Monday, July 31, 2023



 

KARATUN LITTAFIN TUNANINKA KAMANNINKA NA BASHIR OTHMAN TOFA

Gabatarwa

Insha Allahu za mu fara karanta littafin Tunaninka Kamanninka.

TA’ALIKI

 

Da sunan Allah Mai cikakken iko, Mahaliccin Komai, Mai yin abindaYa so.

 

TUNANINKA KAMANNINKA” yunquri ne mai kyau, wajen kyautata xabi’un al’umma tareda xorasu bisa tafarkin da zai ba su xaukaka a duniya da lahira. Marubucin ya nutsu wajen fahimtar halin xan-Adam da kuma irin cutar da ke damun zuciyarsa, sannan kuma ya bayar da maganin cututtukan.  Haqiqa,  a  ganina  ya  gano  maganin. Duk wanda ya sha maganin da Alhaji Bashir Othman Tofa ya ba wa zuciya a wannan littafi, to ya waraka. Sha yanzu magani yanzu!

 

Marubucin, wanda gogagge ne a fannin rayuwa, ya fito da salon rubutun da babu shi a harshen Hausa. Rubutu  a  janibin  falsafa  tsohon  al’amari  ne  a tarihin duniya. Amma a harshenmu, yanzu muka ce: “Assalamu Alaikum“.

 

Allah (swt) Ya qara tabbatar da abinda nake ta tsokaci da shi kullum, cewa: baiwa ta Allah (swt) ce. Yana bayar da ita inda Yake so. Don haka ko yaushe sai mu duba mu gani da idon basira cewa ta wacce hanya za mu iya amfani da baiwar da Allah (swt)   Ya   ba   wa   kowannenmu   domin   qara kusantarSa (Allah swt), da ci gabanmu baki xaya, ba tareda mun raina mafitar basirar ba.

 

Wannan littafi mai albarka, bai sauka daga qa’idar shari’a ko ta xabi’ar rayuwa ba. Zai yi fa’ida ga duk jinsi na al’umma, musammam manyan gobe.

 

Ina mai jan hankalin jama’a da su karanci wannan littafi tareda aiki da shi domin samun al’umma tagari.

 

Allah (swt) Ya albarkaci marubucin da masu karatu baki xaya.

 

Wama taufiq illa billah!

 

 

 

Alhaji (Dr.) Yusuff Maitama Sule

Xan Masanin Kano

 

20th June, 1997



MUHIMMAN TUBALAN GINA RAYUWA

 

Wani Malami ne ya ke yiwa xalibansa misali. Sai ya xauko tukunyar gilashi ya ajiye a kan tebur, sannan ya xauko duwatsu kamar curin fura ya ringa sa su cikin tukunyar har sai da ta cika da su yadda ba wani dutse irinsu da zai shiga. Da ya gama, sai ya tam- bayi xaliban, “Tukunyar ta cika?” Suka ce, I, ta cika.” Malami ya ce, “Kun yi kuskure. Ba ta cika ba. Bari kuma ku gani.”

Ya sunkuya ya xauko kwandon tsakuwa ya ringa zuba su a cikin tukunyar, har sai da ya cike guraben da ke tsakanin duwatsun.

Sannan ya kalle su ya sake tambayarsu, “Yanzu fa?” Sai xalibai

suka yi shiru. Can, sai wani ya ce, “Wataqila.” Malami ya yi mur- mushi ya kaxa kansa.

Ya sake sunkuyawa, ya xauko kwanon rairayi, ya yi ta zuba shi cikin tukunya, har sai da ya cike duk xan gurbin da ya saura tsa-

kanin tsakuwoyin. Sannan ya tambayesu. Suka ce, Basu sani ba.

Sai kuma ya xauko kwanon ruwa, ya yi ta zuba shi cikin tu- kunya, har sai da ta cika maqil, bayan rairayi ya tsotsi abinda zai

iya. Sannan da kansa ya ce wa xaliban, “To yanzu watakila ta cika.

Kun fahimci darasin wannan misali?”

Wani haziqin xalibi ya ce, “Duk qaracin lokacinka, in ka yi qoqari zaka yi yin wasu abubuwan dabam.”

Malam ya ce, “A a. Darasin shi ne, idan ba ka fara shigar da

muhimman tubalan rayuwarka da farko ba, to ba zaka iya shigar da su gaba xaya nan gaba ba. Lallai ka yi tunaninsu, ka sansu, sannan ka  jera  su  daidai  muhimmancinsu;  manyan  da  farko  sannan qananan, ka kuma tunkaresu cikin hanzari da lura. Komai daidai muhimancinsa. Da da rairayin na fara da tsakuwar ba ta shiga ba, da kuma ko dutse xaya ba zan iya sa wa ba. Amma yanzu ga shi komai ya shiga ya sami mazauninsa.

 

Waxannene naka muhimman tubalan rayuwar?

Ka sansu ka kuma tsara su daidai da muhimancinsu?

Ya za ka tsara waxannan? Addininka, Ilminka, Iyalinka, Sana’arka, Mutumcinka, Tausayawarka da Jin-daxinka da ….?

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...