Friday, April 14, 2023

SHARHIN LITTAFIN JIKI MAGAYI



MATANIN LITTAFIN JIKI MAGAYI

Sunan littafi:                      Jiki Magayi

Marubuta:                          John Tafida Umaru Zariya da Rupert East

Shekarar Wannan Bugun:                1995

Madaba’a:                           Northern Nigeria Publishing Company (NNPC)

Bugawa:                               Ahmad Bello University Press, Samaru, Zaria

Yawan Shafuka:                    52

Mai Nazari:                         Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

 

Jiki Magayi labari ne na wani kasurgumin kuma shahararren attajiri mai suna Mallam Shaihu mazaunin cikin birnin Galma. Saboda yawan kudin Mallam Shaihu ba inda sunan shi bai kai ba (shafi na 1). Kai hatta shi kan shi Mallam Shaihu bai san yawan dukiyarsa ba (shafi na 2)

Sai dai kash! Duk da tarin dukiyar Mallam Shaihu, Allah bai taba ba shi haihuwa ba, ya yi aurarraki don samun haihuwa, amma bai taba samu ba. Haka nan ya batar da dukiya ba adadi a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori duk don neman maganin haihuwa, amma ko batan wata ba a taba samu a cikin matansa ba.

Damuwar Mallam Shaihu ta rashin haihuwa ta yawaita wanda har ta kai shi ga yin mafarki da wata yarinya a gidan Mallam Audu mai suna Zainabu, wanda a mafarkin aka yi masa isharar idan ya aure ta lallai zai sami haihuwa.

Mallam Shaihu bai yi kasa a guiwa ba ya tuntubi malamin duba da tsubbu a kan mafarkin da ya yi. Malamin ya duba masa, ya ba shi labari zai auri wata yarinya ‘yar gidan Mallam Audu din, kuma za su haihu, sai dai auren yana cike da wahala da da-na-sani, ya ba shi shawarar ya hakura da batun auren.

Mallam Shaihu ya yi ta tunani dangane da wannan al’amari, amma saboda son haihuwa ya shure maganar malamin kasa, ya sa aka kira masa Mallam Audu don neman auren ‘yarsa.

Yarinyar da Mallam Shaihu ya gani a mafarki ita ce Zainabu, sai dai tana da wanda take so, don haka ko da mahaifin Zainabu wato Mallam Audu ya zo gare shi ya sanar da shi cewa:

“Wannan magana tana da wuya, domin kuwa ita Zainabu, tun suna kanana akwai wani yaro sunansa Abubakar tare suka taso, tana sonsa, shi kuma yana son ta, har kuwa kowa ya sani ita zai aura…” (Shafi na 3)

Duk da haka Mallam Shaihu bai gamsu ba ya ci gaba da neman auren Zainabu, har a wajen malamin duba.

Mallam Shaihu ya nemi yardar Zainabu, amma ta ki, don ya cimma burinsa sai ya sa wani shahararren malamin tsubbu mai suna Mallam Sambo ya yi masa aiki a kan yarinyar wanda ya juye mata hankali ta dawo gare shi. Ta rabu da saurayinta Abubakar wanda aka yi musu ‘baiwa’ da shi.

Mallam Shaihu ya auri Zainabu bayan ya saki guda daga cikin matansa. Wannan abu ya tunzura Abubakar ya sha alwashin daukar fansa, ya kudire cewar in har a kan da ne aka yi masa haka, to zai yi maganin da sai albarkar da yake nema ga dan ta zama la’ana. Hakan ya sa, ya shiga fadi-tashi tsakanin bokaye da wahalar duniya a garuruwa, har sai da ya samo maganin da ya je, wanda a lokacin Mallam Shaihu da Zainabu sun haifi yaron kirki mai suna Abdullahi ana kiransa Kyauta, ya yi masa magani, yaron ya zama fitinanne kuma kasurgumin barawo har ya hadu da wani shahararren barawo mai suna Dogon Yaro.

A karshe a yawon yin sata har Kyauta ya je yin sata garin da mahaifinsa ya gudu, kuma gidansa tsautsayi ya sa, ya kashe uban.

Sharri dan aike, kuma alhaki kwikwiyo mai shi yakan bi, bayan mutuwar Mallam Shaihu, mahaifiyar Kyauta; Zainabu ta gaya wa danta wanda ya yi masa asiri ya zama barawo. Wannan ta sa Kyauta ya yi nadama kuma ya doshi Galma don daukar fansa a wurin Abubakar. Sai dai kash! Lokacin da ya isa Galma, har wajen Abubakar din, ya tarar da shi yana cikin tsananin rashin lafiya, ko da shi Abubakar din ya gan shi sai ya ce:

“Ka makara! Wata fansar sai gobe kiyama.” (shafi na 49) sai ya tuntsire ya mutu. Saboda yana cikin tsananin rashin lafiya.

A karshe Kyauta ya koma Ganye don dauko mahaifiyarsa. Dukiyar mahaifinsa kuwa bayan an yi mata kima an cire ushura aka damka masa komai. Ya tara dukkan malaman garin don yi wa ubansa addu’a ya raba musu ita. Haka ya rabar da kudi da kayayyakin mahaifinsa da takarce da dabbobi. Suka dawo Galma shi da mahaifiayrsa, anan ma aka ba shi gado, ya bai wa mahaifiyarsa, shi kuma ya yi sallama da ita don barin garin domin ya tafi neman rage alhakin da ya dauka. Ya fita daga shi sai sandarsa da gafaka da ‘yar buta.

