Monday, July 31, 2023



 

KARATUN LITTAFIN TUNANINKA KAMANNINKA NA BASHIR OTHMAN TOFA

Gabatarwa

Insha Allahu za mu fara karanta littafin Tunaninka Kamanninka.

TA’ALIKI

 

Da sunan Allah Mai cikakken iko, Mahaliccin Komai, Mai yin abindaYa so.

 

TUNANINKA KAMANNINKA” yunquri ne mai kyau, wajen kyautata xabi’un al’umma tareda xorasu bisa tafarkin da zai ba su xaukaka a duniya da lahira. Marubucin ya nutsu wajen fahimtar halin xan-Adam da kuma irin cutar da ke damun zuciyarsa, sannan kuma ya bayar da maganin cututtukan.  Haqiqa,  a  ganina  ya  gano  maganin. Duk wanda ya sha maganin da Alhaji Bashir Othman Tofa ya ba wa zuciya a wannan littafi, to ya waraka. Sha yanzu magani yanzu!

 

Marubucin, wanda gogagge ne a fannin rayuwa, ya fito da salon rubutun da babu shi a harshen Hausa. Rubutu  a  janibin  falsafa  tsohon  al’amari  ne  a tarihin duniya. Amma a harshenmu, yanzu muka ce: “Assalamu Alaikum“.

 

Allah (swt) Ya qara tabbatar da abinda nake ta tsokaci da shi kullum, cewa: baiwa ta Allah (swt) ce. Yana bayar da ita inda Yake so. Don haka ko yaushe sai mu duba mu gani da idon basira cewa ta wacce hanya za mu iya amfani da baiwar da Allah (swt)   Ya   ba   wa   kowannenmu   domin   qara kusantarSa (Allah swt), da ci gabanmu baki xaya, ba tareda mun raina mafitar basirar ba.

 

Wannan littafi mai albarka, bai sauka daga qa’idar shari’a ko ta xabi’ar rayuwa ba. Zai yi fa’ida ga duk jinsi na al’umma, musammam manyan gobe.

 

Ina mai jan hankalin jama’a da su karanci wannan littafi tareda aiki da shi domin samun al’umma tagari.

 

Allah (swt) Ya albarkaci marubucin da masu karatu baki xaya.

 

Wama taufiq illa billah!

 

 

 

Alhaji (Dr.) Yusuff Maitama Sule

Xan Masanin Kano

 

20th June, 1997



MUHIMMAN TUBALAN GINA RAYUWA

 

Wani Malami ne ya ke yiwa xalibansa misali. Sai ya xauko tukunyar gilashi ya ajiye a kan tebur, sannan ya xauko duwatsu kamar curin fura ya ringa sa su cikin tukunyar har sai da ta cika da su yadda ba wani dutse irinsu da zai shiga. Da ya gama, sai ya tam- bayi xaliban, “Tukunyar ta cika?” Suka ce, I, ta cika.” Malami ya ce, “Kun yi kuskure. Ba ta cika ba. Bari kuma ku gani.”

Ya sunkuya ya xauko kwandon tsakuwa ya ringa zuba su a cikin tukunyar, har sai da ya cike guraben da ke tsakanin duwatsun.

Sannan ya kalle su ya sake tambayarsu, “Yanzu fa?” Sai xalibai

suka yi shiru. Can, sai wani ya ce, “Wataqila.” Malami ya yi mur- mushi ya kaxa kansa.

Ya sake sunkuyawa, ya xauko kwanon rairayi, ya yi ta zuba shi cikin tukunya, har sai da ya cike duk xan gurbin da ya saura tsa-

kanin tsakuwoyin. Sannan ya tambayesu. Suka ce, Basu sani ba.

Sai kuma ya xauko kwanon ruwa, ya yi ta zuba shi cikin tu- kunya, har sai da ta cika maqil, bayan rairayi ya tsotsi abinda zai

iya. Sannan da kansa ya ce wa xaliban, “To yanzu watakila ta cika.

Kun fahimci darasin wannan misali?”

Wani haziqin xalibi ya ce, “Duk qaracin lokacinka, in ka yi qoqari zaka yi yin wasu abubuwan dabam.”

