Saturday, July 15, 2023

'YA'YA BIYU

 ‘YA’YA BIYU

(Family Planning Saga)

Muna zaune ni da budurwata Nabila, muna hira. Ta dube ni, tare da tambaya ta.

“Yau babu wani sharaɗi ko shawarar na ji ka yi shiru?”

Na bi ta da murmushi.

“Kamar kin shiga raina, yunƙurin nan da kika ga na yi, zan gaya miki ne, sai kika tambaya.”

“To ina sauraronka.” Tana murmushi take maganar.

“Nabila, a rayuwata ina son ‘ya’ya, amma maganar gaskiya ina son shekaru goma sha biyar ɗin farkon aurenmu mu haifi ‘ya’ya biyu kawai.”

Ta kalle ni da mamaki a idonta.

“Na san kana da hujja, amma ko za ka iya gaya min tare da ƙarin bayani. Iya sani na, Allah ne mai yi ga rayuwar halittunsa, amma ta ya za mu yi haka?”

“Good, Nabila kaso tamanin na rayuwar ɗan’adam tana hannunsa, tun da Allah ya yi mu mutanen ya ba mu hankali da tunani da ilimi, don haka tsara haifar ‘ya’ya biyu a cikin shekaru goma sha biyar zuwa ashirin abu ne mai sauƙi.”

“Na ji wannan, saura dalili.” Ta ce da ni.

“Lafiyar ki, da tarbiyantar da ‘ya’yan da ɗora su a kan kyakkyawar rayuwa gwargwadon iyawarmu da biyan haƙƙoƙinsu har su hau kan gwadaben rayuwa mai inganci. Sannan sai a nemi wani ko wasu, su ne dalilaina.”

Ta yi shiru, kafin ta numfasa.

“Na ɗauka Allah ne mai shiryarwa da bai wa ɗan’adam abinci da arziƙinsa tun daga lokacin da yake halittarsa?” Ta tuhuma.

“Allah shi ne mai shiriya, amma bisa mataki-mataki ciki har da wanda ya ɗora wa iyaye na haƙƙoƙin ci da sha da tarbiyya.” Na numfasa, “Nabila komai da kika sani Allah ya yi shi bisa sanadi, sanadin shi ne iyaye su kula da abubuwan da na lissafa miki, idan suka gaza da gangan sai Allah ya kama su. Ai Allah shi ne mai halitta, me ya sa bai ce idan aka Haifa, a watsar da su za su tashi da tarbiyya, za su ci, su sha su tufatu daga sama ba, ya bai wa iyaye alhakin tarbiyyar? Saboda haka tsarinsa yake.”

Yayin da na yi shiru, ta dube ni tana son yin tambaya, ta kasa, na ɗora da cewa.

“Don haka, Nabila muna buƙatar mu yi wannan aikin idan mun yi aure, Allah ya ba mu haihuwa, mu sami ‘ya’ya biyun mu yi namu aikin, Allah ya yi na shi.”

Ta yi ajiyar zuciya.

“Na gamsu da bayaninka Habib.”

Bayan aurenmu, a cikin shekaru uku Allah ya ba mu ‘ya’ya biyu mace; Fatima da namiji Muhammad (Al’amin)

Muna cikin shekara ta huɗu da aurenmu, da ‘ya’yanmu guda biyu cikin farin ciki da kula da soyayya da nutsuwa, a gidan kaina nake, madaidaici ne mai ɗakunan Nabila da falonta, ni ma nawa ɗakin da falo, da ɗakin saukar baƙi, haka su ma yara kowa da nashi ɗakin da banɗakuna daban-daban. Motata ta kai miliyan biyu da rabi.

Harkar siyar da shaddodi da yaduka su ne kasuwancina. Ina kula da ‘yan’uwana da na Nabila gwargwadon iyawa ta.

A wannan shekarar ne ‘yan’uwan Nabila da iyayenta mata suka fuskanci ta tsallake shekaru biyu ba ɓatan wata, ba ɓari ba ciki. Take suka sa ƙahon zuƙa sai da suka gano jinkirin haihuwa muke yi.

Watarana ina ɗakina a zaune, Maman Nabila; Baba Gambo da yayarta mai suna Atuwa suka zo gidan, ban yi tsammanin sun san ina nan ba, na ji suna hira, suna ɗaga murya.

“Ke muke saurare, gaya mana abin da ya sa kuke yin family planning?” cewar Baba Gambo.

“Gaskiya tun kafin aure mun yi wannan yarjejeniyar da shi. Kuma ni ina ganin ba wani abu ba ne...”

Atuwa ta katse ta, “Ke sakarya, kya ce ba wani abu ba ne mana, tun da an ninke ki baibai. To tsaya ki ji in gaya miki gaula ya mayar da ke. Kina nan zaune da ‘ya’ya biyu zai ƙaro aure har biyu, ke har uku ma, ai haka mazan yanzu suke, su mayar da mace shashasha, su banka miki maganin rashin haihuwa, ki zauna da ‘ya’ya biyu ko uku, shi kuma ya je, ya yi ta aure, ya more rayuwarsa, tun da ba ‘ya’ya da yawa a gabansa.”

Baba Gambo ta karɓa, “To bari in gaya miki, mazan yanzu ‘ya’ya ake juye musu, kamata ya yi, shekaru biyar kina da ‘ya’ya shida, a lokacin da kuke shekaru goma da aure kina da ‘ya’ya goma ko sha ɗaya, idan ya ga yawan ‘ya’yan ba zai iya tunkarar wata shegiyar ‘yar da neman aure ba, ke ko ita yarinyar duk tsiyarta idan ta san yana da ‘ya’ya da yawa ba za ta shigo miki gida a matsayin kishiya ba, don za ta ce rainon ‘ya’ya za ta zo yi masa a banza...”

