KIRARI
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Kirari wani tsararren zance ko magana ce ta hikima da akan shirya musamman don kambama mutum ko al’umma ko wani abu.
A takaice dai, kirari shi ne a yabi mutum da wasu kalmomi wadanda za su zuga shi. Sau da yawa akan yi wa mutum kirari a kai shi wani matsayin da bai kai ya je ba. A kan yi wa mutum kirari galibi ta hanyar siffanta shi da ko giwa, zaki, gobara, aljanu, ko wasu fitattun mutane ko masu mulki da sarakuna da makamantansu.
Abin sha'awa da kirari shi ne yadda mutane ke yi wa kansu kirari su koda kansu da kansu. Irin wadannan mutane masu koda kansu sun hada da magori, 'yan tauri, 'yan kokawa, 'yan farauta da sauransu.
Dangambo (1982) ya ce kirari na iya zama yabon kai kamar yadda 'yan tauri ko 'yan dambe ke yi, ko kuma yabon wani kamar yadda maroka ke yi da sauransu.
Kirari ya kunshi yabo da zuga ne. Cikin irin wannan yabo da zuga ne ake amfani da sarrafa harshe cikin hikima.
Zarruk (1986) kuwa ya ce kirari yana da salo irin na magana-magana, waka-waka. Shi ba waka ba saboda ba a rangwadar murya shi kuwa ba magana kara zube ba saboda kana iya jin wani kari a cikinsa. Amma duk da haka akan samu kirari ya fito a cikin waka.
Ire-iren kirari:
1. KIRARIN MUTUM
i. Dan’adam kuzajje da mugunta
ii. Dan’adam dan mutuwa jikan rasuwa
iii. Dan’adam kayan Allah ana tare da kai kana tare da halinka.
iv. Talaka bawan Allah
2. KIRARIN MATA
a) Mata kun riga bugu kun riga tashi
b) Hantsi kun leka gidan kowa, ba a leka gidanku ba
c) Matata iyayengida masu akwai da babu
d) Mata adon gari.
3. KIRARIN GARURUWA
i. Kano jalla babbar Hausa, yaro ko da mai ka zo an fi ka
ii. Katsina dakin kara
iii. Bichi kanwar birni
iv. Kura ta dan baba
v. Gwambawa diban fari ba a kwana da ku ba an tashi da ku.
vi. Lagos cunkus dakin tsummma makarin ki sai na dawo
vii. Gombe ta doma lahirar masu kudi
viii. Bauchi naman kai ga kitse ga tauri
ix. Kaduna birnin gwamna
4. KIRARIN JAMI'A
i. Jami'a iyakar boko
ii. Jami'a uwar boko
iii. Jami'a gidan ban kashi
iv. Jami'a matattarar Farfesa daga ke sai Turai.
5. KIRARIN SANA'A
i. Noma na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar
ii. Jima romon jaba ga kitse ga wari
iii. Saka ba don ke ba da an tafi tsirara
6. KIRARIN DUNIYA
i. Duniya ina za ki da mu
ii. Duniya rumfar kara, idan ka hau da karfi ta rushe
iii. Duniya hayakin taba
iv. Duniya kwallon mangoro, kana tsotsarta tana kubuce maka
v. Duniya mai ido a tsakar ka
vi. Duniya budurwar wawa
vii. Duniya makwantar rikici
viii. Duniya ba ta auren rago
ix. Duniya gidan kashe ahu
x. Duniya rawar 'yanmata
xi. Duniya mace da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba.
KADAN DAGA MISALAN KIRARI
1. Soja marmari daga nesa
2. Soja na gwamna ga rawa ga yaki
3. Soja birgimar hankaka
4. Moda shirgin banza ko a teku sai an danna
5. Danwake na jakala cimar kuturu, kowa ya ci dubu zai ci dan mutum
6. Zawo mai saka manya sauri
7. Daki ko kana zuba ka fi waje
8. Titi ba a tsallaka ka sai an waiga
9. Bature ci-gari ka kwana a daji
10. Bature, babban mutum da rigar yara
11. Fullo na Gambo, sha ruwa ka binne rijiya
12. Kudi, na gwamna masu gidan rana
13. Barebari, na Shehu Larabawan bidi'a
14. Huntu ubangijin mai riga
15. Gamji kashe na rabe jikinka
16. Gwari 'yar gidan kantoma kida kusa wasa nesa
17. Giwa bukkar daji
18. Gajere ba yaro ba
19. Dogo ka ci a reshe
20. Amarsu ta ango ba kya laifi ko kin kashe dan masu gida
21. Garin kwaki ko ka yi taimako an wahala
22. Sauro lange-lange mai ramar keta, rammme haukata kato, sa mutum ya mari jikinsa, mugu hana barci
23. Hadari malafar duniya
24. Jikin bushiya ba a masa wawan damka
25. Tsakin tama gagara tauna
26. Mushen kura ya wuce Allah Sarki
27. Damisa ki sabo
28. Bushiya kowa ya kwana da ke ya kwana salati
29. Damisa kin ki kallo biyu
30. Dan-tsakon jimina gagara daukar shaho.
Manazarta
Dan Hausa, A.M. (2021) Hausa Mai Dubun Hikima, Kano, Century Research and Publishing Company, Kano Nigeria.
Gwammaje K.D. (2010) Karin Magana a Kasar Hausa, littafi na 1-3 K.D.G Publisher Kano.
Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (2002) “Harshe da Adabin Hausa a Kammale; Don Manyan Makarantun Sakandire.” Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan-Nigeria
Muhammad, Y.M. (2005) “Adabin Hausa.” Zaria: Ahmadu Bello Unibersity Press Ltd., Samaru-Zaria
Dangambo A. (1982) Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmacin Ga Rayuwar Hausawa, Triumph KanoNigeria.
Dangambo, A. (1984) “Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa.” Madaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.
Danhausa, A.M (2012) “Hausa Mai Dubun Hikima.” Kano: Century Research and Publishing Company, Kano-Nigeria
Yahya I.Y. (1988) Hausa A Rubuce, Tarihin Rubuce-rubuce Cikin Hausa N.N.P.C Zaria
Yahya I.Y. da wasu (1992) Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Littafi na 1-2 Unibersity press PLC Ibadan
Yahya I.Y. da Dangambo A. (1986) Jagoran Nazarin Harshen Hausa N.N.P.C Zaria
Yunusa, Y. (2000) “Hausa a Dunkule.” Kano: Madaba’ar Jakara Bookshop.
Zarruk R.M da wasu (1986) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan Makarantun Sakandire. Littafi na daya. Unibersity Press L.T.D. Ibadan
No comments:
Post a Comment