Malam ya ce, “A a. Darasin shi ne, idan ba ka fara shigar da

muhimman tubalan rayuwarka da farko ba, to ba zaka iya shigar da su gaba xaya nan gaba ba. Lallai ka yi tunaninsu, ka sansu, sannan ka  jera  su  daidai  muhimmancinsu;  manyan  da  farko  sannan qananan, ka kuma tunkaresu cikin hanzari da lura. Komai daidai muhimancinsa. Da da rairayin na fara da tsakuwar ba ta shiga ba, da kuma ko dutse xaya ba zan iya sa wa ba. Amma yanzu ga shi komai ya shiga ya sami mazauninsa.

 

Waxannene naka muhimman tubalan rayuwar?

Ka sansu ka kuma tsara su daidai da muhimancinsu?

Ya za ka tsara waxannan? Addininka, Ilminka, Iyalinka, Sana’arka, Mutumcinka, Tausayawarka da Jin-daxinka da ….?

Saturday, July 15, 2023

'YA'YA BIYU

 ‘YA’YA BIYU

(Family Planning Saga)

Muna zaune ni da budurwata Nabila, muna hira. Ta dube ni, tare da tambaya ta.

“Yau babu wani sharaÉ—i ko shawarar na ji ka yi shiru?”

Na bi ta da murmushi.

“Kamar kin shiga raina, yunÆ™urin nan da kika ga na yi, zan gaya miki ne, sai kika tambaya.”

“To ina sauraronka.” Tana murmushi take maganar.

“Nabila, a rayuwata ina son ‘ya’ya, amma maganar gaskiya ina son shekaru goma sha biyar É—in farkon aurenmu mu haifi ‘ya’ya biyu kawai.”

Ta kalle ni da mamaki a idonta.

“Na san kana da hujja, amma ko za ka iya gaya min tare da Æ™arin bayani. Iya sani na, Allah ne mai yi ga rayuwar halittunsa, amma ta ya za mu yi haka?”

“Good, Nabila kaso tamanin na rayuwar É—an’adam tana hannunsa, tun da Allah ya yi mu mutanen ya ba mu hankali da tunani da ilimi, don haka tsara haifar ‘ya’ya biyu a cikin shekaru goma sha biyar zuwa ashirin abu ne mai sauÆ™i.”

“Na ji wannan, saura dalili.” Ta ce da ni.

“Lafiyar ki, da tarbiyantar da ‘ya’yan da É—ora su a kan kyakkyawar rayuwa gwargwadon iyawarmu da biyan haƙƙoÆ™insu har su hau kan gwadaben rayuwa mai inganci. Sannan sai a nemi wani ko wasu, su ne dalilaina.”

Ta yi shiru, kafin ta numfasa.

“Na É—auka Allah ne mai shiryarwa da bai wa É—an’adam abinci da arziÆ™insa tun daga lokacin da yake halittarsa?” Ta tuhuma.

“Allah shi ne mai shiriya, amma bisa mataki-mataki ciki har da wanda ya É—ora wa iyaye na haƙƙoÆ™in ci da sha da tarbiyya.” Na numfasa, “Nabila komai da kika sani Allah ya yi shi bisa sanadi, sanadin shi ne iyaye su kula da abubuwan da na lissafa miki, idan suka gaza da gangan sai Allah ya kama su. Ai Allah shi ne mai halitta, me ya sa bai ce idan aka Haifa, a watsar da su za su tashi da tarbiyya, za su ci, su sha su tufatu daga sama ba, ya bai wa iyaye alhakin tarbiyyar? Saboda haka tsarinsa yake.”

Yayin da na yi shiru, ta dube ni tana son yin tambaya, ta kasa, na É—ora da cewa.

“Don haka, Nabila muna buÆ™atar mu yi wannan aikin idan mun yi aure, Allah ya ba mu haihuwa, mu sami ‘ya’ya biyun mu yi namu aikin, Allah ya yi na shi.”

Ta yi ajiyar zuciya.

“Na gamsu da bayaninka Habib.”

Bayan aurenmu, a cikin shekaru uku Allah ya ba mu ‘ya’ya biyu mace; Fatima da namiji Muhammad (Al’amin)

Muna cikin shekara ta huÉ—u da aurenmu, da ‘ya’yanmu guda biyu cikin farin ciki da kula da soyayya da nutsuwa, a gidan kaina nake, madaidaici ne mai É—akunan Nabila da falonta, ni ma nawa É—akin da falo, da É—akin saukar baÆ™i, haka su ma yara kowa da nashi É—akin da banÉ—akuna daban-daban. Motata ta kai miliyan biyu da rabi.

Harkar siyar da shaddodi da yaduka su ne kasuwancina. Ina kula da ‘yan’uwana da na Nabila gwargwadon iyawa ta.