 

Babban jigon littafin Jiki Magayi shi ne “neman/son haihuwa”, domin wadannan dalilai:

Misali a shafi na biyu, marubutan littafin sun ce:

 

“Shekararsa ashirin da yin aure amma bai taba haihuwa ba. Ya yi aure da yawa, kullum gidansa ba a rasa matan aure hudu. Ya batad da dukiya ba iyaka wajen malamai da bokaye da ‘yan bori garin neman maganin haihuwa, amma cikin matansa babu wadda ta taba ko batan wata. Ko yaushe idan ya tuna da wannan babbar hasara ta rashin da sai ransa ya dugunzuma..”

Haka a wannan shafin, a mafarkinsa sun ce:

“Godiya tana gidansa har ta haifa masa dan dukushi kyakkyawa…”

A shafi na uku (3)

“Amma don tsananin son da ya maida duk wannan ba a bakin kome ba idan bukatarsa ta biya.”

A shafi na takwas (8) an sake fito da jigond ai.

“….kuma ka cika aure-aure da yawa, duk wadda ka aura kuwa idan kuka yi ‘yan shekaru ka ga ba ta haihu ba sai ka sake ta da cin zarafi…”

A shafi na sha uku (13):

“Dalili dai yana son da ne, an kuwa gaya masa idan ya auri yarinyar nan zai samu…”

A shafi na sha hudu (14):

“To, tun da yake kwadayin da ne ya sa ya yi mini wannan abu…”

A shafi na sha bakwai ma an bayyana jigon:

“….sa’an nan zai ga kwansa…”

“Zainabu ta sami ciki….” Shafi na takwas ke nan da sauransu.

 

KANANAN JIGOGI

Bayan babban jigon “neman haihuwa” littafin Jiki Magaji yana da kananan jigogi masu mara masa baya kamar:

Daukar fansa,

Sata,

Bokanci

=> Daukar Fansa – mun ji yadda Abubakar ya sha alwashin daukar fansar kwace masa masoyiya da Mallam Shaihu ya yi, shi ya sa ya nemo maganin da ya sa dansa Kyauta ya zama kasurgumin barawo.

Haka shi ma Kyauta da ya sami labarin wanda ya yi masa magani har ya zama barawo, ya sha alwashin zuwa don ya dauki fansa a kan Abubakar.

 

=> Sata – Kyauta ya zama kasurgumin barawo tun yana yaro, har ya bar gida, ya je garuruwa yana sata – ta dalilin sata ya hadu da kasurgumin barawo mai suna Dogon Yaro, kuma ta dalilin sata ya kashe mahaifinsa.

 

=> Bokanci/Tsubbu – wadannan suna cikin kananan jigo na labarin Jiki Magayi – domin tun a farko-farkon labarin mun ji yadda Mallam Shaihu ya rinka batar da dukiya mai yawa a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori wajen neman haihuwa (shafi na biyu, sakin layi na 1)

Bugu da kari da malamin duban kasa ya yi amfani wajen juyo da hankalin Zainabu gare shi (shafi na 6)

Shi ma Abubakar ya shiga duniya ne neman shahararren malami don daukar fansa (shafi na 11). Kuma har ya riski malamin mai suna Tausayinka-Da-Sauki wato Zakari (shafi na 12) wanda daga jin sunan ka san boka ne.

 

WURARE DA GARURUWA 

A cikin littafin Jiki Magayi marubutan sun yi amfani da garuruwa kamar irin su: Birnin Galma, Yale, Dawan Rukuki, Sanga, Rimi, Garuje da sauransu.

KA'IDOJIN RUBUTU

In ban da amfani da wasu daga tsoffin salon ka’idojin rubutun Hausa da marubutan suka yi, to a littafin an kiyaye ka’idojin rubutu yadda ya kamata. Misalan tsoffin ka’idojin rubutun sun hadar da:

- Kwantad da maimakon kwantar da

- sanad da maimakon sanar da

- sayad da maimakon sayar da

- sa’ad da maimakon sa’ar da

- garimmu maimakon garinmu

- Halimmu maimakon halinmu

- lalle maimakon lallai

- izni maimakon izini

- ko me maimakon komai

Sai kuma wajen da suke rubuta sunayen lokuta da kananan baki. Ban da wadannan lallai marubutan sun yi kokarin kiyaye ka’idojin rubutu.

Sannan akwai wani abin dubawa a littafin, duk irin tafiye-tafiye da yada zango da shiga garuruwa da wasu taurarin littafin suka yi ba a nuna inda suka yi salla ba ko sau daya – sai dai kawai an ambaci sunayen sallolin Azahar da La’asar a matsayin lokaci kawai.

Haka nan yanayin littafin ya fi kama da fassara.

-Kabiru Yusuf Fagge (anka)

23 Ramadan 1444 = 14 April 2023

 

4 comments:

  1. Shekarar bugawa yakamata ka saka first publishing year da sauran shekaru da aka sake bugawa.

    ReplyDelete
  2. Thanks and that i have a nifty present: Whole House Reno house renovation shows on netflix

    ReplyDelete
  3. Yakamata ka ba takaitacin tarihin ma rubutwn

    ReplyDelete

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...