A daidai lokacin na yi sallama, na shiga falon, suka yi tsuru-tsuru suna kallona, na gaishe da Baba Gambo, ta amsa ciki-ciki. A sanyaye na fara magana.

“Baba wannan abin da kuke magana a kai ba haka ba ne a raina, ban taɓa tunanin zan ƙara aure ba, sai dai abin da Allah ya nufa, bare in sa Nabila ta yi tazara saboda wannan abu da kuke tunani. Mun yi haka ne don lafiyarta da inganta rayuwarmu. Batun aure kuwa, ya kamata ku sani idan na so ko ‘ya’ya ɗari gare ni, akwai ‘yanmata da yawa da za su iya aure na a haka. Ni da Nabila muna son juna, muna son mu rayu har abada a cikin kyakkyawar rayuwa, don haka babu wannan abu da kuke magana...”

Har na gama maganganuna na fita ba su tanka min ba. Ashe dai baya na bari da ƙura don kuwa maganganun da na faɗa musu ko a jikinsu, haka suka zuge Nabila tas!

Watarana ina zaune a falo, ta shigo rai a ɓace.

“Ya aka yi abar ƙaunar?” Na ce da ita. Ta kawar da kai.

“Habib ba zan ƙara yin tazarar haihuwa ba, don yana sa ni rashin lafiya. Yana rikita min al’ada ta.”

Na san ƙarya take yi, na yi ta lallashinta, amma fafur ta ƙi. Da na ɗan nuna mata ɓacin rai sai ta nuna kamar ta haƙura, ashe yaudara ta za ta yi, sun ƙulla mata abin da za ta yi idan na matsa.

Wata na gaba sai ga Nabila da ciki. Da na yi magana sai ta ce Allah ne ya yi ikonsa, ni kuma na san ƙarya take, ƙin shan maganin ta yi. Lokaci na yi ta haifo ‘yar da muka sa wa suna Zulaiha.

Muka ƙara hawa teburin tattaunawa, na nemi ta yi allura, ta ce sai dai ta sha magani. Da na nemi matsa mata a kan ta yi allurar, ta bijire min tare da yunƙurin yin yaji, dole na haƙura, na yarda ta sha maganin.

Aka kuma maimaitawa. Ta sake yaudara ta, ta ƙi shan maganin. Wannan karo namiji ta haifa, sunan shi Shamsu. Cikin shekaru bakwai muna da ‘ya’ya huɗu.

Na sake nuna mata ɓacin raina sosai, a kan lallai sai ta yi allura, ta yarda aka yi mata wadda za ta yi wata uku. Bayan cikar wata ukun, na tuna mana lokacin sake yi ya yi, sai ta tubure cewar waccan allurar ba ta sake ta ba, wai ta tabbatar ba za a sami ciki ba, don haka ba za ta sake yin wata allurar ba.

Nan ma dai ciki ya bayyana. Wata takwas ta haifo Naziru. Muka kai ruwa rana wajen a sa mata abin tazarar na hannu, da ƙyar ta yarda aka sa. Ashe daga baya ta koma wani asibitin sun cire mata.

A cikin shekararmu ta goma sha biyu da aure muna da ‘ya’ya tara.

Sai wane babi, dole na saduda, ba don Allah ba, sai don yadda rayuwa ta bida ni. Abubuwa suka sakwarkwace, saboda:

Ban ninka samu ba, amma buƙatu sun ninku sun ruɓanya har sau biyar ko fi a kaina. Abinci, abubuwan buƙatun gida, harkar makarantun yara, babu abin da bai ninku ya ƙara ba.

Kafin wani lokaci jarina ya yi ƙasa sosai saboda tsadar kayan masarufi da na buƙatunmu. Na siyar da motata, don biyan kuɗin makarantar yara da siyen kayan abinci. Da tafiya ta ƙara nisa na siyar da gidan da muke ciki, muka koma gidan haya.

A yanzu, watanni sun ƙaru, mun ƙara samun ‘ya’ya biyu sun zama su sha ɗaya, da ni da ita mu sha uku ke nan. Rayuwarmu kacokam ta koma kan gwadaben ƙarma-ƙarma.

Na je ga Nabila ina duban ta. Zan yi magana, ta fashe da kuka.

“Kukan me kike yi?”

“Na san abin da za ka faɗa. Kuma tabbas ni ce sila, na kauce wa gaskiya ga halin da muka faɗa.”

Na zauna.

“In ƙara maimaita miki, kaso tamanin na rayuwar ɗan’adam tana hannunsa. Allah ya yi masa komai tun da ya ba shi abubuwa guda uku; hankali da tunani da ilimi, sannan halak ne tsarin iyali a Musulunci. Allah zai tambayi duk wasu iyaye a kan ‘ya’yan da suka haifa, idan ka san akwai matsala, to kar ka haifa, hatta auren ma ba tilas ba ne a kanka idan akwai matsala.”

“Ni ganau ce ba jiyau ba Habib. Ko kana da damar ɗaukar ɗawainiyar wasu, idan suka yi yawa ba za ka iya ba. Yanzu me ya kamata mu yi.” Tana hawaye.

Muka yi shiru, muna duban juna.

Na gama

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

 

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...