A wannan shekarar ne ‘yan’uwan Nabila da iyayenta mata suka fuskanci ta tsallake shekaru biyu ba É“atan wata, ba É“ari ba ciki. Take suka sa Æ™ahon zuÆ™a sai da suka gano jinkirin haihuwa muke yi.

Watarana ina É—akina a zaune, Maman Nabila; Baba Gambo da yayarta mai suna Atuwa suka zo gidan, ban yi tsammanin sun san ina nan ba, na ji suna hira, suna É—aga murya.

“Ke muke saurare, gaya mana abin da ya sa kuke yin family planning?” cewar Baba Gambo.

“Gaskiya tun kafin aure mun yi wannan yarjejeniyar da shi. Kuma ni ina ganin ba wani abu ba ne...”

Atuwa ta katse ta, “Ke sakarya, kya ce ba wani abu ba ne mana, tun da an ninke ki baibai. To tsaya ki ji in gaya miki gaula ya mayar da ke. Kina nan zaune da ‘ya’ya biyu zai Æ™aro aure har biyu, ke har uku ma, ai haka mazan yanzu suke, su mayar da mace shashasha, su banka miki maganin rashin haihuwa, ki zauna da ‘ya’ya biyu ko uku, shi kuma ya je, ya yi ta aure, ya more rayuwarsa, tun da ba ‘ya’ya da yawa a gabansa.”

Baba Gambo ta karÉ“a, “To bari in gaya miki, mazan yanzu ‘ya’ya ake juye musu, kamata ya yi, shekaru biyar kina da ‘ya’ya shida, a lokacin da kuke shekaru goma da aure kina da ‘ya’ya goma ko sha É—aya, idan ya ga yawan ‘ya’yan ba zai iya tunkarar wata shegiyar ‘yar da neman aure ba, ke ko ita yarinyar duk tsiyarta idan ta san yana da ‘ya’ya da yawa ba za ta shigo miki gida a matsayin kishiya ba, don za ta ce rainon ‘ya’ya za ta zo yi masa a banza...”

A daidai lokacin na yi sallama, na shiga falon, suka yi tsuru-tsuru suna kallona, na gaishe da Baba Gambo, ta amsa ciki-ciki. A sanyaye na fara magana.

“Baba wannan abin da kuke magana a kai ba haka ba ne a raina, ban taÉ“a tunanin zan Æ™ara aure ba, sai dai abin da Allah ya nufa, bare in sa Nabila ta yi tazara saboda wannan abu da kuke tunani. Mun yi haka ne don lafiyarta da inganta rayuwarmu. Batun aure kuwa, ya kamata ku sani idan na so ko ‘ya’ya É—ari gare ni, akwai ‘yanmata da yawa da za su iya aure na a haka. Ni da Nabila muna son juna, muna son mu rayu har abada a cikin kyakkyawar rayuwa, don haka babu wannan abu da kuke magana...”

Har na gama maganganuna na fita ba su tanka min ba. Ashe dai baya na bari da ƙura don kuwa maganganun da na faɗa musu ko a jikinsu, haka suka zuge Nabila tas!

Watarana ina zaune a falo, ta shigo rai a ɓace.

“Ya aka yi abar Æ™aunar?” Na ce da ita. Ta kawar da kai.

“Habib ba zan Æ™ara yin tazarar haihuwa ba, don yana sa ni rashin lafiya. Yana rikita min al’ada ta.”

Na san ƙarya take yi, na yi ta lallashinta, amma fafur ta ƙi. Da na ɗan nuna mata ɓacin rai sai ta nuna kamar ta haƙura, ashe yaudara ta za ta yi, sun ƙulla mata abin da za ta yi idan na matsa.

Wata na gaba sai ga Nabila da ciki. Da na yi magana sai ta ce Allah ne ya yi ikonsa, ni kuma na san Æ™arya take, Æ™in shan maganin ta yi. Lokaci na yi ta haifo ‘yar da muka sa wa suna Zulaiha.

Muka ƙara hawa teburin tattaunawa, na nemi ta yi allura, ta ce sai dai ta sha magani. Da na nemi matsa mata a kan ta yi allurar, ta bijire min tare da yunƙurin yin yaji, dole na haƙura, na yarda ta sha maganin.

Aka kuma maimaitawa. Ta sake yaudara ta, ta Æ™i shan maganin. Wannan karo namiji ta haifa, sunan shi Shamsu. Cikin shekaru bakwai muna da ‘ya’ya huÉ—u.

