SOYAYYA A BAHAUSHIYAR AL’ADA
An sha buga muhawara, ana cewa sam Bahaushe bai iya soyayya ba, kuma sau tari sai waɗanda suka ɗauki ɓangaren cewa Bahaushen bai iya soyayyar ba sun yi nasara, kuma sam ba haka ba ne, ba wai soyayya ce Bahaushe bai iya ba, a’a fitsara ce dai bai iya ba, sannan kuma al’adarsa ba ta yi kama da irin abubuwan da ake gani a matsayin soyayya ba.
A fagen soyayya Bahaushe mutum ne mai kunya da haƙuri da dauriya da kuma kawar da kai da bin maganar magabatansa sau da ƙafa.
A da, a gargajiyar Bahaushe akan ɗaurawa saurayi aure ba tare da ya ga budurwar da aka yi musu auren ba, haka ita ma budurwar akan yi mata auren ba tare da sanin mijin ba, kuma su tare, su zauna lafiya, zaman aure mai nagarta, zaman soyayya.
A rayuwar Hausawa akwai wata al’ada ta tsarance, inda ake haɗa masoya, wato saurayi da budurwa su kwana a ɗaki guda, kuma su wayi gari ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba duk kuwa da irin son junansu da suke yi, wannan ya nuna irin kyakkyawar halayar Bahaushe ta fuskar tsari irin na soyayya.
A Bahaushiyar al’ada idan budurwa tana soyayya da saurayi ba ta iya zuwa gidansu don ziyara ko wai kawai don ta gan shi, sai dai idan wani babban dalili ne kamar rashin lafiya ko mutuwa ko wani biki na musamman.
Haka nan budurwa Bahaushiya ba ta iya bin hanyar da ta san za ta haɗu da saurayinta. Haka kuma da wuya ka ji budurwa tana ambatar sunan saurayinta kai tsaye, kamar yadda shi ma saurayin da wuya ka ji yana kiran sunan budurwarsa sai dai su ba junansu wani sunan daban.
Idan suka yi aure kuwa, to matar nan ba ita ba faɗar sunan mijin kuma a nan za ka ga soyayya cikin ladabi da biyayya. Ke nan Bahaushe ya iya soyayya amma cikin kunya da girmamawa.
Idan saurayi Bahaushe ya ga budurwa yakan gaya wa ƙawarta ta gaya mata yana son ta, ko ya gaya wa abokinsa shi kuma ya gaya mata.
Sannan akwai tsarin fara tuntuɓar gidan budurwa kafin saurayi ya je wajenta zance.
A rayuwar Hausawa ta soyayya da yamma ido na ganin ido saurayi yake zuwa zance wajen budurwa. Kuma yakan je shi da abokinsa ko abokansa, ita kuma budurwa ta fito tare da ƙawarta ko ƙanwarta.
Ko a dandali, akwai yanayin kunya da tsarin basarwa tsakanin saurayi da budurwa. A soyayyar Bahaushe budurwa ba ta karɓar kuɗin saurayi, duk kuɗin da aka ga saurayi ya kai gidan budurwa, to an san da zuwan kuɗin da kuma matsayin kuɗin a wurin yarinyar, kamar kuɗin toshi ko kuɗin na-gani-ina-so da sauransu.
A da, a dandali ‘yanmata sukan rera waƙoƙin soyayya a tsaftace cikin nuna irin kyakkyawar ɗabi’ar Bahaushe. Misali a wata waƙa mai suna “Masoyi” ‘yanmatan sukan rera waƙar tun daga farkonta har ƙarshe babu inda budurwa ke ambaton sunan saurayin ta ƙarara, sai dai sakaye ta fuskar sana’a ko aikinsa, misali a waƙar:
Ayye yaraye alo maraya,
Ayye yeraye.
Nawa masoyin zan faɗa ku jiye,
Ayye yeraye.
Ni kan nawa ɗan malami ne,
Ayye yeraye.
Mu ci aya, mu kwana cin aya,
Ayye yeraye.
Har aya ta kwana bayanmu,
Daidai muwa,
Ayye yeraye.
Ni ko nawa mai sa da goro,
Ayye yeraye.
Mu ci goro ya kwana bayanmu
Daidai da muwa,
Ayye yeraye.
Har ƙarshe inda suke jero sunayen ayyuka da sana’o’in samarin, ba su damu da faɗin sunayensu ba kowa ya ji, ya san da wanda take (a duba cikin littafin Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigogi na Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, sh. 213-217 don ganin cikakkiyar waƙar)
Me ya faru?
Soyayyar Bahaushe ba ta fara gurɓacewa ba sai da ya haɗu da bakin al’ummu, ta yadda wasu al’adu suka ratsa al’adar Bahaushe, wasu abubuwa suka shigar masa. A cikin al’adun wasu don namiji ya riƙe mace ko ƙani ya rungumi ƙanwarsa ko ya ta sumbaci ubanta ba komai ba ne, ko kuma yarinya da ta fara balaga ta rinƙa yawo ba malulluɓi ko riga su ba komai ba ne, amma sam Bahaushe bai san wannan ba, abin kunya ne a wurin Bahaushe.
Kabiru Yusuf Anka

No comments:
Post a Comment