Saturday, July 17, 2021

LAKANIN MALLAKA

LAKANIN MALLAKA (Gajeren Labari) Kabiru Yusuf Fagge (ANKA) Lokacin da matashi Ayuba ya shigo zauren Malamin Tsubbun mai suna Malam Nakande, malamin ya yi mamaki, domin mata ne suka fi zuwa wjensa ba maza ba, mazan ma baren samari. “Allah ya sa kwashewa ce.” Ya fada a ransa, a fili ya ce, “Sannu da zuwa ‘yan samari an ce ka dade kana jira a waje ko?” Yana murmushi “E wallahi amma ba komai.” “A to madalla, me ke tafe da kai?” “Malam ina son maganin mallaka ne?” “Mallaka, kamar wacce?” “Mallaka dai ta mallake mutum.” “E na sani, ita din ai kala-kala ce, akwai mallake maigida na kasuwa don a cuce shi, ko mallake uba, ko kuma mallake budurwa, kai dai na san ba ka da aure, bare in ce mallake matarka.” “Gaskiya ne Malam, ba ni da mata, budurwata nake so na mallake.” “To ka ji batu. Shi mallake budurwar taka wanne iri? Kana so ka mallake ta har ka aure ta, ko kuma ka mallake ta, ka rinka yin yadda ka so da ita?” Ayuba ya dan yi shiru. Malam Nakande ya kalle shi. “Kai saurayi, a irin wannan wuri ba a boye-boye in dai kana son bukata ta biya sai ka bude bayani openly.” “E, s nake in mallake ta, sai yadda na yi da ita.” Malam Nakande ya yi murmushi. “Ja’iri ana son a sha lagwada a wataya. An gama, ajiye min dubu bakwai da dari tara da hamsin, idan an jima ka dawo ka karbi zoben da za a hada lakanin a kansa.” Ayuba bai yi musu ba, ya kwo kudi ya ajiye, ya tafi. Da La’asar sakaliya Ayuba ya dawo, Malam Nakande ya dauki zobe mai ruwan azurfa da bakin kai ya ba shi. “Ka je da wannan zoben ka ba budurwar taka, za ka ga aiki da cikawa. Na tabbatar sai ka dawo, ka kara min wani abu.” Ayuba ya karba yana godiya ya tafi. ** Bayan kwana hudu, Malam Nakande na zaune a turakarsa, ‘yarsa Jummala durkushe a gabansa. “Baba an ce mu kawo kudin jarrabawa ne, shi ne Umma ta ce in zo, in gaya maka.” Malam Nakande yana son wannan diya tasa, yana son ta yi karatu sosai, ya yi murmushi. “Zuwa yaushe suke son ku kai?” “Jibi Juma’a.” “Jibi, ya aka yi ba ki gaya min da wuri ba.” “Mu ma, sai dazu suke gaya mana.” Suka dan yi shiru. “Shi ke nan, tashi je ki, zuwa an jima zan ba Umman taki, ta ba ki.” “To Baba, na gode, Allah ya saka da alheri.” Daidai lokacin da Jummala ta mike tsaye, idanun Malam Nakande ya kai bisa zoben da ke hannun Jummala, tabbas ya tuno da zoben, shi ya bai wa Ayuba shi, kwanaki biyar da suka wuce. “Ke, wa ya ba ki wannan zoben?” Ta dubi hannunta cikin kounya, ta dukar da kai, ta kasa magana. “Ke Jummala, tambayarki nake yi.” “Baba wani saurayina ne mai suna Ayuba ya ba ni, daman ina son, zan kawo shi wajenka ku gaisa.” Ji ya yi kamar ta lafta masa mari, ya ji wani gumi yana tsattsafo masa ta bayan wuya. “Ciro ki kawo shi nan.” Ta tsaya cikin mamaki, ba ta cire ba. “Ciro mana.” Ta cire, ta mika masa. “To je ki.” Ba musu, a sanyaye Jummala ta tafi, amma tana cike da mamakin me ke faruwa. Bayan fitar Jummala, Malam Nakande ya girgiza kai cikin damuwa. “Ka ga dan iskan yaro, ashe ni za a yi wa wannan shegantakar ya sa ni aiki? To karyarka ta sha karya, ba dai ka lalata min Jummala ba.”

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...