Na sake nuna mata ɓacin raina sosai, a kan lallai sai ta yi allura, ta yarda aka yi mata wadda za ta yi wata uku. Bayan cikar wata ukun, na tuna mana lokacin sake yi ya yi, sai ta tubure cewar waccan allurar ba ta sake ta ba, wai ta tabbatar ba za a sami ciki ba, don haka ba za ta sake yin wata allurar ba.

Nan ma dai ciki ya bayyana. Wata takwas ta haifo Naziru. Muka kai ruwa rana wajen a sa mata abin tazarar na hannu, da ƙyar ta yarda aka sa. Ashe daga baya ta koma wani asibitin sun cire mata.

A cikin shekararmu ta goma sha biyu da aure muna da ‘ya’ya tara.

Sai wane babi, dole na saduda, ba don Allah ba, sai don yadda rayuwa ta bida ni. Abubuwa suka sakwarkwace, saboda:

Ban ninka samu ba, amma buƙatu sun ninku sun ruɓanya har sau biyar ko fi a kaina. Abinci, abubuwan buƙatun gida, harkar makarantun yara, babu abin da bai ninku ya ƙara ba.

Kafin wani lokaci jarina ya yi ƙasa sosai saboda tsadar kayan masarufi da na buƙatunmu. Na siyar da motata, don biyan kuɗin makarantar yara da siyen kayan abinci. Da tafiya ta ƙara nisa na siyar da gidan da muke ciki, muka koma gidan haya.

A yanzu, watanni sun Æ™aru, mun Æ™ara samun ‘ya’ya biyu sun zama su sha É—aya, da ni da ita mu sha uku ke nan. Rayuwarmu kacokam ta koma kan gwadaben Æ™arma-Æ™arma.

Na je ga Nabila ina duban ta. Zan yi magana, ta fashe da kuka.

“Kukan me kike yi?”

“Na san abin da za ka faÉ—a. Kuma tabbas ni ce sila, na kauce wa gaskiya ga halin da muka faÉ—a.”

Na zauna.

“In Æ™ara maimaita miki, kaso tamanin na rayuwar É—an’adam tana hannunsa. Allah ya yi masa komai tun da ya ba shi abubuwa guda uku; hankali da tunani da ilimi, sannan halak ne tsarin iyali a Musulunci. Allah zai tambayi duk wasu iyaye a kan ‘ya’yan da suka haifa, idan ka san akwai matsala, to kar ka haifa, hatta auren ma ba tilas ba ne a kanka idan akwai matsala.”

“Ni ganau ce ba jiyau ba Habib. Ko kana da damar É—aukar É—awainiyar wasu, idan suka yi yawa ba za ka iya ba. Yanzu me ya kamata mu yi.” Tana hawaye.

Muka yi shiru, muna duban juna.

Na gama

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

 

Friday, April 14, 2023

SHARHIN LITTAFIN JIKI MAGAYI



MATANIN LITTAFIN JIKI MAGAYI

Sunan littafi:                      Jiki Magayi

Marubuta:                          John Tafida Umaru Zariya da Rupert East

Shekarar Wannan Bugun:                1995

Madaba’a:                           Northern Nigeria Publishing Company (NNPC)

Bugawa:                               Ahmad Bello University Press, Samaru, Zaria

Yawan Shafuka:                    52

Mai Nazari:                         Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

 

Jiki Magayi labari ne na wani kasurgumin kuma shahararren attajiri mai suna Mallam Shaihu mazaunin cikin birnin Galma. Saboda yawan kudin Mallam Shaihu ba inda sunan shi bai kai ba (shafi na 1). Kai hatta shi kan shi Mallam Shaihu bai san yawan dukiyarsa ba (shafi na 2)

Sai dai kash! Duk da tarin dukiyar Mallam Shaihu, Allah bai taba ba shi haihuwa ba, ya yi aurarraki don samun haihuwa, amma bai taba samu ba. Haka nan ya batar da dukiya ba adadi a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori duk don neman maganin haihuwa, amma ko batan wata ba a taba samu a cikin matansa ba.

Damuwar Mallam Shaihu ta rashin haihuwa ta yawaita wanda har ta kai shi ga yin mafarki da wata yarinya a gidan Mallam Audu mai suna Zainabu, wanda a mafarkin aka yi masa isharar idan ya aure ta lallai zai sami haihuwa.

