen da ke tsattsaye a
cikin makabartar, sai na ga idan na gudu ban yi musu adalci ba, ta yiwu akwai
da yawa da suka fi ni uzuri.
Ina cikin wannan tunani na ji muryar Alaramma
Mu-Cika-Da-Addu'a na fadin, "Mu yi salati goma-goma...ga Annabi...."
Da karfi ya fada.
A rikice na dawo da hankalina gurin, na kalli bakinsa yana
ta mutsul-mutsul, take cikin ikon Allah wata dabara ta fado min. Kawai, sai na
ji ya ce, "Mu yi Kulhuwallahu kafa bakwai-bakwai." Ban jira ba, na
amsa masa, ina mai daga murya fiye da ta shi, na ce "Kulhuwallahu kafa
bakwai-bakwai, Allah ya yi masa rahama..."
Ya kalle ni, ya yi murmushi, don ya samu wanda zai rinka
isar da sakon addu'ar tasa da karfi. To a daidai lokacin na shammace shi na
daga murya na ce, "FATIHA!!!" tare da shafawa.
Ai kuwa, duk mutanen da ke wurin suma, suka amsa, suka ce
"Fatiha!!!" a tare, sannan suka shafa, suna hamdala, wasu suka dauki
hanyar fita daga makabartar cikin jin dadi, wasu suka fara yiwa iyalan mamacin
ta'aziyya.
Ni ma hanyar fitar na nufa a sukwane don na san na yi wa su
Alaramma kancal, ta gefen ido ina hango su a tsugunne sun yi jangwam da su
kamar murafun takwane, suna yiwa juna kallon-kallo a lokaci guda suna hango ni
ina sauri, idanunsu jawur kamar su yo tsalle su dirar min, amma ba hali.
Na fita, ina murna, sai
dai na san zan sha mita da kumfar baki a unguwa daga wajen su Alaramma, amma a
banza, tunda na sa an fita hakkin mutane, sai dai in ce Allah ya sa mu gane, mu
bi sunnar ma'aiki mikakkiya, amin.
No comments:
Post a Comment