Mallam Shaihu bai yi kasa a guiwa ba ya tuntubi malamin duba da tsubbu a kan mafarkin da ya yi. Malamin ya duba masa, ya ba shi labari zai auri wata yarinya ‘yar gidan Mallam Audu din, kuma za su haihu, sai dai auren yana cike da wahala da da-na-sani, ya ba shi shawarar ya hakura da batun auren.

Mallam Shaihu ya yi ta tunani dangane da wannan al’amari, amma saboda son haihuwa ya shure maganar malamin kasa, ya sa aka kira masa Mallam Audu don neman auren ‘yarsa.

Yarinyar da Mallam Shaihu ya gani a mafarki ita ce Zainabu, sai dai tana da wanda take so, don haka ko da mahaifin Zainabu wato Mallam Audu ya zo gare shi ya sanar da shi cewa:

“Wannan magana tana da wuya, domin kuwa ita Zainabu, tun suna kanana akwai wani yaro sunansa Abubakar tare suka taso, tana sonsa, shi kuma yana son ta, har kuwa kowa ya sani ita zai aura…” (Shafi na 3)

Duk da haka Mallam Shaihu bai gamsu ba ya ci gaba da neman auren Zainabu, har a wajen malamin duba.

Mallam Shaihu ya nemi yardar Zainabu, amma ta ki, don ya cimma burinsa sai ya sa wani shahararren malamin tsubbu mai suna Mallam Sambo ya yi masa aiki a kan yarinyar wanda ya juye mata hankali ta dawo gare shi. Ta rabu da saurayinta Abubakar wanda aka yi musu ‘baiwa’ da shi.

Mallam Shaihu ya auri Zainabu bayan ya saki guda daga cikin matansa. Wannan abu ya tunzura Abubakar ya sha alwashin daukar fansa, ya kudire cewar in har a kan da ne aka yi masa haka, to zai yi maganin da sai albarkar da yake nema ga dan ta zama la’ana. Hakan ya sa, ya shiga fadi-tashi tsakanin bokaye da wahalar duniya a garuruwa, har sai da ya samo maganin da ya je, wanda a lokacin Mallam Shaihu da Zainabu sun haifi yaron kirki mai suna Abdullahi ana kiransa Kyauta, ya yi masa magani, yaron ya zama fitinanne kuma kasurgumin barawo har ya hadu da wani shahararren barawo mai suna Dogon Yaro.

A karshe a yawon yin sata har Kyauta ya je yin sata garin da mahaifinsa ya gudu, kuma gidansa tsautsayi ya sa, ya kashe uban.

Sharri dan aike, kuma alhaki kwikwiyo mai shi yakan bi, bayan mutuwar Mallam Shaihu, mahaifiyar Kyauta; Zainabu ta gaya wa danta wanda ya yi masa asiri ya zama barawo. Wannan ta sa Kyauta ya yi nadama kuma ya doshi Galma don daukar fansa a wurin Abubakar. Sai dai kash! Lokacin da ya isa Galma, har wajen Abubakar din, ya tarar da shi yana cikin tsananin rashin lafiya, ko da shi Abubakar din ya gan shi sai ya ce:

“Ka makara! Wata fansar sai gobe kiyama.” (shafi na 49) sai ya tuntsire ya mutu. Saboda yana cikin tsananin rashin lafiya.

A karshe Kyauta ya koma Ganye don dauko mahaifiyarsa. Dukiyar mahaifinsa kuwa bayan an yi mata kima an cire ushura aka damka masa komai. Ya tara dukkan malaman garin don yi wa ubansa addu’a ya raba musu ita. Haka ya rabar da kudi da kayayyakin mahaifinsa da takarce da dabbobi. Suka dawo Galma shi da mahaifiayrsa, anan ma aka ba shi gado, ya bai wa mahaifiyarsa, shi kuma ya yi sallama da ita don barin garin domin ya tafi neman rage alhakin da ya dauka. Ya fita daga shi sai sandarsa da gafaka da ‘yar buta.

 

Babban jigon littafin Jiki Magayi shi ne “neman/son haihuwa”, domin wadannan dalilai:

Misali a shafi na biyu, marubutan littafin sun ce:

 

“Shekararsa ashirin da yin aure amma bai taba haihuwa ba. Ya yi aure da yawa, kullum gidansa ba a rasa matan aure hudu. Ya batad da dukiya ba iyaka wajen malamai da bokaye da ‘yan bori garin neman maganin haihuwa, amma cikin matansa babu wadda ta taba ko batan wata. Ko yaushe idan ya tuna da wannan babbar hasara ta rashin da sai ransa ya dugunzuma..”

Haka a wannan shafin, a mafarkinsa sun ce:

“Godiya tana gidansa har ta haifa masa dan dukushi kyakkyawa…”

A shafi na uku (3)

“Amma don tsananin son da ya maida duk wannan ba a bakin kome ba idan bukatarsa ta biya.”

A shafi na takwas (8) an sake fito da jigond ai.

“….kuma ka cika aure-aure da yawa, duk wadda ka aura kuwa idan kuka yi ‘yan shekaru ka ga ba ta haihu ba sai ka sake ta da cin zarafi…”

A shafi na sha uku (13):

“Dalili dai yana son da ne, an kuwa gaya masa idan ya auri yarinyar nan zai samu…”

A shafi na sha hudu (14):

“To, tun da yake kwadayin da ne ya sa ya yi mini wannan abu…”

A shafi na sha bakwai ma an bayyana jigon:

“….sa’an nan zai ga kwansa…”

“Zainabu ta sami ciki….” Shafi na takwas ke nan da sauransu.

 

KANANAN JIGOGI

Bayan babban jigon “neman haihuwa” littafin Jiki Magaji yana da kananan jigogi masu mara masa baya kamar:

Daukar fansa,

Sata,

Bokanci

=> Daukar Fansa – mun ji yadda Abubakar ya sha alwashin daukar fansar kwace masa masoyiya da Mallam Shaihu ya yi, shi ya sa ya nemo maganin da ya sa dansa Kyauta ya zama kasurgumin barawo.

Haka shi ma Kyauta da ya sami labarin wanda ya yi masa magani har ya zama barawo, ya sha alwashin zuwa don ya dauki fansa a kan Abubakar.

 

=> Sata – Kyauta ya zama kasurgumin barawo tun yana yaro, har ya bar gida, ya je garuruwa yana sata – ta dalilin sata ya hadu da kasurgumin barawo mai suna Dogon Yaro, kuma ta dalilin sata ya kashe mahaifinsa.

 

=> Bokanci/Tsubbu – wadannan suna cikin kananan jigo na labarin Jiki Magayi – domin tun a farko-farkon labarin mun ji yadda Mallam Shaihu ya rinka batar da dukiya mai yawa a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori wajen neman haihuwa (shafi na biyu, sakin layi na 1)

Bugu da kari da malamin duban kasa ya yi amfani wajen juyo da hankalin Zainabu gare shi (shafi na 6)

Shi ma Abubakar ya shiga duniya ne neman shahararren malami don daukar fansa (shafi na 11). Kuma har ya riski malamin mai suna Tausayinka-Da-Sauki wato Zakari (shafi na 12) wanda daga jin sunan ka san boka ne.

 

WURARE DA GARURUWA 

A cikin littafin Jiki Magayi marubutan sun yi amfani da garuruwa kamar irin su: Birnin Galma, Yale, Dawan Rukuki, Sanga, Rimi, Garuje da sauransu.

KA'IDOJIN RUBUTU

In ban da amfani da wasu daga tsoffin salon ka’idojin rubutun Hausa da marubutan suka yi, to a littafin an kiyaye ka’idojin rubutu yadda ya kamata. Misalan tsoffin ka’idojin rubutun sun hadar da:

- Kwantad da maimakon kwantar da

- sanad da maimakon sanar da

- sayad da maimakon sayar da

- sa’ad da maimakon sa’ar da

- garimmu maimakon garinmu

- Halimmu maimakon halinmu

- lalle maimakon lallai

- izni maimakon izini

- ko me maimakon komai

Sai kuma wajen da suke rubuta sunayen lokuta da kananan baki. Ban da wadannan lallai marubutan sun yi kokarin kiyaye ka’idojin rubutu.

Sannan akwai wani abin dubawa a littafin, duk irin tafiye-tafiye da yada zango da shiga garuruwa da wasu taurarin littafin suka yi ba a nuna inda suka yi salla ba ko sau daya – sai dai kawai an ambaci sunayen sallolin Azahar da La’asar a matsayin lokaci kawai.

Haka nan yanayin littafin ya fi kama da fassara.

-Kabiru Yusuf Fagge (anka)

23 Ramadan 1444 = 14 April 2023

 

MAKAHO MAI FITILA

MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...